Bayan haka a wannan rubutu da kake yi kana kawo hadisai don tabbatar da FALALAR SHI'A da 'YAN SHI'A, to shi ne ni kuma zan fara raddin abin da kake kawowa ta hanyar sanar da kai matsayin Hadisan da kake kawowa don kafa hujja da su, alhali ba tare da ka tabbatar mana da ingancinsu ba. Ka sani QA'IDA ce a wajen Malaman Hadisi:
الكلام على فقه الحديث فرع عن ثبوته.
Ma'ana; ba ka kafa hujja da wani Hadisi akan wata mas'alar Addini, har sai ka tabbatar mana da INGANCINSA, don mu samu tabbacinsa daga Manzon Allah (saw).
1 - HADISI NA FARKO:
Wato na TAFSIRIN AYAR SURATUL BAYYINAH, Hadisi ne na KARYA. Kwata - kwata bai tabbata daga Manzon Allah (SAW) ba.
Hadisi ne da Ibn Jariir Al - Dabariy ya kawo a tafsirinsa, daga ALBAQIR, a cikin ISNADINSA akwai ABUL JARUUD, Ibn Ma'een da Abu Dawuud saka ce: MAKARYACI ne.
Ibn Hibban ya ce: RAFIDI ne yana KIRKIRAN Hadisi. Don haka Malaman Hadisi suka masa hukuncin NA KARYA ne.
HADISI NA 2:
Hadisi na gaba da ka ambata, wato wanda Dabaraaniy ya ruwaito shi a cikin AL'AUSAD, da ya tabbata, to da hujja ne akanku, ba wai hujjarku ba, don ai yanke Hadisin kayi, ba dukansa ka kawo shi ba. Ga yadda Hadisin yake, RUWAYAR UMMU SALMAH:
( يا علي, أنت وأصحابك في الجنة، أنت وشيعتك في الجنة، إلا أنه ممن يزعم أنه يحبك أقوام يضفزون الإسلام ثم يلفظونه ، يقرأون القرآن لا يجاوز تراقيهم ، لهم نبز, يقال لهم : الرافضة ، فإن أدركتهم فجاهدهم ، فإنهم مشركون .
فقلت : يا رسول الله ! ما العلامة فيهم ؟ قال : لا يشهدون جمعة ولا جماعة ، ويطعنون على السلف الأول )
To in ka duba wannar magana ZARGIN RAFIDA ('YAN SHI'A) ake yi, kuma da bayanin cewa, KARYA SUKE YI, su a hakikanin gaskiya ba SHI'AR ALIYU (ra) ba ne, kawai suna rayawa ne.
To duk da cewa wannan Hadisin hujjarmu ne akanku, amma mu ba ma farin ciki da shi, ba za mu kafa HUJJA da shi ba, saboda wannar magana KARYA ce aka jingina wa MANZON ALLAH (saw). Ga bayani kamar haka:
A cikin Isnadin Hadisin akawai SAWWAAR BIN MUS'AB. Mutum ne da ake TUHUMARSA da KARYA.
Bukahari yace: Hadisinsa abun QI ne.
Annasaa'iy yace: MATRUUKI ne, ma'ana malamai sun bar Hadisansa.
Ibn Hibbaan yace: ya kasance yana kawo hadisai MUNKARAI (abin kyama) ya jingina su ga Shahararrun Maruwaita, har ya kwanta ma rai cewa shi ne yake kirkiransu.
Hakiim yace: yana ruwaito Hadisai abin kyama daga A'amash, da Ibn Khalid, yana ruwaito Hadisan KARYA kuma daga Adiyyah. (wannan Hadisin kuwa daga Adiyyan ya ruwaito shi).
Shi kuma Adiyyan DA'IIFI ne a wajen malaman Hadisi. Duba TARJAMARSA ko cikin TAQREEB na IBN HAJAR.
Sa'annan shi ALFADLU BIN GANIM wanda ya riwaito shi daga SAWWAAR, shi ma DA'IIFI ne.
Yahya bin Ma'een yace: Shi ba komai ba ne, ma'ana ba a karbar Hadisinsa. Daraqudniy yace: ba shi da karfi (ma'ana; mai rauni ne). Khadibul Bagdadiy kuma yace: DA'IIFI NE.
Do haka Malaman Hadisi suka yi hukunci ma wannan Hadisi naka da cewa: MAUDUU'I NE, Ma'ana HADISIN KARYA NE.
HADISI NA 3:
ka kawo daga cikin littafin MAS'UUDIY, wato MURUUJUZ ZAHAB, GA ABIN DA YACE:
ووجدت في كتاب الأخبار لأبي الحسن علي بن محمد بن سليمان النوفلي عن صالح بن علي بن عطية الأصم قال: حدثنا عبد الرحمن بن العباس الهاشمي، عن أبي عون صاحب الدولة، عن محمد بن علي بن عبد الله بن العباس، عن أبيه، عن جده، عن العباس بن عبد المطلب، قال: كنت عند رسول الله صلى الله عليه وسلم إذ أقبل علي بن أبي طالب، فلما رآه أسفر في وجهه، فقلت: يا رسول الله، إنك لتسفر في وجه هذا الغلام، فقال: ياعم رسول الله، والله الله أشد حبا له مني، إنه لم يكن نبي إلا وذريته الباقية بعدي من صلبه، وإن ذريتي بعدي من صلب هذا، إنه إذا كان يوم القيامة دعي الناس بأسمائهم واسماء أمهاتهم سترا من الله عليهم، إلا هذا وشيعته فإنهم يدعون بأسمائهم السماء آبائهم لصحة ولادتهم.
