GA BAYANI AKANSU KAMAR HAKA:
(1) HADISI NA FARKO DA KA AMBATA, WANDA AL- MAGAZI...LIY YA RUWAITO A CIKIN LITTAFINSA; MANAK'IBU AMIRIL MUMININA ALIYU BIN ABI 'DALIB. GA HADISIN KAMAR HAKA:
24- أخبرنا أبو بكر أحمد بن محمد بن طاوان قال: حدثنا أبو الحسين أحمد بن الحسين ابن السماك قال: حدثنا أبو محمد جعفر بن محمد بن نصير الخلدي، حدثنا علي بن سعيد بن قتيبة الرملي قال: حدثنا ضمرة بن ربيعة القرشي عن ابن شوذب عن مطر الوراق عن شهر بن حوشب عن أبي هريرة قال: من صام يوم ثماني عشرة خلت من ذي الحجة، كتب له صيام ستين شهراً، وهو يوم غدير خم لما أخذ النبي صلى الله عليه وسلم بيد علي بن أبي طالب فقال: ((ألست أولى بالمؤمنين من أنفسهم؟)) قالوا: بلى يا رسول الله، قال: ((من كنت مولاه فعلي مولاه)) فقال: عمر بن الخطاب بخ بخ لك يا علي بن أبي طالب، أصبحت مولاي ومولى كل مؤمن. فأنزل الله تعالى {اليوم أكملت لكم دينكم}.
GA TARJAMAR WASU MARUWAITAN HADISIN KAMAR HAKA:
(1) ABUL HUSAINI AHMAD BINUL HUSAINI BIN SAMMAK, WANNAN MUTUMIN MAK'ARYACI NE. GA ABIN DA IBNU HAJAR YA FA'DA GAME DA SHI A LITTAFINSA ''LISANUL MIZAN'':
460 - أحمد بن الحسين أبو الحسين بن السماك الواعظ عن جعفر الخلدي ونحوه ونقل الخطيب عن أشياخه أنه كذاب وقد سمع منه الخطيب وكذبه بن أبي الفوارس مات سنة أربع وعشرين وأربع مائة انتهى قال الخطيب روى عن أبي عمرو بن السماك بحديث مظلم الإسناد منكر المتن فذكرت روايته لأبي القاسم الصيرفي فقال لم يدرك أبا عمرو وهو أصغر من ذلك لكنه وجد جزء فيه سماع أبي الحسين بن أبي عمرو بن السماك من أبيه فرتب على ذلك السماع وادعاه قال الصيرفي ولم يدرك الخلدي أيضا ولا عرف بطلب العلم إنما كان يبيع السمك في السوق إلى أن صار رجلا ثم سافر فصحب الصوفية وقال أبو الفتح أحمد المصري لم أكتب ببغداد عمن أطلق عليه الكذب من المشايخ غير أربعة أحدهم أبو الحسين بن السماك وقال رزق الله التميمي كان أبو الحسين بن السماك يتكلم على الناس بجامع المنصور وكان لا يحسن من العلوم شيئا إلا ما شاء الله وكان مطبوعا يتكلم على مذهب الصوفية فكتب إليه رقعة ما تقول في رجل مات ظماراها في الفرائض رماها وقال أنا أتكلم على مذهب قوم إذا ماتوا لم يخلفوا شيئا فأعجب الحاضرين.
(2) DAMRATU BIN RABI'A, SHI WANNAN SADUUK' NE, AMMA YANA YIN 'DIMUWA KA'DAN.
IBNU HAJAR YA CE:
2988- ضمرة ابن ربيعة الفلسطيني أبو عبدالله أصله دمشقي صدوق يهم قليلا من التاسعة مات سنة اثنتين ومائتين بخ 4
DUBA TAK'RUBUT TAHZEEB.
(3) MA'DAR AL- WARRAK', SHI KUMA SADUK'UN NE MAI YAWAN KUSKURE.
IBNU HAJAR YA CE:
6699- مطر بفتحتين ابن طهمان الوراق أبو رجاء السلمي مولاهم الخراساني سكن البصرة صدوق كثير الخطأ وحديثه عن عطاء ضعيف من السادسة مات سنة خمس وعشرين ويقال سنة تسع خت م 4
DUBA TAK'REEBUT TAHZEEB.
(4) SHAHAR BIN HAUSHAB, SHI MA SADUK'UN NE, AMMA YANA DA YAWA IRSALIN HADISI, DA YAWAN WAHAMI ('DIMUWA).
IBNU HAJAR YA CE:
2830- شهر ابن حوشب الأشعري الشامي مولى أسماء بنت يزيد ابن السكن صدوق كثير الإرسال والأوهام من الثالثة مات سنة اثنتي عشرة بخ م 4
DUBA TAK'RUBUT TAHZEEB.
DON HAKA WANNAN HADISIN NA K'ARYA NE SABODA AKWAI MAK'ARYACI A CIKIN ISNADINSA.
KUMA KA AMBACI CEWA; YANA CIKIN TARIKHU BAGDAD, GA YADDA YAKE:
أنبأنا عبد الله بن علي بن محمد بن بشران أنبأنا علي بن عمر الحافظ حدثنا أبو نصر حبشون بن موسى بن أيوب الخلال حدثنا علي بن سعيد الرملي حدثنا ضمرة بن ربيعة القرشي عن بن شوذب عن مطر الوراق عن شهر بن حوشب عن أبي هريرة قال من صام يوم ثمان عشرة من ذي الحجة كتب له صيام ستين شهرا وهو يوم غدير خم لما أخذ النبي صلى الله عليه و سلم بيد علي بن أبي طالب فقال ألست ولي المؤمنين قالوا بلى يا رسول الله قال من كنت مولاه فعلي مولاه
فقال عمر بن الخطاب بخ بخ لك يا بن أبي طالب أصبحت مولاي ومولى كل مسلم فأنز الله اليوم أكملت لكم دينكم ومن صام يوم سبعة وعشرين من رجب كتب له صيام ستين شهرا وهو أول يوم نزل جبريل عليه السلام على محمد صلى الله عليه و سلم بالرسالة
اشتهر هذا الحديث من رواية حبشون وكان يقال إنه تفرد به.
وقد تابعه عليه أحمد بن عبد الله بن النيري فرواه عن علي بن سعيد.
أخبرنيه الأزهري حدثنا محمد بن عبد الله بن أخي ميمي حدثنا أحمد بن عبد الله بن أحمد بن العباس بن سالم بن مهران المعروف بابن النيري إملاء حدثنا علي بن سعيد الشامي حدثنا ضمرة بن ربيعة عن بن شوذب عن مطر عن شهر بن حوشب عن أبي هريرة قال من صام يوم ثمانية عشر من ذي الحجة وذكر مثل ما تقدم أو نحوه
TO SHI MA DAI ISNADINSA IRIN WANCAN NA FARKO NE, SAI DAI SHI WANNAN A CIKINSA BABU WANCAN MAK'ARYACIN. DON HAKA SHI ISNADINSA DA'IFI NE. AMMA SAI DAI MUNKARI NE. DON HAKA HADISIN YA ZAMA MAI TSANANIN RAUNI. SABODA DALILAI KAMAR HAKA:
(1) YANAYIN MARUWAITANSA, DUKKANSU BABU THIK'A KO 'DAYA A CIKINSU. KUMA MUN FA'DI HALIN WASU DAGA CIKINSU.
(2) HADISIN ISNADINSA MAI RAUNI NE, AMMA YA YI KARO DA INGANTACCEN HADISI. SHI NE WANDA YA ZO YAKE TABBATAR DA CEWA; ITA AYAR DA TAKE CIKIN HADISIN:
اليوم أكملت لكم دينكم.
TA SAUK'A NE A RANAR ARAFA, RANAR JUMA'A.
(3) ABIN DA KE K'ARSHEN HADISIN, WANDA YA KE NUNA CEWA; - WAI - SHI NE RANAR FARKO DA JIBRILU YA SAUK'A DA MANZANCI WA ANNABI (SAW), WANNAN YA SA'BA MA ABIN DA YA TABBATA A WAJEN MALAMAN SIRA; RANAR FARKO DA JIBRILU YA SAUK'A WA ANNABI (SAW) ITA CE RANAR LITININ 21 GA WATAN RAMADAN. YANA 'DAN SHEKARA 40 DA HAIHUWARSA.
AMMA ITA RANAR GADEER KUMA RANAR LAHADI CE,18 GA ZUL HIJJA.
DON HAKA HADISIN SAM BAI TABBATA BA.
GA ABIN DA MALAMAN TAFSIRI SUKA TABBATAR GAME DA WURIN SAUK'AR AYAR:
(1) AL- 'DABARIY BAYAN YA KAWO HADISAI DA MAGANGANUN MAGABATA AKAN CEWA AYAR TA SAUK'A NE A RANAR ARAFA, SAI YA CE:
قال أبو جعفر: وأولى الأقوال في وقت نزول الآية، القول الذي... روي عن عمر بن الخطاب: أنها نزلت يوم عرفة يوم جمعة، لصحة سنده، ووهي أسانيد غيره.
MAGANAR DA TA FI KOWACCEE DACEWA GAME DA LOKACIN SAUK'AR AYAR, ITA CE RANAR ARAFA, A RANAR JUMA'A. SABODA INGANCIN ISNADINSA, DA KUMA RAUNIN ISNADOJIN WAN'DANDA BA WANNAN BA.
(2) HAKA IBNU KASIR YA TABBATAR GA INDA YA KE CEWA:
قلت: وقد روى ابن مردويه من طريق أبي هارون العبدي عن أبي سعيد الخدري: أنها نزلت على رسول الله صلى الله عليه وسلم يوم غدير خم حين قال لعلي "من كنت مولاه فعلي مولاه". ثم رواه عن أبي هريرة، وفيه أنه اليوم الثامن عشر من ذي الحجة يعني مرجعه عليه السلام من حجة الوداع، ولا يصح هذا ولا هذا بل الصواب الذي لا شك فيه ولا مرية أنها أنزلت يوم عرفة، وكان يوم جمعة كما روى ذلك أمير المؤمنين عمر بن الخطاب وعلي بن أبي طالب، وأول ملوك الإسلام معاوية بن أبي سفيان، وترجمان القرآن عبد الله بن عباس، وسمرة بن جندب رضي الله عنهم، وأرسله الشعبي وقتادة بن دعامة وشهر بن حوشب وغير واحد من الأئمة والعلماء، واختاره ابن جرير الطبري رحمه الله.
