BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
AN TAMBAYI SHAIKHUL ISLAM IBNU TAIMIYYA (R) GAME DA WANI SHARIFI MAI RIK'O DA SUNNA, SAI DAI WANI LOKACI YANA SAMUN SHAKKA A WAJEN FIFITA ABUBAKAR DA UMAR DA USMAN A AKAN ALIYU (RA), SAI YA YI ZATON ALIYU (RA) YA FISU FALALA. HAR YAKE KAFA HUJJA DA FA'DIN ANNABI (SAW):
((أنت مني وأنا منك))
KAI DAGA GARENI KAKE, NI MA DAGA GAREKA NAKE.
DA KUMA FA'DINSA:
((أنت مني بمنزلة هارون من موسى))
MATSAYINKA A WAJENA KAMAR MATSAYIN HARUNA NE A WAJEN MUSA.
SABODA HARUNA YANA DA MATSAYI MA'DAUKAKI A WAJEN ANNABI MUSA (AS), BA SHI DA WANI MAFI GIRMA FIYE DA SHI.
DA FA'DINSA (SAW) A RANAR KHAIBARA:
((لأعطين الراية غداً رجلاً يحب الله ورسوله، ويُحِبُّه الله ورسوله يفتح الله على يده))
GOBE ZAN BA DA TUTA MA WANI MUTUMIN DA YAKE SON ALLAH DA MANZONSA, KUMA ALLAH DA MANZONSA SUKE SONSA, ALLAH ZAI BA DA NASARA A HANUNSA.
SAI YA BAYAR DA ITA MA ALIYU (RA).
DA FA'DINSA (SAW):
((من كنت مولاه فعليٌّ مولاه، اللهم والِ من والاه، وعادِ من عاداه، وأدر الحق معه كيفما دار)).
DUK WANDA NA ZAMA MASOYINSA, TO ALIYU MASOYINSA NE. YA ALLAH KA SO WANDA YA SO SHI, KA K'I WANDA YA K'I SHI, KUMA KA KEWAYA GASKIYA TARE DA SHI DUK INDA TA ZAGAYA.
DA KUMA FA'DINSA (SAW) A RANAR GADEER KHUM:
((أُذكركم الله في أهل بيتي))
INA TUNA MUKU ALLAH GAME DA IYALAN GIDANA.
DA KUMA FA'DIN ALLAH (T):
{ فقل تعالوا ندع أبناءنا وأبناءكم }
KA CE: KU ZO ZAMU KIRA 'YA'YANMU DA 'YA'YANKU...
DA FA'DINSA (T):
{ هذان خصمان اختصموا في ربهم }
WA'DANNAN MASU HUSUMA GUDA 2 NE, WA'DANDA SUKA YI HUSUMA GAME DA UBANGIJINSU.
DA FA'DINSA:
{ هل أتى على الإنسان حينٌ من الدهر لم يكن شيئاً مذكورا }
YANA GANIN CEWA; SURAR TA SAUK'A NE A GAME DA ALIYU (RA).
DON HAKA, KU BA MU FATAWA, ALLAH SHI GAFARTA WA MALAM:
SAI IBNU TAIMIYYA (R) YA CE:
YABO DA GODIYA YA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN HALITTU.
DA FARKO, YA WAJABA MU SANI; LALLAI FIFITA WANI A KAN WANI YANA KASANCEWA NE IDAN WASU KE'BANTATTUN FALALOLI SUN TABBATA GA MAFIFICIN, WA'DANDA BABU SU A WAJEN WANDA AKA FIN. AMMA IDAN SUN DAIDAITA A ABUBUWAN DA SUKE SA A SAMU FIFIKON, SAI 'DAYA DAGA CIKINSU YA KE'BANTA DA WASU ABUBUWAN DA 'DAYAN BAI YI TARAYYA DA SHI A CIKINSU BA, TO WANCAN YA FI WANNAN FALALA. AMMA ABIN DA MUTUM YA KASANCE YA YI TARAYYA DA WANINSA A CIKINSA, NA ABABEN YABO, WA'DANNAN SU AKE KIRA DA ''MANAK'IB''; ABIN YABO DA FALALA DA ABIN KIRKI. SAI DAI BA SU WAJABTA FIFITA MUTUM A KAN WANIN NASA. IN KUMA SUN ZAMA AN YI TARAYYA A CIKINSU, TO BA KI'BANTACCEN MATSAYI (KHASWA'IS) BA NE.
