BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
JAMA'A ASSALAMU ALAIKUM!
KAMAR YADDA AKA SANI, KASHE HUSAINI (RA) YANA DAGA CIKIN MANYAN MASIFU DA SUKA SAMU WANNAN AL'UMMA. AMMA SAI DAI MAK'IYA MUSULUNCI SUN YI AMFANI DA WANNAR DAMA DON YA'DA GUBARSU A CIKIN AL'UMMAR MUSULMI. DON HAKA SUKA YI K'ARERAYI AKAN WANNAR FITINA, K'ARYAN DA BABU WANDA YA SAN IYAKARSA SAI ALLAH MA'DAUKAKIN SARKI.
WANNAN YA SA YA ZAMA WAJIBI A YI BAYANIN GASKIYAR ABIN DA YA FARU, DON HAKA A YAU ZAMU FARA MAGANA DA TANTANCE WANNAN TARIHI MAI MUHIMMANCI A WAJEN MAK'IYA ADDINI!!!
YA KAMATA MUTANE SU SANI, DUK WATA MUSIBA, A BAYAN MUSIBAN RASUWAR MANZON ALLAH (SAW) TAKE. HAKA KUMA A BAYAN KASHE KHALIFANSA UMAR (RA) TAKE, SA'ANNAN A BAYAN KASHE KHALIFAN MANZON ALLAH (SAW) USMANU (RA) TAKE.
DON HAKA DUKKAN MUSIBU DA SUKA SAMEMU A CIKIN MUSLUNCI, BA ABIN DA ZAMU CE SAI:
إنا لله وإنا إليه راجعون!!!
TARJAMAR HUSAINI (RA):
AN HAIFI HUSAINI (RA) A SHEKARA TA 2, BAYAN HIJIRA. YANA DAGA CIKIN YARA SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW). HAK'IK'A AN RUWAITO HADISAI DA DAMA DA SUKE BAYANIN FALALARSA, DA KUMA YADDA MANZON ALLAH (SAW) YAKE SONSA SHI DA 'DAN UWANSA HASSAN (RA).
LALLAI BABU WANI ABU DA AKA SAMU DA YAKE NUNA SHAGALTUWARSA DA LAMURAN SHUGABANCI A ZAMANIN KHULAFA'UR RASHIDUNA. SAI DAI YANA DAGA CIKIN SOJOJIN BABANSA ALIYU (RA), A LOKACIN MANYAN FITINUN NAN DA SUKA FARU.
A LOKACIN DA 'DAN UWANSA HASAN (RA) YA FIFITA YA MIK'A KHALIFANCI WA MU'AWIYA (RA), HUSAINI (RA) YA KASANCE YANA DAGA CIKIN MARASA GOYON BAYA. DON A LOKACIN DA HASAN (RA) YA BA SHI LABARIN CEWA YA RUBATA WA MU'AWIYA (RA) TAKARDAR SULHU. HUSAINI (RA) CEWA YA YI: INA HA'DAKA DA ALLAH, YANZU ZAKA GASKATA ZANCEN MU'AWIYA KA K'ARYATA ZANCEN ALIYU. SAI HASAN (RA) YA CE MASA: KA YI SHIRU! NI NA FIKA SANIN LAMARIN.
DUBA TARIKHU'D 'DABARIY.
LALLAI MU'AWIYA (RA) YA KASANCE YANA SADA ZUMUNCI WA HUSAINI (RA) KUMA YANA KYAUTATA MASA. TO A LOKACIN DA MU'AWIYA (RA) ZAI YI WASIYYAN KHALIFANCI MA 'DANSA YAZIDU A BAYANSA, HUSAINI (RA) YANA DAGA CIKIN MASU NUNA RASHIN GOYON BAYA. KUMA YA KASANCE AKWAI SADARWA A TSAKANINSA DA MUTANEN IRAK'I, MAGOYA BAYAN BABANSA. DON HAKA YA SA MU'AWIYA (RA) YA YI WASIYYA MA 'DANSA YAZIDU A LOKACIN MUTUWARSA YA CE: AMMA SHI HUSAINI LALLAI MUTANEN IRAK'I BA ZA SU BAR SHI BA, HAR SAI SUN SA SHI YA YI MAKA TAWAYE. TO IDAN YA YI MAKA TAWAYE, IN KA SAME SHI KA YI MASA AFUWA, DOMIN YANA DA DANGANTAKA MAI K'ARFI DA KAI, KUMA YANA DA HAK'K'I MAI GIRMA A KANKA.