YA YI BAYANIN CEWA, MAGANAR SAUK'AR WANNAR AYA A RANAR GADEER, SAM BAI INGANTA BA. ABIN DA BABU SHAKKA A CIKINSA SHI NE CEWA; AYAR TA SAUK'A NE A RANAR ARAFA, RANAR JUMA'A. SAI YA AMBACI SAHABBAN DA SUKA RUWAITO HAKAN. DAGA CIKINSU HAR AKWAI SHI ALIYUN (RA) DA IBNU ABBAS (RA). DA KUMA SAURAN TABI'AI.
(3) SA'ANNAN AL- SUYU'DIY YA CE:
وأخرج ابن مردويه ، وابن عساكر بسند ضعيف عن أبي سعيد الخدري قال لما نصب رسول الله صلى الله عليه وسلم عليا يوم غدير خم فنادى له بالولاية هبط جبريل عليه بهذه الآية {اليوم أكملت لكم دينكم}
SAI YA CE:
بسند ضعيف.
MA'ANA; DA ISNADI MAI RAUNI.
KUMA DU YA CE:
وأخرج ابن مردويه والخطيب ، وابن عساكر بسند ضعيف عن أبي هريرة قال : لما كان يوم غدير خم وهو يوم ثماني عشر من ذي الحجة قال النبي صلى الله عليه وسلم : من كنت مولاه فعلي مولاه ، فانزل الله {اليوم أكملت لكم دينكم}.
A WANNAN MA YA CE:
بسند ضعيف.
DA ISNADI MAI RAUNI.
DON HAKA MAGANAR CEWA; - WAI - AYAR TA SAUK'A NE A RANAR GADEER, SAM BA HAKA NE, DUKKAN RUWAYOYIN BA SU INGANTA BA.
(2) SA'ANNAN KA KAWO WANI HADISIN DAGA MUSNAD AHMAD. GA SHI KAMAR HAKA:
حدثنا عبد الله حدثني أبي ثنا عفان ثنا حماد بن سلمة أنا على بن زيد عن عدى بن ثابت عن البراء بن عازب قال : كنا مع رسول الله صلى الله عليه و سلم في سفر فنزلنا بغدير خم فنودي فينا الصلاة جامعة وكسح لرسول الله صلى الله عليه و سلم تحت شجرتين فصلى الظهر وأخذ بيد علي رضي الله تعالى عنه فقال ألستم تعلمون انى أولى بالمؤمنين من أنفسهم قالوا بلى قال ألستم تعلمون انى أولى بكل مؤمن من نفسه قالوا بلى قال فأخذ بيد على فقال من كنت مولاه فعلي مولاه اللهم وال من والاه وعاد من عاداه قال فلقيه عمر بعد ذلك فقال هنيئا يا بن أبي طالب أصبحت وأمسيت مولى كل مؤمن ومؤمنة
SHI MA WANNAN HADISIN MAI RAUNI NE, SAM BAI TABBATA BA. SABODA A CIKIN ISNADINSA AKWAI ALIYU BIN ZAID SHI KUMA DA'IFI NE.
IBNU HAJAR YA CE:
4734- علي ابن زيد ابن عبدالله ابن زهير ابن عبدالله ابن جدعان التيمي البصري أصله حجازي وهو المعروف بعلي ابن زيد ابن جدعان ينسب أبوه إلى جد جده ضعيف من الرابعة مات سنة إحدى وثلاثين وقيل قبلها بخ م 4
DUBA TAK'RIBUT TAHZEEB.
(3) ABIN DA YA TABBATA NA HADISIN GADEER, SHI NE:
من كنت مولاه فعلي مولاه.
MA'ANAR MAULA A CIKIN HADISIN SHI NE MASOYI. BA - WAI - SHUGABA BA, KAMAR YADDA KUKA 'DAUKA. SABODA DALILAI MASU YAWA.
(1) KA CE:
a bisa abinda ya tabbata daga Malaman Hadisi shi Hadisi koda ya kai guda dubu da aka sami rauni a cikinsa, sai a gefe guda aka sami ingantacce guda daya tal, to wannan Had...isin guda daya tal ingantacce ya fi karfin wadancen dubun raunannu, kai ya ma tashe su ne daga raunana sun koma Hasanai.
YA KAMATA KA SANI; HADISI BA YA TA'BA ZAMA ''HASAN'' IDAN RAUNINSA MAI TSANANI NE. MA'ANA IDAN A CIKIN ISNADINSA AKWAI WANDA AKE TUHUMA DA K'ARYA KO MAKAMANCINSA, BALLANTANA KUMA IN MAK'ARYACI NE.
HAKA KUMA IN YA ZAMA MUNKARI, WATO HADISI MAI RAUNI DA YA K'UNSHI ABIN DA YA SA'BA WA INGANTACCEN HADISI.
AL- IRAK'IY YA CE:
( والحسن المعروف مخرجا وقد ... اشتهرت رجاله بذاك حد )
( حمد وقال الترمذي ما سلم ... من الشذوذ مع راو ما اتهم )
( بكذب ولم يكن فردا ورد ... قلت وقد حسن بعض ما انفرد )
( وقيل ما ضعف قريب محتمل ... فيه وما بكل ذا حد حصل )
( وقال بان لي فيه بامعان النظر ... أن له قسمين كل قد ذكر )
( قسما وزاد كونه ما عللا ... ولا ينكر أو شذوذ شملا )
SAI AL- SAKHAWIY YA YI SHARHI YA CE:
ما سلم من الشذوذ يعني بالتفسير الماضي في الصحيح ( مع راو ) أي مع أن رواة سنده كل منهم ما اتهم بكذب فيشمل ما كان بعض رواته سيىء الحفظ ممن وصف بالغلط أو الخطأ أو مستورا لم ينقل فيه جرح ولا تعديل وكذا إذا نقلا ولم يترجح أحدهما على الآخر أو مدلسا بالعنعنة أو مختلطا بشرطه لعدم منافاتها اشتراط نفي الاتهام بالكذب.
YA CE: (YANA MAGANA AKAN HADISI HASAN) WANDA YA KU'BUTA DAGA SHUZUZI. YANA NUFIN NA BAYANINSA NA BAYA, WANDA YA GABATA A BABIN ''AL- SAHIH''. MA'ANA; LALLAI YA ZAMA MARUWAITAN ISNADINSA KOWANNENSU BA A TUHUME SHI DA K'ARYA BA. SAI YA K'UNSHI WANDA WASU MARUWAITAN NASA MASU MUMMUNAR HADDA CE, DAGA WANDA AKA SIFFANTA SHI DA GALA'DI KO KUSKURE, KO MASTURI; WANDA BA A SAMU WATA MAGANA A KANSA TA AIBANTAWA KO BAYANIN ADALCINSA BA, KO KUMA AN SAMU AMMA BA A RINJAYAR DA 'DAYA DAGA CIKINSU BA. KO KUMA MUDALLISI MAI ''AN'ANA'' (RUWAYA DA LAFAZIN ''AN'') KO WANDA YA RIKICE BISA SHARA'DINSA. SABODA (DUKA WA'DANNAN SIFFOFI) BA SU KORE SHARA'DIN DA AKA SA NA KORUWAN TUHUMAR MUTUM DA K'ARYA. (MA'ANA; WA'DANNAN SIFOFI BA SU HANA TUHUMAR MUTUM DA K'ARYA, ALHALI RASHIN TUHUMAR MUTM DA K'ARYA SHARA'DI NE KAFIN HADISINSA YA ZAMA ''HASAN'')
DUBA FATHUL MUGITH, NA SAKHAWIY.
IRAK'IY YA CIGABA SAI YA CE:
( وإن يكن لكذب أو شذا ... أو قوي الضعف فلم يجبر ذا )
TO GA ASALIN MUHALLUSH SHAHID 'DINMU.
YA CE: IDAN RAUNIN HADISI YA ZAMA SABODA K'ARYAR MARUWAICI NE, KO KUMA SHAZZI NE, KO KUMA RAUNIN YA YI K'ARFI (AN AMBACI IRINSU A MAGANAR SAKHAWIY A BAYA) TO BA ZA 'DORA WANNAN HADISI BA. (MA'ANA WANNAN KARYAYYEN HADISI MAI RAUNIN BA ZAI TA'BA 'DORUWA YA ZAMA ''HASAN'' BA, SABODA WANNAR MATSALA TASA).
DON HAKA NURU; HADISIN DA KA KAWO DAGA WURARE GUDA 2, 'DAYA AKWAI MAK'ARYACI A CIKIN SANADINSA, 'DAYA KUMA MARUWAITANSA MASU YAWAN KUSKURE NE, BABU THIK'A KO 'DAYA A CIKINSU, TO DON ALLAH KA GAYA MINI; WACE K'A'IDA CE TA MALAMAN HADISIN DA SUKA CE; HADISIN ZAI IYA ZAMA ''HASAN''???!!!
SAI DAI IN MALAMAN HADISIN RAFIDA NE KO??!!
ABIN DA ZAI TABBATAR DA WANNAN SHI NE SHARHIN DA SAKHAWIY YA YI WA BAITIN:
( وإن يكن ) ضعف الحديث ( لكذب ) روايه ( أو شذا ) أي وشذوذ في روايته بإن خالف من هو أحفظ أو أكثر ( أو قوى الضعف ) بغيرهما ما يقتضي الرد (فلم يجبر ذا) أي الضعف بواحد من هذه الأسباب ولو كثرت طرقه كحديث (من حفظ على أمتي أربعين حديثا) فقد نقل النووي اتفاق الحفاظ على ضعفه مع كثرة طرقه ولكن بكثرة طرقه القاصرة عن درجة الاعتبار بحيث لا يجبر بعضها ببعض يرتقي عن مرتبه المردود المنكر الذي لا يجوز العمل به بحال إلى رتبة الضعيف الذي يجوز العمل به في الفضائل.
