BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
IBNU TAIMIYYA (R) YA CIGABA DA CEWA:
AMMA FA'DINSA (SAW):
((من كنت مولاه فعلي مولاه اللهم والِ من والاه وعادِ من عاداه، وانصر من نصره واخذل من خذله وأدر الحق معه كيفما دار))
DUK WANDA NA ZAMA MASOYINSA, TO ALIYU MASOYINSA NE. YA ALLAH KA SO WANDA YA SO SHI, KA K'I WANDA YA K'I SHI, KA TAIMAKI WANDA YA TAIMAKE SHI, KAR KA TAIMAKI WANDA YA K'I TAIMAKONSA. KUMA KA KEWAYA GASKIYA TARE DA SHI DUK INDA TA ZAGAYA.
WANNAN HADISI BA YA CIKIN MANYAN LITTAFAN HADISI SAI TIRMIZIY, KUMA BABU A CIKINSA SAI:
((من كنت مولاه فعلي مولاه))
DUK WANDA NA ZAMA MASOYINSA, TO ALIYU MASOYINSA NE.
AMMA K'ARIN A KANSA BA YA CIKIN HADISIN. AN TAMBAYI IMAMU AHMAD (R) GAME DA SHI, SAI YA CE:
(( الزيادة كوفية ))
MUTANEN KUFA NE SUKA K'ARA.
LALLAI KO SHAKKA BABU WANNAN K'ARIN K'ARYA NE, SABODA WASU DALILAI:
NA FARKO: ITA GASKIYA BA TA JUYAWA TARE DA WANI MUTUM GUDA BAYAN ANNABI (SAW). KO DA KUWA ABUBAKAR NE, KO UMAR KO USMAN KO ALIYU (RA). SABODA IN YA ZAMA HAKA, DA MUTUMIN YA ZAMA A MATSAYIN ANNABI (SAW), WANDA YA WAJABA A YI MASA BIYAYYA A KAN DUKKAN ABIN DA YAKE FA'DI. ALHALI SANANNE NE SHI ALIYU (RA) SAHIBANSA DA MABIYANSA SUN KASANCE SUNA YI MASA JAYAYYA A MAS'ALOLI MASU YAWA, KUMA BA SA BARIN FAHIMTARSU SU KOMA ZUWA GA MAGANARSA. KAI, AKWAI MAS'ALOLIN DA AN SAMU NASSOSHI DAGA ANNABI (SAW) WA'DANDA SUKE GOYON BAYAN FAHIMTAR WA'DANDA SUKA SA'BA MASAN. KAMAR MAS'ALAR MATAR DA MIJINTA YA MUTU TANA DA CIKI. LALLAI SHI ALIYU (RA) YA YI FATAWAN TA YI IDDA DA MAFI NISAN AJALI GUDA 2. AMMA UMAR DA IBNU MAS'UD DA WASUNSU SUN YI FATAWA NE DA YIN IDDA ZUWA HAIFE CIKIN NATA. KUMA WANNAN SHI NE ABIN DA HADISIN ANNABI (SAW) YA TABBATAR. AN TAMBAYI ANNABI (SAW) - ABUS SANABIL YA KASANCE YANA FATAWA DA IRIN FAHIMTAR ALIYU (RA) - SAI ANNABI (SAW) YA CE:
((كذب أبو السنابل قد حللت فانكحي))
ABUS SANABIL YA YI K'ARYA, (KUSKURE), LALLAI KIN FITA DAGA TAKABA, KI YI AURE.
YA FA'DI WANNAN NE WA SUBAI'ATUL ASLAMIYYAH A LOKACIN DA TA TAMBAYE SHI A KAN HAKAN.
AMMA FA'DINSA:
((اللهم انصُر من نصره، واخذل من خذله))
YA ALLAH KA TAIMAKI WANDA YA TAIMAKE SHI, KAR KA TAIMAKI WANDA YA K'I TAIMAKONSA.
WANNAN SA'BANIN ABIN DA YA FARU NE. SABODA ABIN DA YA FARU BA HAKA BA NE. KAI, AKWAI MUTANEN DA SUKA YI YAK'I TARE DA SHI A SIFFIN AMMA BA SU CI NASARA BA. KUMA AKWAI WA'DANDA BA SU YI YAK'I TARE DA SHI BA, AMMA ALLAH BAI K'I TAIMAKONSU BA. KAMAR SA'AD BIN ABI WAK'K'ASW (RA) WANDA SHI YA BU'DE IRAK'I, BAI YI YAK'I TARE DA SHI (ALIYU (RA)) BA. HAKA NAN MUTANEN MU'AWIYA (RA) DA BANI UMAYYA, WA'DANDA SUKA YAK'E SHI, SUN BU'DE GARURUWAN KAFIRAI MASU YAWA, KUMA ALLAH YA TAIMAKESU.
HAKA NAN FA'DINSA:
((والِ من والاه، وعادِ من عاداه))
YA ALLAH KA SO WANDA YA SO SHI, KA K'I WANDA YA K'I SHI.