DUBA 'DABARI DA IBNU KASIR A CIKIN AL- BIDAYAH.
MAFARIN FITINAR:
RASUWAR MU'AWIYA (RA) KE DA WUYA, SAI YAZIDU YA RUBUTA TAKARDA ZUWA GA GWAMNANSA NA MADINA; AL- WALEED BIN UTBAH BIN ABI SUFYAN, YANA BA SHI LABARIN RASUWAR MU'AWIYA (RA), KUMA YANA SON YA NEMI WA'DANDA BA SU YARDA DA NA'DIN DA BABANSA YA YI MASA BA, DA SU YI MASA MUBAYA'AH. NA GABA - GABANSU KUWA AKWAI HUSAINI (RA) DA ABDULLAHI BIN ZUBAIR (RA).
A LOKACIN DA AKA NEMI HAKAN A WAJENSU, SAI IBNU ZUBAIR (RA) YA CE: ZAN DUBA ZUWA DARE ZAN BA KU LABARIN RA'AYINA. SAI SUKA CE MASA; TO.
DA DARE YA YI KAWAI SAI YA FITA DAGA MADINA YA KAMA HANYAR MAKKAH, YA K'I YIN MUBAYA'A.
DA AKA ZO WAJEN HUSAINI (RA) AKA CE MASA KA YI MUBAYA'A. SAI YA CE: BA ZAN YI A 'BOYE BA, ZAN YI NE A BAYYANI A CIKIN MUTANE. SAI SUKA CE: TO.
SHI MA DARE NA YI, SAI YA BI BAYAN IBNU ZUBAIR (RA). YA FITA DA DARE YA NUFI MAKKA, TARE DA SHI AKWAI 'YA'YANSA DA 'YAN UWANSA DA MAFI YAWAN MUTANEN GIDANSA. BAI BI BABBAR HANYA BA, HAR YA ISA MAKKA, BA TARE DA BANU UMAYYA SUN BI BAYANSA BA, KO SUN TSARE SHI A HANYA BA.
DAGA LOKACIN DA LABARIN MUTUWAR MU'AWIYA (RA) DA RASHIN MUBAYA'AR IBNU ZUBAIR (RA) DA HUSAINI (RA) YA ISA WA MUTANEN KUFA, SAI SUKA K'ARA TAURIN KANSU DA NOK'EWA KAMAR YADDA SUKE A DA. KAWAI SAI SUKA FARA AIKA WA HUSAINI (RA) WASIK'U AKAI - AKAI, SUNA KIRANSA YA ZO GARESU, SUN YI MASA ALKAWARIN TAIMAKA MASA.
2- AIKIN MUSLIM BIN AK'EEL:
MUTANEN KUFA SUNA TA KIRAN HUSAINI (RA) AMMA SAI YA YI TAKA - TSAM -TAM, SAI YA AIKA 'DAN BAFFANSA MUSLIM BIN AK'EEL ZUWA KUFAN, DON YA JE YA TABBATAR DA GASKIYAR LAMARIN. TO YA JE SAI YA SAUKA A GIDAN HANI'I BIN URWAH, SAI MUTANEN KUFA SUKE TA FITOWA SUNA MASA MUBAYA'A A 'BOYE, 'DAI - 'DAIKU DA JAMA'A - JAMA'A.
TO A LOKACIN GWAMNAN KUFA SHI NE; ANNU'UMAN BIN BASHEER, SHI KUMA MUTUM NE MAI SANYI, DA LABARI YA SAME SHI SAI YA KAU DA KAI KAMAR BAI SANI BA, AMMA BAI GUSHE BA YANA UMURTANSU DA YIN BIYAYYA WA SHUGABA DA KUMA LIZIMTAR AL'UMMAR MUSULMI.