YA CE: IDAN RAUNIN HADISI YA KASANCE SABODA K'ARYAN MARUWAICINSA NE, KO KUMA SHUZUZI NE A CIKIN RUWAYAR TASA, TA YADDA YA SA'BA WA WANDA YA FI SHI HADDA, KO SHI 'DAYA YA SA'BA WA MASU YAWA. KO KUMA RAUNIN YA YI K'ARFI DA WANI ABU BA SU BIYUN BA, NA ABIN DA YAKE HUKUNTA JEFAR DA HADISI, TO BA ZA A 'DORA (K'ARFAFA) WANNAN RAUNIN BA, DA 1 DAGA WA'DANNAN DALILAI, KO DA KUWA HANYOYIN HADISIN SUN YAWAITA. KAMAR HADISIN ''MAN HAFIZA ALA UMMATIY 40 HADISAN....'' HAK'IK'A NAWAWIY YA RUWAITO ITTIFAK'IN MALAMAN HADISI AKAN RAUNINSA DUK KUWA DA YAWAN HANYOYINSA....
DUBA FATHUL MUGITH, NA SAKHAWIY.
DON HAKA, NA RASA A INA KA SAMO WACCAR MAGANAR TAKA???!!
BAI KAMATA ANA K'ARYA WA MALAMAN HADISI BA, IN DA GASKE NE SAI A YI CUTTING 'DIN MAGANAR TASU DA INDA TAKE.
MAGANAN DA KA KE YI NA HADISI INGANTACCE KUMA, BAITIN DA KA KAWO YANA TABBATAR MAKA DA CEWA; HADISI BA YA TA'BA ZAMA INGATACCE HAR SAI YA CIKA SHARU'DA GUDA 5:
(1) ITTISALUS SANADI.
(2) ADALA.
(3) DAB'DI.
(4) ADAMUL SHUZUZI.
...(5) ADAMUL ILLAH.
DON HAKA HADISIN DA KA KAWO DAGA LITTAFIN AL- MAGAZALI, A CIKIN ISNADINSA A KWAI ''KAZZAB'' KAMAR YADDA NA KAWO MAKA DAGA LITTAFIN ''LISANUL MIZAN''.
TA YAYA HADISIN MAK'ARYACI ZAI ZAMA ''HASAN''??!!
SHI KUMA WANDA YAKE CIKIN TARIKHU BAGDAD, MARUWAITANSA KUSAN DUKKANSU MASU ''WAHAMI'' DA YAWAN KUSKURE NE, KAMAR YADDA NA TABBATAR A BAYA.
TO YANZU WANNAN HADISIN NE ZAI YI KARO DA INGANTATTUN HADISAI??!!
GA SU KAMAR HAKA:
عن طارق بن شهاب عن عمر بن الخطاب أن رجلا من اليهود قال له يا أمير المؤمنين آية في كتابكم تقرءونها لو علينا معشر اليهود نزلت لاتخذنا ذلك اليوم عيدا قال أي آية قال{اليوم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دينا}قال عمر قد عرفنا ذلك اليوم والمكان الذي نزلت فيه على النبي صلى الله عليه وسلم وهو قائم بعرفة يوم جمعة
BUKHARI DA MUSLIM SUN RUWAITO SHI, HAKA DUKKAN MALAMAN TAFSIRI SUN TABBATAR DA CEWA WANNAR AYAR TA SURATUL MA'IDA TA SAUKA NE A RANAR ARAFA. AMMA KAI KUMA KA ZO KA KAWO WANI HADISIN K'ARYA KA CE; -WAI- TA SAUKA NE A RANAR GADEER!!
AI GA NAN HADISIN GADEER 'DIN, TIRMIZIY YA RUWAITO SHI:
حدثنا محمد بن بشار حدثنا محمد بن جعفر حدثنا شعبة عن سلمة بن كهيل قال سمعت أبا الطفيل يحدث عن ابي سريحة أو زيد بن أرقم شك شعبة : عن النبي صلى الله عليه و سلم قال من كنت مولاه فعلي مولاه.
SAI KA NUNA MANA INDA AKA CE; - WAI - UAMAR (RA) YA CE: BAKHIN, BAKHIN..??!!
SA'ANNAN KA NUNA MANA IN DA AKA CE A YI AZUMIN WANNAR RANAR??!!
SA'ANNAN KA NUNA MANA INDA AKA CE; AYAR ''AL- YAUMA AKMALTU LAKUM DINAKUM... TA SAUK'A NE A WANNAR RANA??!!
KAWAI KA 'DEBO MAGANAR MAK'ARYATA KA ZO KA CE; -WAI- HADISIN ANNABI NE??!!
AN YI MAKA BAYANIN CEWA; BAI TABBATA DAGA ANNABI (SAW) BA, KA TSAYA KANA TA WANI JAYAYYA MARAS AMFANI!!!
KO KUMA DUK WA'DANNAN ABUBUWAN AKWAI SU A CIKIN HADISIN GADEER DA MUSLIM YA RUWAITO DAGA ZAIDU BIN ARK'AM (RA)??
SABODA TSANTSAR GULUWWI DA K'IN GASKIYA KAWAI MUTANE SU TSALLAKE ABIN DA YA TABBATA, SU JE SUNA 'DEBO HADISAN K'ARYA DA RU'BA'B'BUN HADISAI -WAI- DA SU ZA SU TABBATAR DA ''WILAYAR IMAMANSU''???!!
DON HAKA HADISIN ABU HURAIRA (RA) DA KA KAWO DAGA TARIKHU BAGDAD, SHAZZI NE MUNKARI, SABODA YA SA'BA MA INGANTATTUN HADISAI KUMA YA ZO DA ABIN YA SA'BA MA ABIN DA AKA SANI.
WAI AZUMIN WANNAR RANAR YANA DAIDAI DA AZUMIN WATA 60, AI DAGA JI MA KA SAN WANNAN HADISIN K'ARYA NE. MUSAMMAN SABODA A CIKIN ISNADINSA AKWAI MAK'ARYACI.
SABODA HAKA NI SHAWARAR DA NAKE BA KA, - A MAIMAKON KA TSAYA KANA KWA'BA DA KARAN TSAYE WA ILMIN HADISI-; YA KAMATA KA SAMU WANI MALAMI DA YA SAN HADISI, SAI KA SA WANI LITTAFI NA ''MUS'DALAHU'' KAMAR ''TADRIBUR RAWIY'' DA MAKAMANCINSA, SAI KA KARANCE SHI A WAJENSA YA YI MAKA BAYANIN ABIN DA ILMIN YA K'UNSA, YA FI AKAN KAWAI KA NA TSUNDUMA CIKIN LITTATAFAI KANA TA KWASO ABUBUWAN DA BA KA SAN HAK'IK'ANINSU BA, KA ZO KANA INGANTA HADISAI HAKA KAWAI BA K'A'IDA. SABODA KARATU BA MALAMI YANA DA ILLA MATUK'A. WANI YA CE:
يظن الغمر أن الكتب تهدي *** أخا فهم لإدراك العلوم
وما يدري الجهول بأن فيها *** غوامض حيرت عقل الفهيم
إذا رمت العلوم بغير شيخ *** ضللت عن الصراط المستقيم
وتلتبس العلوم عليك حتى *** تصير أضل من توما الحكيم
KA CE:
Ka kawo wasu tarjamomi na wasu sanadan wadanda ba su na kawo ba, kamar yadda kai ma ka fada a baya, to ai kamata ya yi ka kama ni da laifin abin da na aikata ba wanda ban aikata ba,
HADISIN DA KA KAWO NA ABU HURAIRA, WANDA KA CE; YAN...A CIKIN ''MANAK'IBU ALIYU BIN ABI 'DALIB'' NA AL- MAGAZILIY, KUMA KA CE; YANA CIKIN TARIKHU BAGDAD. SHI NA 'DAUKO NA YI MAKA BAYANIN RAUNINSA DA K'ARYAR DA TAKE CIKINSA. IN KUMA BA SHI BA NE, TO KA KWAFO SHI DA LARABCINSA MU GANI??!!
KU DA KUKE ZAGIN ABU HURAIRA (RA) KUKE TUHUMARSA DA K'ARYA, SHI NE YAU ZAKU 'DAUKO HADISINSA KU KAFA HUJJA DA SHI, SABODA SON ZUCIYA??!!
KA JI ABIN MAMAKI, DA YAKE MUN BAYYANA MAKA AIBIN HADISIN DA KA KAWON, AI DOLE KA ZILLE KA CE; WANDA KA KAWON DAGA ''ALBIDAYA'' NA IBNU KASIR NE!!!
TO WALLAHI GA ABIN DA KA KAWO A WALL 'DIN HASAN BALA:
KA CE:
BAI'AR UMAR DAN HATTAABIY GA IMAM ALIY (A) A GHADIIR:
• Ibnul-Magaaziliy ya fitar a cikin Manaaqibu Aliyyubni Abii Taalib a shafi na 18 – 19 a lamba tat a 24. Daga Abuu Hurairah yace: "Duk wanda ya azumci ranar goma sha takwas na Zul-hijja, za'a rubuta masa ladan azumin wata sittin, kuma shine ranar Gadiiru Khuum, yayin da Manzo (S) ya rike hannun Aliy (A) kuma yace: Shin ba nine na fiyewa Muminai ba akan kansu ba? Suka ce: Kaine ya Manzon Allah, (Annabi) yace: Duk wanda na zamo shugabansa, to Aliyyu shugabansa. Sai Umar dan Hattabi yace: Yayi kyau, yayi kyau (Bakhin, bakhin) ya Aliyyubni Abii Taalib, ka wayi gari shugabana da kuma shugaban dukkanin Mumini, sai Ubangiji Madaukakin Sarki ya saukar da: (A yau ne na cika muku addininku ………)" Surat Maa'idah:3.
Haka nan dai wannan ruwayar dai tazo a cikin Taariikhu Bagdaad juzu'insa na takwas (8) shafi na (289), shima dai daga Abuu Hurairah.
• Ahmad bn Hanbali shima ya fitar a cikin Musnadinsa: "…… duk wanda na zamo shugabansa, to Aliyyu shugabansa, Ubangiji ka jibinci lamarin wanda ya dauke shi shugaba, kayi gaba da wanda bai yadda shi Shugabansa bane, yace sai Umar ya riske shi bayan hakan sanna yace masa mun yarda Ya 'dan Abii Taallib ka wayi gari kuma ka wuni shugaban dukkanin Mumini da Mumina" (Musnad Ahmad bn Hanbali uzu'insa na hudu (4), shafi na (281).