Ni dai har yanzu ban samu wannar magana ba a cikin littatafan Hadisi, abin da yake nuna cewa Hadisin ba shi da ASALI. Hakan kuwa alama ce ta cewa Hadisin KIRKIRARRE NE. Abin da zai karfafa wannan kuwa, shi ne fadin shi AL- MAS'UUDIY:
ووجدت في كتاب الأخبار لأبي الحسن علي بن محمد بن سليمان النوفلي.
Ma'ana ya samu maganar ce a cikin littafin LABARAI, wanda sananne ne, irin wadannan littatafai na SHAFA LABARI SHUNI, KARYA SHI NE MAFI YAWAN ABIN DA KE CIKINSU.
HADISI NA 4:
Hadisi na gaba da ka kawo daga AL- SAWA'IQ na Ibn Hajar AL- HAITAMIY, ga abin da yace:
وأخرج الديلمي: يا علي إن الله قد غفر لك ولذريتك ولولدك ولأهلك ولشيعتك ولمحبي شيعتك فأبشر فإنك الأنزع البطين.
وهو ضعيف.
Da farko wani abu da ya kamata ka sani shi ne; Idan DAILAMIY ya ruwaito Hadisi a cikin littafinsa MUSNADUL FIRDAUSI, to alama ce ta rashin INGANCIN HADISIN. Wannan QA'IDA ce a wajen malaman Hadisi, saboda da ma littafin matattaran GURBATATTU da RUBABBUN Hadisai ne.
Na 2, sai ga shi mai littafin AL- SAWA'IQ da kansa bayan ya kawo Hadisin sai yace maka:
وهو ضعيف.
Ma'ana; mai RAUNI ne.
Amma kai kuma ba ka ambaci hakan ba, miye DALILI??
HADISI NA 5:
Hadisin da ka kawo daga littafin IBNUL ATHIIR, har yanzu ban same shi da ISNADINSA ba, haka kuma ban same shi cikin littatafan Hadisi ba, bare in samu maganganun malamai akansa. Ga dai yadda yake a cikin littafin, amma har yanzu dai bai kai ya zama hujja ba tukun, har sai ka tabbatar mana da INGANCINSA, don alamar Hadisin ba shi da ASALI.
وفي حديث علي [ قال له النبي صلى الله عليه وسلم : ستقدم على الله أنت وشيعتك راضين مرضيين ويقدم عليه عدوك غضابا مقمحين ثم جمع يده إلى عنقه يريهم كيف الإقماح ]
HADISI NA 6:
( إن أول أربعة يدخلون الجنة : أنا وأنت والحسن والحسين ، وذرارينا خلف ظهورنا ، وأزواجنا خلف ذرارينا ، وشيعتنا عن ايماننا وعن شمائلنا ) .
Wannan Hadisin KARYA ne. Bai tabbata daga Manzon Allah (SAW). A cikin ISNADINSA akwai; Muh'd bin Ubaidillah. Ga maganganun Malamai akansa:
قال يحيى بن معين: محمد بن عبيد الله ليس حديثه بشيء
قال ابو حاتم: ضعيف الحديث منكر الحديث جدا ذاهب
قال البخاري: منكر الحديث
قال الذهبي: ضعفوه
A karshe Zahabin yace:
وحرب أيضا متكلم فيه، والحديث باطل بهذا الاسناد.
To don Allah ina HUJJA a cikin wannan Hadisin.
HADISI NA 7:
قال النبي صلى الله عليه وسلم: ''والذي نفسي بيده إن هذا وشيعته لهم الفائزون يوم القيامة''
Wannan Hadisi asalinsa Ibn Asaakir ne ya ruwaito shi daga Jabir (RA), Suyudiy kuma ya kawo shi a cikin Tafsirinsa a Suratul BAYYINAH. Malaman Hadisi sun yi masa hukunci da cewa, MAUDU'I ne, ma'ana; HADISIN KARYA ne, mutumin da ya ruwaito shi daga Jabir shi ne Abu Azzubair, MUDALLIS ne, kuma yayi AN'ANA. Sauran RIJAALIN ISNADIN kuma ba su da TARJAMA. Ma'ana; ba a san ko su waye ba!
HADISI NA 8:
( شفاعتي لأمتي: من أحب أهل بيتي ، وهم شيعتي ) .
Wannan Hadisi ne mai RAUNI, a cikin ISNADINSA akwai ALQASIM BIN JA'AFAR. Khadibul Bagdadiy a TARJAMARSA yace:
"قدم بغداد وحدث بها عن أبيه عن جده عن ابائه نسخة أكثرها مناكير " .
Duba TARJAMAR ALQASIM A BABIN QAAFUN.
Don haka mutum ne da yake ruwaito MUNKARAN HADISAI, wannan kuma yana daga cikinsu kamar yadda Malamai suka bayyana.
MALAM NURA, LALLAI INA MAMAKINKU, TA YADDA KU KE SAURI GASKATA KARYA, WANDA HAKAN YA SA ADDININ RAFIDANCI YA GINU AKAN KARYA. TO GA SHI DAI DUKKAN HADISAN DA KUKE TINKAHO DA SU DUKANSU BA SU TABBATA DAGA MANZON ALLAH (SAW) BA, DUKA MAGANGANU NE KAWAI NA KARYA DON NUFIN RUSA ADDININ MUSLUNCI, DA SAUYA SHI DA WANI ABU DABAN.
WAI KU ME YA SA BA ZA KU YI KARATU KUSAN QA'IDOJIN ILMI BA NE, KAWAI KU ZO KUNA KAWO WA MUTANE HADISAN KARYA DA SUNAN HUJJAR ABIN DA KUKE TAFIYA AKAI.
TO ALLAH YA SHIRYAR DAMU, SAI A NEMO WASU HADISAN WADANNAN KAM BABU HUJJA KO MISQALA ZARRATIN A CIKINSU.

No comments:
Post a Comment