WANNAN YA SA'BA MA GINSHIK'AN MUSLUNCI. SABODA AL- K'UR'ANI YA YI BAYANIN CEWA; LALLAI MUMINAI DUK DA YAK'I A TSAKANINSU, DA KUMA TAWAYEN (BAGYU) WASU GA WANI SASHE, SU 'YAN UWA NE MUMINAI. KAMAR YADDA ALLAH YA CE:
{ وإن طائفتان من المؤمنين اقتتلوا فأصلحوا بينهما فإن بغت إحداهما على الأخرى فقتلوا التي تبغي حتى تفيء إلى أمر الله فإن فاءت فأصلحوا بينهما بالعدل وأقسطوا إن الله يحبُّ المقسطين. إنما المؤمنون إخوة فأصلحوا بين أخويكم }
IDAN 'BANGARE 2 NA MUMINAI SUKA YAK'I JUNA, TO KU YI SULHU A TSAKANINSU. IN KUMA 'DAYANSU YA YI TAWAYE MA 'DAYAN, TO KU YAK'I WACCE TA YI TAWAYEN HAR SAI TA KOMA GA DOKAR ALLAH. IN YA KOMA, TO KU YI SULHU A TSAKANINSU DA ADALCI. KU YI ADALCI, LALLAI ALLAH YANA SON MASU ADALCI. LALLAI MUMINAI 'YAN UWAN NE, DON HAKA KU YI SULHU A TSAKANIN 'YAN UWANKU 2.
DON HAKA YAYA ZA A YI ANNABI (SAW) YA FA'DI WANNAN MAGANA GA MUTUM 'DAYA DAGA CIKIN AL'UMMARSA, YA CE:
((اللهم وال من والاه وعادِ من عاداه))
YA ALLAH KA SO WANDA YA SO SHI, KA K'I WANDA YA K'I SHI??!!
ALLAH YA BA DA LABARIN CEWA; SHI WALIYYIN (MASOYIN) MUMINAI NE. MUMINAI KUMA MASOYANSA NE. KUMA SASHENSU MASOYA SASHE NE. KUMA SU 'YAN UWAN JUNA NE, KO DA KUWA SUN YAK'I JUNA, SASHE YA YI TAWAYE MA SASHE.
AMMA FA'DINSA:
((من كنت مولاه فعليٌّ مولاه))
DUK WANDA NA ZAMA MASOYINSA, TO ALIYU MASOYINSA NE.
A CIKIN MALAMAN HADISI AKWAI WANDA YA SOKE SHI, KAMAR BUKHARI DA WANINSA. DAGA CIKINSU KUMA AKWAI WANDA YA KYAUTATA SHI, KAMAR AHMAD BIN HANBAL DA TIRMIZIY DA WANINSU.
TO, A LOKACIN DA ANNABI (SAW) YA FA'DI WANNAN, IN YA KASANCE YANA NUFIN SOYAYYA CE WACCE ALIYU (RA) YA KE'BANTA DA ITA, KO KUMA BAI YI NUFI WATA SOYAYYA BA FACE WACCE AKA YI TARAYYA A CIKINTA. WATO ITA CE; SOYAYYAR IMANI WACCE ALLAH YA SANYATA A TSAKANIN MUMINAI?!
DA WANNAN YA BAYYANA CEWA: ALIYU (RA) YANA DAGA CIKIN MUMINAI MASU TAK'AWA WA'DANDA YA WAJABA A SOSU. SA'BANIN ABIN DA NASIBAI SUKE FA'DI, CEWA; BAI CANCANCI SOYAYYA BA. ITA MUWALATI (SOYAYYA) KISHIYAR K'IYAYYA CE. LALLAI BABU SHAKKA WAJIBI NE ASO DUKKAN MUMINAI, ALIYU (RA) KUMA YANA DAGA CIKIN SHUGABAN MUMINAI, KAMAR YADDA YA WAJABA ASO ABUBAKAR DA UMAR DA USMAN, DA SAURAN SAHABBAI, MUHAJIRAI DA ANSAR (RA). BAI HALATTA A YI GABA DA 'DAYA DAGA CIKIN WA'DANNAN BA. KUMA DUK WANDA BAI SOSU BA, LALLAI YA SA'BA MA ALLAH DA MANZONSA. KUMA IMANINSA YA RAGU GWARGWADON ABIN DA YA BARI NA SOYAYYAR DA TA WAJABA A KANSA. ALLAH YA CE:
{ إنما وليكم الله ورسوله والذين ءامنوا الذين يقيمون الصلاة ويؤتون الزكوة وهم راكعون . ومن يتولَّ الله ورسوله والذين ءامنوا فإن حزب الله هم الغالبون }
LALLAI MASOYINKU SHI NE ALLAH DA MANZONSA, DA WA'DANDA SUKA YI IMANI SUKE TSAI DA SALLAH, SUKE BA DA ZAKKAH, KUMA SUNA YIN RUKU'I. DUK WANDA YA SO ALLAH DA MANZONSA DA WA'DANDA SUKA YI IMANI, TO LALLAI K'UNGIYAR ALLAH SU NE MASU YIN GALBA.
WANNAR AYAR TANA WAJABTA SOYAYYA GA DUKKAN MUMINAI.
AMMA HADISIN YIN SADAKA DA ZOBE A CIKIN SALLAH K'ARYA NE, K'IRK'IRARRE NE BISA ITTIFAK'IN MASANA. WANNAN KUWA AN YI BAYANINSA TA FISKOKI MASU YAWA A FA'DA'DE A WANI WAJEN DABAN.
KU BIYOMU AKWAI CIGABA...
ALLAH YA SA MU DACE.
No comments:
Post a Comment