TO INA NA ''ALBIDAYAN'' DA KA CE SHI KA KAWON???
NURUDDEEN BAI KAMATA KANA TADLISI DA TALBISI WA MUTANE BA!!!
SA'ANNAN SU RUWAYOYIN DA KA KAWO DAGA ''ALBIDAYA'' TA IBNU KASIR, AI TA 2 TANA NAN A CIKIN SAHIHU MUSLIM MA, AMMA BABU LAFAZIN; ''MAN KUNTU MAULAHU...'' WANDA SHI MA HADISIN DA YA ZO DA WANNAN LAFAZIN; ''MAN KUNTU MAULAHU...'' YA TABBATA DAGA MANZON ALLAH (SAW). SAI DAI MAGANARMU DA KU AKANSA SHI NE A WAJEN MA'ANAR KALMAR ''MAULA'' KUMA ABIN DA KA KAWO DAGA ''ALBIDAYA'' NA SABABIN DA YA SA MANZO ALLAH (SAW) HAR YA FA'DI HADISIN, SHI YAKE NUNA MAKA CEWA; ABIN DA ANNABI (SAW) YA KE NUFI DA KALMAR SHI NE MASOYI, KAMAR YADDA BAYANI ZAI ZO A GABA, INSHA ALLAHU.
DON HAKA DAI YANZU KA SALLAMA CEWA; HADISIN BAI'AR UMAR (RA) NA K'ARYA NE. MAGANAR SAUK'AR AYAR ''AL- YAUMA AKMALTU.., DA KUMA MAGANAR AZUMIN RANAR GADEER, DUKA WA'DANNAN KWATA - KWATA BA SU TABBATA BA!!!
LAFAZIN ''MAULA'' KUMA DA YA ZO A CIKIN HADISIN, SAI KA GAMA RUBUTA ABIN DA ZA KA RUBUTA ZAMU ZO MU YI MAKA BAYANI.
ALLAH YA SA MU DACE!
KA CE:
A dai wannan shafin ne Dr. Wasiyyullaah yake tahqiiqi yake cewa: "Isnadin wannan Hadisin Hasanun ne ligairihi, saboda Aliyyu bn Zaid Raunanna ne (Dha'iifun) sai dai ya biye bayan Hadisin da ya gabata a lamba ta 1016 ta hanyar Hammaad kuma Hadisin ingantacce ne kuma ya gabata a lamba ta 947 har wala iyau".
A INA NE YA CE: HASANUL LI GAIRIHIN??
KUMA DA YA CE: HADISIN SAHIHI NE, ME YAKE NUFI??
SHIN YANA NUFIN HADISIN ''MAN KUNTU MAULAHU NE..'' KO KUMA NA ''BAI'AR UMAR (R)''??!
SA'ANNAN DON ME YA SA BA KA KAWO WA'DANDA YA YI IHALA ZUWA GARESU BA; WATO HADISI NA 947, 1021, KA KAWO SU DA LAFAZINSU MANA??!!
DON ALLAH KA JI TSORON ALLAH KA DENA TADLISI, ADDINI FA NA ALLAH NE BA NAKA BA!!
TO WALLAHI TUN DA WURI KA YI BAYANIN GASKIYAR ABIN DA SHAIKH WASIYYULLAH YA FA'DA A CIKIN LITTAFINSA, KAFIN IN FARA YI MAKA RADDI, IN FALLASA RASHIN GASKIYARKA DA TADLISINKA!!
HADISI NA 1, WANDA AHMAD YA RUWAITO A ''FADA'ILUS SAHABA'' GA SHI KAMAR HAKA:
1016 - حدثنا عبد الله قثنا أبي نا عفان قثنا حماد بن سلمة قال أنا علي بن زيد عن عدي بن ثابت عن البراء بن عازب قال : كنا مع رسول الله صلى الله عليه و سلم في سفر فنزلنا بغدير خم فنودي فينا الصلاة جامعة وكسح لرسول الله صلى الله عليه و سلم تحت شجرتين فصلى الظهر وأخذ بيد علي فقال ألستم تعلمون اني أولى بالمؤمنين من أنفسهم قال بلى قال ألستم تعلمون إني أولى بكل مؤمن من نفسه قالوا بلى قال فأخذ بيد علي فقال اللهم من كنت مولاه فعلي مولاه اللهم وال من والاه وعاد من عاداه قال فلقيه عمر بعد ذلك فقال هنيئا لك يا بن أبي طالب أصبحت وأمسيت مولى كل مؤمن ومؤمنة
GA NAN WAJEN MAGANARMU WANDA SHI NE K'ARSHEN HADISIN:
قال فلقيه عمر بعد ذلك فقال هنيئا لك يا بن أبي طالب أصبحت وأمسيت مولى كل مؤمن ومؤمنة
YA CE: SAI UMAR YA HA'DU DA SHI, SAI YA CE MASA: INA MAKA MURNA YA 'DAN ABU 'DALIB; KA WAYI GARI, KUMA KA WUNI KA ZAMA MASOYIN KOWANE MUMINI DA MUMINA.
TO DA WANNAR MAGACE NURUDDEEN YAKE CEWA; -WAI- UAMAR (RA) YA YI MUBAYA'A MA ALIYU (RA)??!!
TO WANNAR MAGANA DAI MAI RAUNI CE; DA'IFIYA CE, SAM BA TA INGANTA BA. SABODA A CIKIN ISNADIN HADISIN AKWAI; ALIYU BIN ZAID, SHI KUMA DA'IFI NE, MAI RAUNI NE.
IBNU HAJAR YA CE:
4734- علي ابن زيد ابن عبدالله ابن زهير ابن عبدالله ابن جدعان التيمي البصري أصله حجازي وهو المعروف بعلي ابن زيد ابن جدعان ينسب أبوه إلى جد جده ضعيف من الرابعة مات سنة إحدى وثلاثين وقيل قبلها بخ م 4
DUBA TAK'RIBUT TAHZEEB.
NURU KA CE:
A dai wannan shafin ne Dr. Wasiyyullaah yake tahqiiqi yake cewa: "Isnadin wannan Hadisin Hasanun ne ligairihi,
WALLAHI WANNAR MAGANA BA HAKA TAKE BA. GA ABIN DA SHAIKH WASIYYUL LAH YA FA'DA:
(1016) اسناده ضعيف لاجل علي بن زيد بن جدعان.
وهو في المسند (4: 281) بهذا الاسناد مثله, واخرجه ابن ابي عاصم في السنة (ل 134 ب) عن شيخه هدبة عن حماد. والحديث صحيح ومضي برقم (947) وياتي (1024).
YA CE: ISNADINSA DA'IFI NE. SABODA ALIYU BIN ZAIDI BIN JUD'AN.
DUBA 'DAB'A TA FARKO NA LITTAFIN WANDA AKA BUGA A JAMI'AR UMMUL K'URA TA MAKKA. A SHEKARA TA 1403H - 1983M, SHAFI 2/ 596.
SA'ANNAN KUMA KA DUBA 'DAB'AR ''DARU IBNUL JAUZIY'' BUGU NA 2, A 1420H - 1999M, SHAFI NA 2/ 738.
DON HAKA MAGANAR CEWA; WASIYYULLAH YA CE: HASANUL LI GAIRIHI K'ARYA NE.
BARI MU BI MAGANAR WASIYYULLAH DALLA - DALLA, YA CE:
وهو في المسند (4: 281) بهذا الاسناد مثله,
MA'ANA HADISIN YANA CIKIN ALMUSNAD:
18479 - حدثنا عفان، حدثنا حماد بن سلمة، أخبرنا علي بن زيد، عن عدي بن ثابت، عن البراء بن عازب، قال: كنا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم في سفر، فنزلنا بغدير خم، فنودي فينا: الصلاة جامعة، وكسح لرسول الله صلى الله عليه وسلم تحت شجرتين، فصلى الظهر، وأخذ بيد علي رضي الله عنه، فقال: " ألستم تعلمون أني أولى بالمؤمنين من أنفسهم ؟ " قالوا: بلى، قال: " ألستم تعلمون أني أولى بكل مؤمن من نفسه ؟ " قالوا: بلى، قال: فأخذ بيد علي، فقال: " من كنت مولاه ، فعلي مولاه، اللهم وال من والاه ، وعاد من عاداه " قال: فلقيه عمر بعد ذلك، فقال: " له هنيئا يا ابن أبي طالب، أصبحت وأمسيت مولى كل مؤمن، ومؤمنة "
WANNAN DAI TUN TUNI MUN CE ISNADINSA DA'IFI NE, KUMA SHI NE ABIN DA WASIYYULLAH YA TABBATAR A CIKIN LITTAFINSA. WATO SABODA ALIYU BIN ZAID.
SA'ANNAN YA CE:
واخرجه ابن ابي عاصم في السنة (ل 134 ب) عن شيخه هدبة عن حماد.
MA'ANA HADISIN YANA CIKIN AL- SUNNA NA IBNU ABI ASEEM, GA SHI KAMAR HAKA:
1363- حدثنا هدبة بن خالد ، حدثنا حماد بن سلمة عن علي بن زيد وأبي هارون عن عدي بن ثابت عن البراء قال قال رسول الله صلى الله عليه وسلم لعلي هذا مولى من أنا مولاه أو ولي من أنا مولاه.
WANNAN SHI NE ASALIN YADDA HADISIN YAKE, AMMA K'ARIN ''BAI'AR UMAR'' RAFIDA NE SUKA CUSA SHI KAMAR YADDA HAKAN ZAI BAYYANA A GABA!!
DUBA AL- SUNNA, 2/ 605 'DAB'AR ''ALMAKTABUL ISLAMI'' TAKHARIJIN ALLAMATUL ALBANIY, BUGU NA FARKO 1400H - 1980M.
TAMBAYARMU A NAN ITA CE:
INA MAGANAR ''BAI'AR UMAR (RA)'' A CIKIN HADISIN???!
SA'ANNAN YA CE:
والحديث صحيح ومضي برقم (947) وياتي (1024).
MA'ANA HADISIN INGANTACCE NE. YA GABATA A LAMBA TA (947) KUMA ZAI ZO A LAMBA TA (1024).