ANA HAKA SAI WANI YA SULALE YA KAI LABARI WA YAZIDU, TO JIN HAKA SAI YA CANJA GWAMNAN KUFA, SAI YA SA UBAIDULLAHI BIN ZIYAD, DA YANA GWAMNA NE A BASRA. SABODA SHI IBNU ZIYAD YA SAMU DAMAR GAMAWA DA TAURIN KAN 'YAN SHI'A A BASRAN. KAWAI SAI YA YI GAGGAWAN TAFIYA KUFA TARE DA MUTANE 10, SUN YI SHIGAN NINJA, SAI MUTANE SUKA YI TSAMMANIN HUSAINI (RA) NE. SAI MARABA SUKE TA YI MASA; MARABA DA ZUWA YA 'DAN MANZON ALLAH, KA YI KYAKKYAWAN ZUWA. HATTA SHI MA ANNU'UMAN BIN BASHEER GWAMNAN KUFAN BAI GANE SHI BA. SHI MA YA 'DAUKA HUSAININ NE. HAR YA HA'DA SHI DA ALLAH AKAN YA KOMA, SABODA TSORON FITINA.
IBNU ZIYAD YANA SAMUN GINDIN ZAMA SOSAI, SAI YA FARA MU'AMALANTAR MUTANEN KUFA DA GASKE. AMMA DUK DA HAKA YANA TA K'OK'ARIN NEMAN HA'DIN KAN MANYAN GARI, DA K'USOSHIN SHI'A. HAR YA JE YA GAIDA HANI'I BIN URWAH, MAI MASAUK'IN MUSLIM BIN AK'EEL DA YAYI RASHIN LAFIYA. AMMA DUK DA HAKA 'YAN SHI'AN SUN YI NIYYAN KASHE SHI, AMMA SAI SHI HANI'I YA K'I YARDA, KAR A KASHE SHI A GIDANSA. HAKA WANI BABBA A CIKINSU; SHAREEK BIN A'AWAR YA YI RASHIN LAFIYA SAI GWAMNA IBNU ZIYAD YA SO YA JE YA GAISHE SHI, AMMA SAI YA SHIRYA KASHE SHI, KUMA YA KWA'DAITAR DA MUSLIM BIN AK'EEL AKAN HAKAN, TO KAFIN YA JE DA KWANA 3 SAI YA RASU. SAI IBNU ZIYAD YA SO YA JE BISNE SHI, AMMA DA YA JI LABARIN ABIN DA SHAREEK YA SHIRYA MASA, SAI YA FASA. YA CE: WALLAHI HAR ABADA BA ZAN YI SALLAH WA GAWAR WANI 'DAN IRAK'I BA.
TO DAGA BAYA IBNU ZIYAD YA SAMU DAMAN GANO LAMARIN MUSLIM BIN AK'EEL, DA MASAUK'INSA, DA MAGOYA BAYANSA. HAR YA SA AKA KAMA HANI'I BIN URWAH MAI MASAUKINSA AKA TSARE SHI. TO HAKAN SAI YA TUNZURA WA'DANDA SUKA YI MA MUSLIM BIN AK'EEL MUBAYA'A KUSAN MUTUM 18,000. SAI YA FITO DA MUTUM 4000, SUKA YI K'AWANYA WA FADAR IBNU ZIYAD. ALHALI BA KOWA A TARE DA SHI SAI MASU TSARONSA MUTUM 30, DA MUTUM 20; DAGA CIKIN MANYAN GARI DA MUTANEN FADA DA BAYINSA. TO SAI MANYAN MUTANEN NAN SUKA SAMU DAMAN KASHE MA MUTANEN MUSLIM BIN AK'EEL GUIWA, KAWAI SAI SUKA WATSE SUKA BAR SHI. SHI KUMA SAI YA YI SAURI YA SHIGA GIDAN WATA TSOHUWA YA FAKE. KAWAI DAGA BAYA SAI AKA SAMU LABARINSA YANA GIDAN, SAI SUKA KASHE SHI TARE DA MAI MASAUK'INSA DA AKA KAMA HANI'I BIN URWAH.
DUBA TARIKHU'D 'DABARIY.
A BIMU A HANKALI, HAR ZUWA K'ARSHE, ZA A SHA MAMAKI; ANA TSAMMANIN WUTA A MAK'ERA SAI AKA SAMETA A MASAK'A.
No comments:
Post a Comment