TO GA SU KAMAR HAKA:
947 - حدثنا أبو عبد الرحمن عبد الله بن أحمد بن حنبل قال حدثني أبي رحمه الله قثنا وكيع قثنا الأعمش عن سعد بن عبيدة عن بن بريدة عن أبيه قال قال رسول الله صلى الله عليه و سلم : من كنت وليه فعلى وليه
WANDA YA CE: YANA LAMBA TA 1024 SHI NE WANNAN MAI LAMBA 1021, SABODA NA LAMBA TA 1024 WANI HADISIN DABAN NE:
1021 - حدثنا عبد الله قال حدثني أبي نا محمد بن جعفر نا شعبة عن أبي إسحاق قال سمعت سعيد بن وهب قال نشد على الناس فقام خمسة أو ستة من أصحاب النبي صلى الله عليه و سلم فشهدوا ان رسول الله صلى الله عليه و سلم قال : من كنت مولاه فعلي مولاه.
GA NA 1024 'DIN:
1024 - حدثنا عبد الله قال حدثني أبي قثنا يحيى بن آدم قال نا شريك عن عياش العامري عن عبد الله بن شداد بن الهاد قال : قدم على رسول الله صلى الله عليه و سلم من أهل اليمن وفد ليشرح قال فقال رسول الله صلى الله عليه و سلم لتقيمن الصلاة أو لأبعثن إليكم رجل يقتل المقاتلة ويسبي الذرية قال ثم قال رسول الله صلى الله عليه و سلم اللهم أنا أو هذا وانتشل بيد علي
TO WASIYYULLAH YA CE:
والحديث صحيح ومضي برقم (947) وياتي (1024).
MA'ANA HADISIN INGANTACCE NE. YA GABATA A LAMBA TA (947) KUMA ZAI ZO A LAMBA TA (1024).
TAMBAYARMU A NAN ITA CE:
INA MAGANAR ''BAI'AR UMAR (RA)'' A CIKIN HADISIN???!
DON HAKA MENENE MA'ANAR MAGANAR WASIYYULLAH???!
ABIN DA WASIYYULLAH (H) YAKE NUFI SHI NE; HADISIN;
من كنت مولاه فعلي مولاه.
INGANTACCE NE. AMMA BAN DA K'ARIN MAGANAR ''BAI'AR UMAR'' SABODA A CIKIN ISNADINSA AKWAI ALIYU BIN ZAID, DA'IFI NE, KUMA BABU WANNAN K'ARIN A CIKIN HADISAI 2 DA YA YI IHALA ZUWA GARESU; NA 947, 1024.
IN KUMA AKWAI MUNA SAURARO???!
HADISI NA 2, WANDA NURUDDEEN YA KAWO, SHI MA AHMAD NE YA RUWAITO SHI AMMA A CIKIN MUSNAD:
18479 - حدثنا عفان، حدثنا حماد بن سلمة، أخبرنا علي بن زيد، عن عدي بن ثابت، عن البراء بن عازب، قال: كنا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم في سفر، فنزلنا بغدير خم، فنودي فينا: الصلاة جامعة، وكسح لرسول الله صلى الله عليه وسلم تحت شجرتين، فصلى الظهر، وأخذ بيد علي رضي الله عنه، فقال: " ألستم تعلمون أني أولى بالمؤمنين من أنفسهم ؟ " قالوا: بلى، قال: " ألستم تعلمون أني أولى بكل مؤمن من نفسه ؟ " قالوا: بلى، قال: فأخذ بيد علي، فقال: " من كنت مولاه ، فعلي مولاه، اللهم وال من والاه ، وعاد من عاداه " قال: فلقيه عمر بعد ذلك، فقال: " له هنيئا يا ابن أبي طالب، أصبحت وأمسيت مولى كل مؤمن، ومؤمنة "
WANNAN SHI NE WANDA NA KAWO SHI A BAYA, SABODA WASIYYULLAH YA CE;
وهو في المسند (4: 281) بهذا الاسناد مثله,
MA'ANA HADISIN YANA CIKIN ALMUSNAD.
AMMA HADISIN DA'IFI NE SABODA A CIKIN ISNADINSA AKWAI ALIYU BIN ZAID, DA'IFI NE.
NURUDDEEN YA CE:
Malam Shu'aibu Al-Arna'uut yayi ta'aliki a kasan wannan Hadisin kuma a nafsin shafin yace: WANNAN HADISIN SAHIIHUN NE LI-GAIRIHI kuma saboda a cikin sanadin akwai Aliyyubn Zaid Dha'ifi ne.
GA NAN MAGANAR SHU'AIBUL ARNA'U'D GABA 'DAYANTA:
(2) صحيح لغيره، وهذا إسناد ضعيف من أجل علي بن زيد- وهو ابن جدعان - وباقي رجاله ثقات رجال الشيخين، غير حماد بن سلمة، فمن رجال مسلم. عفان : هو ابن مسلم الصفار.=
= وأخرجه ابن أبى شيبة 12/78 عن عفان ، بهذا الإسناد.
وأخرجه ابن ماجه (116) ، وعبد الله بن أحمد في زوائده على فضائل الصحابة لأبيه (1042) من طريقين، عن حماد، به.
وأخرجه النسائي في "الكبرى" (8473) بنحوه، والدولابي في "الأسماء والكنى" 1/160 مختصرا من طريق أبي إسحاق، عن البراء، به.
TO SHI MA BARI MU BI MAGANARSA DALLA - DALLA, YA CE:
وأخرجه ابن أبى شيبة 12/78 عن عفان ، بهذا الإسناد.
MA'ANA IBNU ABI SHAIBAH BA YA RUWAITO SHI, DA WANNAN ISNADIN. GA SHI KAMAR HAKA:
حدثنا عفان قال ثنا حماد بن سلمة قال : أخبرنا علي بن زيد عن عدي بن ثابت عن البراء ، قال : كنا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم في سفر ، قال : فنزلنا بغدير خم ، قال : فنودي : الصلاة جامعة ، وكسح لرسول الله صلى الله عليه وسلم تحت شجرة فصلى الظهر فأخذ بيد علي فقال : " ألستم تعلمون أني أولى بالمؤمنين من أنفسهم ، قالوا : بلى ، قال : ألستم تعلمون أني أولى بكل مؤمن من نفسه ، قالوا : بلى قال : فأخذ بيد علي فقال : الله من كنت مولاه فعلي مولاه ، اللهم وال من والاه وعاد من عاداه " ، قال : فلقيه عمر بعد ذلك فقال : هنيئا لك بابن أبي طالب : أصبحت وأمسيت مولى كل مؤمن ومؤمنة.
HAKA HADISIN YAKE IRI 'DAYA DA NA CIKIN MUSNAD, WANDA A CIKIN ISNADINSA AKWAI ALIYU BIN ZAID, DA'IFI NE.
SA'ANNAN YA CE:
وأخرجه ابن ماجه (116) ، وعبد الله بن أحمد في زوائده على فضائل الصحابة لأبيه (1042) من طريقين، عن حماد، به.
MA'ANA IBNU MAJAH MA YA RUWAITO SHI.
GA SHI KAMAR HAKA:
116 - حدثنا علي بن محمد . حدثنا أبو الحسين . أخبرني حماد بن سلمة عن علي بن زيد بن جدعان عن عدي بن ثابت عن البراء بن عازب قال: - أقبلنا مع رسول الله صلى الله عليه و سلم في حجته التي حج . فنزل في بعض الطريق . فأمر الصلاة جامعة . فأخذ بيد علي فقال ( ألست أولى بالمؤمنين من أنفسهم ؟ ) قالوا بلى . قال ( ألست أولى بكل مؤمن من نفسه ؟ ) قالوا بلى . قال ( فهذا ولي من أنا مولاه . اللهم وال من والاه . اللهم عاد من عاداه)
NA ABDULLAHI BIN AHMAD KUWA MUN AMBACE SHI A BAYA.
TAMBAYARMU A NAN ITA CE:
INA MAGANAR ''BAI'AR UMAR (RA)'' A CIKIN HADISIN???!
SA'ANNAN YA CE:
وأخرجه النسائي في "الكبرى" (8473) بنحوه،
MA'ANA NASA'I MA YA RUWAITO SHI A CIKIN SUNANUL KUBRA, GA SHI KAMAR HAKA:
8473 - أخبرنا أبو داود قال حدثنا عمران بن أبان قال حدثنا شريك قال حدثنا أبو إسحاق عن زيد بن يثيع قال : سمعت علي بن أبي طالب يقول على منبر الكوفة إني منشد الله رجلا ولا أنشد إلا أصحاب محمد صلى الله عليه و سلم من سمع رسول الله صلى الله عليه و سلم يقول يوم غدير خم من كنت مولاه فعلي مولاه اللهم وال من والاه وعاد من عاداه فقام ستة من جانب المنبر وستة من الجانب الآخر فشهدوا أنهم سمعوا رسول الله صلى الله عليه و سلم يقول ذلك قال شريك فقلت لأبي إسحاق هل سمعت البراء بن عازب يحدث بهذا عن رسول الله صلى الله عليه و سلم قال نعم قال أبو عبد الرحمن عمران بن أبان ليس بقوي في الحديث
TAMBAYARMU A NAN ITA CE:
INA MAGANAR ''BAI'AR UMAR (RA)'' A CIKIN HADISIN???!
SA'ANNAN YA CE:
والدولابي في "الأسماء والكنى" 1/160 مختصرا من طريق أبي إسحاق، عن البراء، به.
MA'ANA DULABI MA YA RUWAITO SHI:
حدثني أحمد بن يحيى الصوفي قال : حدثنا إبراهيم بن محمد بن ميمون قال : حدثنا أبو حنيفة سعيد بن بيان سابق الحاج ، عن أبي إسحاق السبيعي عن البراء بن عازب قال : قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : « من كنت مولاه فعلي مولاه »
TAMBAYARMU A NAN ITA CE:
INA MAGANAR ''BAI'AR UMAR (RA)'' A CIKIN HADISIN???!
KAI NURU ABIN DA KA KASA GANEWA SHI NE; RASHIN SANIN ''MUS'DALAHAT'' NA MALAMAN HADISI. ABIN DA SUKE BAYYANA MAKA SHI NE; HADISIN;
من كنت مولاه فعلي مولاه.
INGANTACCE NE. AMMA K'ARIN MAGANAR ''BAI'AR UMAR'', SAI KA NEMO WANI ISNADIN DA ZAI TABBATAR MAKA WANNAN LAFAZI NA ''BAI'AR UMAR''. IN BA HAKA BA YANA NAN A MATSAYINSA NA DA'IFI. SABODA A CIKIN ISNADINSA AKWAI ALIYU BIN ZAID, DA'IFI NE, AMMA LAFAZIN ''MAN KUNTU MAULAHU ...'' YA TABBATA, AMMA SABODA WANI HADISIN DABAN, BA SABODA WANNAN ISNADIN BA.
KUMA BABU WANNAN K'ARIN A CIKIN HADISAN DA SHI ARNA'U'D YA YI IHALA ZUWA GARESU KAMAR YADDA YA BAYYANA A FILI BISA YADDA NA KAWO.
IN KUMA AKWAI MUNA SAURARO???!
SA'ANNAN KA CE:
Allaamah Abul-Muzaffar Sibt Ibnul-Jauziy AL-Hanafiy wanda ya yi wafati hijra na da (654), bayan ya ya kawo wannan Hadisin na Gadiir da Bai'ar Umar din ta fuskoki daban-daban sai yace: Kuma dukkanin wannan ruwayar Ahmad bn Hanbali ya fitar da ita a cikin Fadhaa'il tare da wadannan Karin,...
TAMBAYA: INA SHI WANNAN K'ARIN A CIKIN MUSNAD AHMAD 'DIN, SHIN SHI NE WANDA YAKE CIKIN HADISIN ALIYU BIN ZAID, WANDA MUN RIGA MUN SAN MATSAYINSA, KO KUMA BA SHI BA NE SAI KA KAWO MANA SHI, TARE DA BAYANIN INGANCINSA???
HADISIN BARA'U BIN AZIB (RA) NA CIKIN MUSNAD DA'IFI NE KAMAR YADDA YA GABATA. IN KUMA SHI SIB'DU IBNIL JAUZIY YA INGATASHI SAI KA YI MANA BAYANIN YADDA YA ZAMA INGANTACCEN DALLA - DALLA.
SA'ANNAN KA NUNA CEWA; ALIYU BIN ZAID BA DA'IFI BA NE, HAR KA KAWO MAGANGANU WASU MALAMAI AKANSA, TO YAYA ZA KA YI DA WA'DANNAN MAGANGANUN MALAMAN DA SUKE TABBATAR DA RAUNIN NASA???
GA SU KAMAR HAKA:
ذكره محمد بن سعد في الطبقة الرابعة من أهل البصرة وقال ولد وهو أعمى وكان كثير الحديث وفيه ضعف ولا يحتج به
IBNU SA'AD YA CE: DA'IFI NE, BA A KAFA HUJJA DA SHI.
وقال صالح بن أحمد عن أبيه ليس بالقوي وقد روى عنه الناس
AHMAD YA CE: BA SHI DA K'ARFI.
وقال أحمد ليس بشيء وقال حنبل عن أحمد ضعيف الحديث
AHMAD YA CE: SHI BA KOMAI BA NE. A RUWAYAR HANBAL YA CE: HADISINSA MAI RAUNI NE.
وقال معاوية ابن صالح عن يحيى ضعيف
YAHYA BIN MA'IN YA CE: DA'IFI NE.
وقال عثمان الدارمي عن يحيى ليس بذاك القوي
YAHYA BIN MA'IN YA CE: BA KAMAR MAI K'ARFI YAKE BA.
وقال بن أبي خيثمة عن يحيى ضعيف في كل شيء وفي رواية عنه ليس بذاك وفي رواية الدوري ليس بحجة وقال مرة ليس بشيء
YAHYA YA CE: DA'IFI NE A KOMAI. A WATA RUWAYAR YA CE: BA KAMAR HAKA YAKE BA (BA MAI K'ARFI BA).
A RUWAYAR DURIY YA CE: SHI BA HUJJA BA NE.
A WANI LOKACIN KUMA YA CE: SHI BA KOMAI BA NE.
وقال العجلي كان يتشيع لا بأس به وقال مرة يكتب حديثه وليس بالقوي
IJLIY YA CE: 'DAN SHI'A NE, BABU LAIFI DA SHI, A WANI LOKACIN KUMA YA CE: ANA RUBUTA HADISINSA AMMA BA SHI DA K'ARFI.
وقال الجوزجاني واهي الحديث ضعيف وفيه ميل عن القصد لا يحتج بحديثه
AL- JUZAJANIY YA CE: MAI RAUNIN HADISI NE, DA'IFI. KUMA YANA DA KARKATACCEN NUFI BA A KAFA HUJJA DA HADISINSA.
وقال أبو زرعة ليس بقوي
ABU ZUR'AH YA CE: BA SHI DA K'ARFI.
وقال أبو حاتم ليس بقوي يكتب حديثه ولا يحتج به
ABU HATIM YA CE: BA SHI DA K'ARFI ANA DAI RUBUTA HADISINSA NE AMMA BA A KAFA HUJJA DA SHI.
وقال الترمذي صدوق الا أنه ربما رفع الشيء الذي يوقفه غيره
TIRMIZIY YA CE: SADUK'I NE, SAI DAI SAU DA YAWA YA KAN MAI DA MAUK'UFI YA ZAMA MARFU'I. WATO YANA MAI DA MAGANAR SAHABI TA ZAMA MAGANAR ANNABI (SAW).
وقال النسائي ضعيف
NASA'I YA CE: DA'IFI NE.
وقال بن خزيمة لا أحتج به لسوء حفظه
IBNU KHUZAIMA YA CE: BA ZAN KAFA HUJJA DA SHI BA, SABODA MUNIN HADDARSA.
وقال الحاكم أبو أحمد ليس بالمتين عندهم
ALHAKIM YA CE: BA MAI K'ARFI BA NE A WAJEN MALAMAN HADISI.
وقال الدارقطني أنا أقف فيه لا يزال عندي فيه لين
DARAK'U'DNIY YA CE: NI NA DAKATA GAME DA SHI, BAI GUSHE BA YANA DA RAUNI A WAJENA.
وقال سليمان بن حرب عن حماد بن زيد ثنا علي بن زيد وكان يقلب الأحاديث وفي رواية كان يحدثنا اليوم بالحديث ثم يحدثنا غدا فكأنه ليس ذلك
HAMMAD BIN ZAID YA CE: YA KASANCE YANA JUYA HADISAI, A WATA RUWAYAR KUMA YA CE: YA KASANCE YAU ZAI BA MU HADISI GOBE KUMA SAI YA BA MU SHI, KAMAR BA NA JIYAN BA.
وقال عمرو بن علي كان يحيى بن سعيد يتقي الحديث عن علي بن زيد
YAHYA BIN SA'ID YANA JIN TSORON HADISI IN DAGA ALIYU BIN ZAID YAKE.
وقال يزيد بن زريع رأيته ولم أحمل عنه لأنه كان رافضيا
YAZID BIN ZURAI'I YA CE: NA GAN SHI AMMA BAN 'DAUKI HADISI DAGA WAJENSA BA, SABODA RAFIDI NE.
MALAMAN HADISI SUN YI ITTIFAK'I AKAN CEWA; RAFIDA MAK'ARYATA NE.
وقال أبو سلمة كان وهيب يضعف علي بن زيد
WUHAIBU YA KASANCE YANA RAUNATA ALIYU BIN ZAID.
وقال ابن حبان يهم ويخطىء فكثر ذلك منه فاستحق الترك
IBNU HIBBAN YA CE: YANA WAHAMI ('DIMUWA) A CIKIN HADISI KUMA YANA KUSKURE A CIKINSA. HAR HAKAN YA YI YAWA A WAJENSA. DON HAKA YA CANCANCI A WATSAR DA SHI. WATO A BAR HADISINSA.
DUBA WA'DANNAN MAGANGANU A CIKIN ''TAHZIBUL KAMAL'' NA MIZZIY, DA ''TAHZIBUT TAHZIB'' NA IBNU HAJAR A TARJAMAR SHI ALIYU BIN ZAID BIN JUD'AN.
WANNAN YAKE NUNA CEWA; MALAMAN HADISI SUN YI KUSAN YIN IJMA'I AKAN RAUNIN ALIYU BIN ZAID.
TO JAMA'A, KU GAYA MIN; TA YAYA HADISIN WANNAN MUTUMIN ZAI ZAMA SAHIHI INGANTACCE??!!
TO NURA, KA GA FA GOGAN NAKA MUN 'DORA SHI A SIKELI YA FA'DI BA NAUYI.
(1) SHI RAFIDI NE. RAFIDA KUMA MAK'ARYATA NE.
(2) BA SHI DA HADDA MAI KYAU KO KA'DAN.
DA WANNAN ZAMU TABBATAR DA CEWA; MAGANAR ''BAI'AR UMAR (RA) GA ALIYU (RA)'' K'ARYA CE, RAFIDA NE SUKA K'IRK'IRETA, SUKA RA'BATA DA HADISIN ''MAN KUNTU MAULAHU...''
SA'ANNAN KA CE:
Mafi jullin masu kawo raunin Aliyyu bn Zaid, suna kawowa ne domin shi Shii'a ne kuma yayi kaurin suna ana kiransa Raafidi...
WANNAR MAGANAR K'ARYA CE. SABODA MUTUM 2 NE KAWAI SUKA AMBACI SHI'ANCINSA; SUNE YAZID BIN ZURAI'I DA AL- IJLIY.
SA'ANNAN KA CE:
Don haka a gurguje wannan Hadisin na Bai'ar Umar ga Imaam Aliy ingantacce ne ta wasu fuskokin Sanadan wanda babu wanda ya isa ya kawar da ingancinsu.
WANNAR MAGANAR K'ARYA CE. SABODA GA SHI TA BAYYANA CEWA; RAFIDI ALIYU BIN ZAIDU NE YA K'ARA MAGANAR BAI'AR UMAR 'DIN A CIKIN HADISI.
DON HAKA MAGANAR ''BAI'AR UMAR (RA) WA ALIYU (RA)'' K'ARYA CE!!!
ALHAMDU LILLAH.
NA 1, TUN A BAYA MUN TABBATAR DA CEWA; MAGANAR BAI'AR UAMAR (RA) WA ALIYU (RA) WACCE IMAMU AHMAD (R) YA RUWAITO A CIKIN ''MUSNAD'' BA TABBATACCIYA BA CE. SABODA ALIYU BIN ZAIDU NE KAWAI YA RUWAITO SHI. SHI KUMA MARUWAICI NE DA MALAMAN HADISI SUKA YI KUSAN IJMA'I AKAN RAUNINSA, KAMAR YADDA YA GABATA A BAYA. AMMA SHI NURU YANA DA WATA SHUBUHA, WATO ITA CE; MAGANAR AL- ARNA'U'D WANDA YA YI TAHK'IK'IN ''MUSNADU AHMAD'', INDA YA CE:
" صحيح لغيره وهذا إسناد ضعيف من أجل علي بن زيد"
WANNAR MAGANA TA ZAMA SHUBUHA WA NURU, SABODA RASHIN SANIN ILMIN HADISI; ''MUS'DALAHUL HADIS''.
SAU DA YAWA NAKAN YI ISHARA WA NURA CEWA; BA DA K'A'IDA 'DAYA KAWAI AKE INGANTA HADISI BA. ANA DUBA HADISI NE TA KOWACE FISKA KAFIN A YI MASA HUKUNCI DA INGANCI KO RASHIN INGANCINSA.
YA KAMATA KA LURA DA MAGANAR MALAM ARNA'U'D DA KYAU??!
CEWA YA YI:
" صحيح لغيره.
MA'ANA HADISIN INGANTACCE NE, AMMA SABODA WANI HADISIN DABAN.
TO SAI MUKA KOMA MUKA NEMO WANNAN HADISI DABAN 'DIN DA A DALILINSA NE SHI WANNAN YA ZAMA SAHIHI, MUSAMMAN WA'DANDA SHI ARNA'U'D YA YI IHALA ZUWA GARESU. GA SU KAMAR HAKA:
وأخرجه ابن أبى شيبة 12/78 عن عفان ، بهذا الإسناد.
MA'ANA IBNU ABI SHAIBAH BA YA RUWAITO SHI, DA WANNAN ISNADIN. GA SHI KAMAR HAKA:
حدثنا عفان قال ثنا حماد بن سلمة قال : أخبرنا علي بن زيد عن عدي بن ثابت عن البراء ، قال : كنا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم في سفر ، قال : فنزلنا بغدير خم ، قال : فنودي : الصلاة جامعة ، وكسح لرسول الله صلى الله عليه وسلم تحت شجرة فصلى الظهر فأخذ بيد علي فقال : " ألستم تعلمون أني أولى بالمؤمنين من أنفسهم ، قالوا : بلى ، قال : ألستم تعلمون أني أولى بكل مؤمن من نفسه ، قالوا : بلى قال : فأخذ بيد علي فقال : الله من كنت مولاه فعلي مولاه ، اللهم وال من والاه وعاد من عاداه " ، قال : فلقيه عمر بعد ذلك فقال : هنيئا لك بابن أبي طالب : أصبحت وأمسيت مولى كل مؤمن ومؤمنة.
TO KA GA SHI WANNAN IRI 'DAYA YAKE DA NA CIKIN MUSNAD, WATO A CIKIN ISNADINSA AKWAI ALIYU BIN ZAID, HUKUNCINSU 'DAYA NE WATO DA'IFI NE.
SA'ANNAN YA CE:
وأخرجه ابن ماجه (116) ، وعبد الله بن أحمد في زوائده على فضائل الصحابة لأبيه (1042) من طريقين، عن حماد، به.
MA'ANA IBNU MAJAH MA YA RUWAITO SHI.
GA SHI KAMAR HAKA:
116 - حدثنا علي بن محمد . حدثنا أبو الحسين . أخبرني حماد بن سلمة عن علي بن زيد بن جدعان عن عدي بن ثابت عن البراء بن عازب قال: - أقبلنا مع رسول الله صلى الله عليه و سلم في حجته التي حج . فنزل في بعض الطريق . فأمر الصلاة جامعة . فأخذ بيد علي فقال ( ألست أولى بالمؤمنين من أنفسهم ؟ ) قالوا بلى . قال ( ألست أولى بكل مؤمن من نفسه ؟ ) قالوا بلى . قال ( فهذا ولي من أنا مولاه . اللهم وال من والاه . اللهم عاد من عاداه)
HADISIN ABDULLAHI BIN AHMAD KUWA SHI NE DAI HADISIN ALIYU BIN ZAIDU, SHI MA IRI 'DAYA YAKE DA NA CIKIN MUSNAD AHMAD, HUKUNCINSU 'DAYA, WATO DA'IFI NE.
SA'ANNAN YA CE:
وأخرجه النسائي في "الكبرى" (8473) بنحوه،
MA'ANA NASA'I MA YA RUWAITO SHI A CIKIN SUNANUL KUBRA, GA SHI KAMAR HAKA:
8473 - أخبرنا أبو داود قال حدثنا عمران بن أبان قال حدثنا شريك قال حدثنا أبو إسحاق عن زيد بن يثيع قال : سمعت علي بن أبي طالب يقول على منبر الكوفة إني منشد الله رجلا ولا أنشد إلا أصحاب محمد صلى الله عليه و سلم من سمع رسول الله صلى الله عليه و سلم يقول يوم غدير خم من كنت مولاه فعلي مولاه اللهم وال من والاه وعاد من عاداه فقام ستة من جانب المنبر وستة من الجانب الآخر فشهدوا أنهم سمعوا رسول الله صلى الله عليه و سلم يقول ذلك قال شريك فقلت لأبي إسحاق هل سمعت البراء بن عازب يحدث بهذا عن رسول الله صلى الله عليه و سلم قال نعم قال أبو عبد الرحمن عمران بن أبان ليس بقوي في الحديث
SA'ANNAN YA CE:
والدولابي في "الأسماء والكنى" 1/160 مختصرا من طريق أبي إسحاق، عن البراء، به.
MA'ANA DULABI MA YA RUWAITO SHI:
حدثني أحمد بن يحيى الصوفي قال : حدثنا إبراهيم بن محمد بن ميمون قال : حدثنا أبو حنيفة سعيد بن بيان سابق الحاج ، عن أبي إسحاق السبيعي عن البراء بن عازب قال : قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : « من كنت مولاه فعلي مولاه »
TO GAME HADISIN CIKIN MUSNAD AHMAD MAI DA'IFIN ISNADI, ARNA'U'D YA CE;
" صحيح لغيره وهذا إسناد ضعيف من أجل علي بن زيد"
MA'ANA HADISIN INGANTACCE NE, AMMA SABODA WANI HADISIN DABAN.
TO GA NAN WANIN NASA MUN KAWOSU A SAMA, DA MUKA BI SU 'DAYA BAYAN 'DAYA; WANDA KE CIKIN ''SUNANU IBNI MAJAH'' DA ''SUNANUL KUBRA'' NA NASA'I, DA ''AL'ASMA'U WAL KUNA'' NA DULABIY, SAI MUKA SAMU LAFAZIN HADISIN YA SHA BAMBAM DA NA CIKIN ''MUSNAD AHMAD''. BANBANCIN SHI NE; A CIKINSU KWATA - KWATA BABU MAGANAR ''BAI'AR UMAR''. KAWAI ZAKA SAMU WANNAR MAGANA CE A CIKIN HADISIN ALIYU BIN ZAID. SABODA HAKA ABIN DA YA ZO A CIKIN HADISIN ALIYU BIN ZAID WANDA YAKE KAMAR HAKA:
كنا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم في سفر، فنزلنا بغدير خم، فنودي فينا: الصلاة جامعة، وكسح لرسول الله صلى الله عليه وسلم تحت شجرتين، فصلى الظهر، وأخذ بيد علي رضي الله عنه، فقال: " ألستم تعلمون أني أولى بالمؤمنين من أنفسهم ؟ " قالوا: بلى، قال: " ألستم تعلمون أني أولى بكل مؤمن من نفسه ؟ " قالوا: بلى، قال: فأخذ بيد علي، فقال: " من كنت مولاه ، فعلي مولاه، اللهم وال من والاه ، وعاد من عاداه "
WANNAN NE SAHIHUN LI GAIRIHIN, MA'ANA SAHIHI NE SABODA WANINSA, KAMAR YADDA ARNA'U'D YA FA'DA. SABODA NA KAWO MANA WANIN NASA KUMA ISNADINSA AKWAI INGANCI.
AMMA K'ARIN DA YAKE CIKIN HADISIN ALIYU BIN ZAID NA BAI'AR UMAR:
قال: فلقيه عمر بعد ذلك، فقال: " له هنيئا يا ابن أبي طالب، أصبحت وأمسيت مولى كل مؤمن، ومؤمنة "
WANNAN KAM SAM BABU SHI A CIKIN HADISIN DA YA INGANTA, BARE SHI WANNAN 'DIN YA ZAMA ''SAHIHUN LI GAIRIHI'' WATO INGANTACCE SABODA WANINSA. KUMA SHI MALAM ARNA'U'D DUK DA CEWA YA BAR ABIN A DUNK'ULE, BA NA TUNANIN YANA NUFIN HAR WANNAN K'ARIN SHI MA SAHIHUN LI GAIRIHI NE. IN KUWA HAKAN YAKE NUFI, TO LALLAI YA YI KUSKURE. DON HAKA K'ARIN DAKE CIKIN HADISIN ALIYU BIN ZAID NA BAI'AR UMAR (RA) YANA NAN A MATSAYINSA NA FARKO NA RASHIN INGANCI.
K'ARIN BAI'AR UMAR (RA) NA CIKIN HADISIN ALIYU BIN ZAID BA INGANTACCE BA NE:
DALILAI AKAN RASHIN INGANCIN WANNAN K'ARIN:
قال: فلقيه عمر بعد ذلك، فقال: " له هنيئا يا ابن أبي طالب، أصبحت وأمسيت مولى كل مؤمن، ومؤمنة "
(1) ALIYU BIN ZAIDU NE KAWAI YA KA'DAITA DA WANNAN K'ARIN, SHI KUMA MARUWAICI NE MAI RAUNI (DA'IFI).
(2) WANNAN K'ARIN ''MUNKARI'' NE, WATO MUMMUNA NE ABIN K'I. SABODA WANDA YA KA'DAITA DA SHI DA'IFIN MARUWAICI NE, WATO SHI NE ALIYU BIN ZAID.
AL- SAKHAWIY YA CE:
وأما إذا انفرد المستور أو الموصوف بسوء الحفظ أو المضعف في بعض مشايخه خاصة أو نحوهم ممن لا يحكم لحديثهم بالقبول بغير عاضد يعضده بما لا متابع له ولا شاهد فهذا أحد قسمي المنكر وهو الذي يوجد إطلاق المنكر عليه لكثير من المحدثين كأحمد والنسائي
YA CE:
AMMA IDAN ''MASTURI'' YA KA'DAITA DA HADISI, KO WANDA AKA SIFFANTA SHI DA MUNIN HADDA KO WANDA AKA RAUNATA SHI A WASU MALAMANSA KO MAKAMANCINSU DAGA CIKIN WA'DANDA HADISINSU BAI KAI A YI MASA HUKUNCIN KAR'BUWA BA, IN BA TARE DA WANI MAI K'ARFAFAWA DA ZAI K'ARFAFA SHI BA. WATO WANDA BA SHI DA ''MUTABI'I'' KO SHAIDA. TO WANNAN SHI NE 'DAYA DAGA CIKIN KASHI 2 NA HADISI MUNKARI, KUMA SHI NE WANDA AKA SAMU MALAMAN HADISI MASU YAWA IRIN SU AHMAD DA NASA'I SUKE KIRANSA DA ''MUNKARI''.
DUBA ''FATHUL MUGITH'' NA SAKHAWIY 1/ 235, DA ''AL- NUKAT'' NA IBNU HAJAR 2/ 152.
DA WANNAN NE YA TABBATA CEWA; MAGANAR BAI'AR UMAR (RA) WA ALIYU (RA) WANDA YA ZO A CIKIN HADISIN ALIYU BIN ZAID ''MUNKARI'' CE. WATO RUWAYA CE MUMMUNIYA ABIN K'I, SABODA ALIYU BIN ZAIDU NE KAWAI YA KA'DAITA DA ITA, BABU WANNAR MAGANA A CIKIN DUKKAN SAURAN HADISAN GADEER SAI A NA ALIYU BIN ZAID. SHI KUMA DA'IFIN MARUWAICI NE A WAJEN MALAMAN HADISI.
NA 2, ABIN DA KA KAWO DAGA GAZALIY, RAZIY, SHAHARASTANIY, DUK BA SHI DA WANI AMFANI. SABODA RASHIN INGANCIN HADISIN. KUMA CEWA DA KA YI; SUN INGANTA SHI K'ARYA KAKE YI MUSU.
NA 3, KA CE:
Hadisi na biyu kuwa, wanda na kawo nace Wasiyyullah ya yi tahqiqi akansa kuma ya inganta shi, shine wanda yace an fitar da shi ne daga Hudbah daga Hammaad ba wanda Ammar ya kawo ba daga Affaan daga Hammaad ba. Ga ingantacce Sanadin nan za kawo wanda ya fito daga Hudbah daga Hammaad din, wanda sanadinsa ingantacce ne, kuma mazajen Hadisin dukkaninsu Thiqaat ne...
DUK CIKIN LITTAFIN FADA'ILU SAHABA NA IMAMU AHMAD BABU WANNAN HADISIN. WATO RUWAYAR HUDBAH. GA WA'DANDA SUKE A CIKIN LITTAFIN, KUMA DUKKANSU BIYU TA HANYAR DA'IFIN MARUWAICIN NAN NE, WATO ALIYU BIN ZAIDU:
1016 - حدثنا عبد الله قثنا أبي نا عفان قثنا حماد بن سلمة قال أنا علي بن زيد عن عدي بن ثابت عن البراء بن عازب قال : كنا مع رسول الله صلى الله عليه و سلم في سفر فنزلنا بغدير خم فنودي فينا الصلاة جامعة وكسح لرسول الله صلى الله عليه و سلم تحت شجرتين فصلى الظهر وأخذ بيد علي فقال ألستم تعلمون اني أولى بالمؤمنين من أنفسهم قال بلى قال ألستم تعلمون إني أولى بكل مؤمن من نفسه قالوا بلى قال فأخذ بيد علي فقال اللهم من كنت مولاه فعلي مولاه اللهم وال من والاه وعاد من عاداه قال فلقيه عمر بعد ذلك فقال هنيئا لك يا بن أبي طالب أصبحت وأمسيت مولى كل مؤمن ومؤمنة
1042 - حدثنا إبراهيم قثنا حجاج قثنا حماد عن علي بن زيد عن عدي بن ثابت عن البراء وهو بن عازب قال : اقبلنا مع النبي صلى الله عليه و سلم في حجة الوداع حتى كنا بغدير خم فنودي فينا ان الصلاة جامعة وكسح لرسول الله صلى الله عليه و سلم تحت شجرتين فأخذ بيد علي فقال ألست أولى بالمؤمنين من أنفسهم قالوا بلى يا رسول الله قال هذا مولى من انا مولاه اللهم وال من والاه وعاد من عاداه فلقيه عمر فقال هنيئا لك يا بن أبي طالب أصبحت وامسيت مولى كل مؤمن ومؤمنة
IN AKWAI WANI HADISIN BA WA'DANNAN BA, TO KA KAWO SHI DA LARABCINSA TARE DA LAMBAR HADISIN??!!
HADISIN HUDBA DA WASIYYULLAH YA YI ISHARA GARE SHI, YANA NAN A CIKIN AL- SUNNA NA IBNU ABI ASIM. WASIYYULLAH YA CE:
واخرجه ابن ابي عاصم في السنة (ل 134 ب) عن شيخه هدبة عن حماد.
MA'ANA HADISIN YANA CIKIN AL- SUNNA NA IBNU ABI ASEEM.
TO GA HADISIN KAMAR HAKA:
1363- حدثنا هدبة بن خالد ، حدثنا حماد بن سلمة عن علي بن زيد وأبي هارون عن عدي بن ثابت عن البراء قال قال رسول الله صلى الله عليه وسلم لعلي هذا مولى من أنا مولاه أو ولي من أنا مولاه.
DUBA AL- SUNNA, 2/ 605 'DAB'AR ''ALMAKTABUL ISLAMI'' TAKHARIJIN ALLAMATUL ALBANIY, BUGU NA FARKO 1400H - 1980M.
SAI KA NUNA MANA ''BAI'AR UMAR'' 'DIN???
IN KUMA AKWAI WANI LAFAZIN DABAN, KA KAWO MANA SHI A CIKIN LARABCINSA DA LITTAFIN DA YAKE DA KUMA DA LAMBAR HADISIN??!
SA'ANNAN KA CE:
Wannan Hadisin Al-Haafiz Abul-Abbaas Ash-shaibaaniy An-nasawiy wanda yayi wafati bayan hijira da shekara 303 ya fitar das hi a cikin littafinsa Musnad Abiil-Abbaas Ashshaibaaniy. Kuma dukkanin Malaman da muka ruwaito suna nunawa suce: Sahiihun li-ghairihi, wasu kuma suce ingantacce ne ta hanyar Hudbah daga Hammaad, to dogaron su dai wannan Sanadin ne ba wani ba, bawai kai wanda ka labewa ba
(1) KA KAWO MANA HADISIN ABUL ABBAS AL- SHAIBANIN??!
(2) KA KAWO MANA MAGANGANUN MALAMAN DA SUKA CE; SAHIHUN LI GAIRIHIN NE??!
SA'ANNAN KA CE:
mun kawo maganar Malamin ku ne da yake tabbatar da ingancin Hadisin bai'ar Umar din, kuma ko ka ki ko ka so, Abul-Muzaffar Malaminka ne, domin ya gabace ka, yafi ka ilimi, magabatan Sunna suna dogara da maganarsa, …………………………,
ABUL MUZAFFAR KO MALAMIN SUNNA NE, KO NA SHI'A NE, IN YA KAWO MAGANA MUKA GA TA DACE DA DADAI MU KAR'BA IN KUMA TA SA'BA MA DADAI MU JEFATA A BOLA.
(4) A NASIHARKA DA KA YI MINI KA YI MAGANA AKAN WANNAR MAGANA TAKA:
Mafi jullin masu kawo raunin Aliyyu bn Zaid, suna kawowa ne domin shi Shii'a ne kuma yayi kaurin suna ana kiransa Raafidi..
ME KAKE NUFI DA MAFI JULLIN MASU KAWO RAUNIN ALIYU BIN ZAID??!
MAFI JULLI BA SHI NE MAFI YAWA BA??
TO IN HAKA NE, TABBAS K'ARYA KAKE YI. SABODA KAI MA YANZU GUDA 4 KAWAI KA KAWO. TO MUTUM 4 DAGA CIKIN MUTUM KUSAN 20 KO FIYE DA HAKA NA WA'DANDA SUKA RAUNATA SHIN, SU 4 NE MAFI JULLINSU??!
WANNAN NE YASA NA K'ARYATAKA!!
KUMA NI DA FARKO ABIN DA YA SA NA CE MUTUM 2 NE, NA GA DUKKAN MAGANGANUN FARKO DA KA KAWO AKAN INGANCINSA KA 'DAUKO NE DAGA TAHZIBUT TAHZIB KO KAMAL, AMMA DA YAKE NA RITSAKA SAI KA NEMO WASU MAGANGANUN A CIKIN WASU LITTATAFAN DABAN.
A TAK'AICE DAI KO SU HU'DUN DA KA KAWON NE, IN KA CE; ''MAFI JULLI'' TO LALLAI KA TABBATA MAK'ARYACI, KO KUMA WANDA BAI SAN MA'ANAR KALMAR ''JULLI'' BA.
DON HAKA JAMA'A DA WANNAN NE MUKE K'ARA TABBATAR MUKU DA CEWA; MAGANAR BAI'AR UMAR (RA) WA ALIYU (RA) K'ARYA CE. SABODA RUWAYAR DA TAZO DA HAKAN MUNKARA CE. WATO MUMMUNIYA CE KUMA ABIN K'I!!