IN WANNAN HAKA NE, TO FALALOLIN ABUBAKAR AL- SIDDEEQ (RA) WA'DANDA YA KE'BANTA DA SU, KE'BANTACCEN MATSAYI NE WANDA BABU WANDA YA YI TARAYYA DA SHI A CIKINSA. AMMA FALALOLIN ALIYU (RA) YA YI TARAYYA DA WANINSA DAGA CIKIN MUTANE A CIKINSU. SABODA FA'DIN ANNABI (SAW):
((لو كنت متخذاً من أهل الأرض خليلاً لاتخذت أبا بكر خليلا، لا تبقين في المسجد خوخة إلا سدت إلا خوخة أبي بكر، إن أمنّ الناس عليَّ في صحبته لي وذات يده أبو بكر))
DA ZAN RIK'I WANI A MATSAYIN BADA'DE (CIKAKKEN MASOYIN DA BA SHI DA ABOKIN TARAYYA) DAGA MUTANEN DUNIYA DA NA RIK'I ABUBAKAR A MATSAYIN BADA'DENA. KAR A BAR WATA K'OFA TA SAURA A MASALLACI FACE AN RUFETA, SAI DAI K'OFAR ABUBAKAR. LALLAI MAI FALALA A KAINA DAGA CIKIN MUTANE A ABOKANTAKARSA DA NI DA KUMA ABIN HANUNSA (DUKIYARSA) SHI NE ABUBAKAR.
BUKHARI DA MUSLIM NE SUKA RUWAITO SHI, DAGA HADISIN ABU SAEED AL- KHUDRIY (RA).
K'ISSAR RIK'ONSA BADA'DE YANA CIKIN SAHIHUL BUKHARI TA FISKOKI MASU YAWA.
A CIKIN WANNAN HADISIN AKWAI KE'BANTATTUN ABUBUWA (KHASWA'IS) GUDA 3 NA ABUBAKAR (RA) WA'DANDA BABU WANDA YA YI TARAYYA DA SHI A CIKINSU:
(1) FA'DINSA (SAW):
((إن أمنّ الناس علينا في صُحبته وذات يده أبو بكر))
A CIKINSA YA BAYYANA CEWA; BABU WANI DAGA CIKIN SAHABBAI DA YAKE DA WANI HAK'K'I A KANSA A ABOKANTAKARSA DA SHI DA KUMA DUKIYARSA KAMAR ABUBAKAR (RA).
(2) NA BIYU; FA'DINSA (SAW):
((لا تبقين في المسجد خوخة إلا سدت إلا خوخة أبي بكر))
KAR A BAR WATA K'OFA TA SAURA A MASALLACI FACE AN RUFETA, SAI DAI K'OFAR ABUBAKAR.
A WANNAN AKWAI KE'BANCE ABUBAKAR (RA) SHI KA'DAI BAN DA SAURAN SAHABBAI.
WANI DAGA CIKIN MAK'ARYATA YA SO YA RUWAITO IRIN WANNAN HADISI WA ALIYU (RA), SAI DAI TABBATACCEN INGANTACCEN HADISI BA A YI MASA KARO DA HADISIN K'ARYA MAI RAUNI.
(3) NA UKU; FA'DINSA:
((لو كنت متخذا من أهل الأرض خليلا لاتخذت أبا بكر خليلا))
WANNAN NASSI NE A KAN CEWA; BABU WANI DA YA CANCANCI ZAMA BADA'DE (CIKAKKEN MASOYI) DAGA CIKIN MUTANE. DA KUWA ZAI KASANCE A CIKIN MUTANE DA ABUBAKAR (RA) NE. DA AKWAI WANI WANDA YA FI SHI FALALA DA SHI YA FI CANCANTAR ZAMA BADA'DEN ANNABI (SAW) DA ACE; HAKAN ZAI FARU.
HAKA NAN UMURNIN ANNABI (SAW) GA ABUBAKAR (RA) DA YA YI WA MUTANE SALLAH, A LOKACIN RASHIN LAFIYANSA YANA DAGA CIKIN KE'BANTATTUN FALALOLINSA (KHASWA'IS), WANDA BABU WANDA YA YI TARAYYA DA SHI A CIKINSA. ANNABI (SAW) BAI TA'BA UMURTAN AL'UMMARSA DA SU YI SALLAH A BAYAN WANI BA, A CIKIN RAYUWARSA ALHALI YANA GARI (BAI YI TAFIYA BA) SAI A BAYAN ABUBAKAR (RA).
HAKA NAN NA'DA ABUBAKAR (RA) A MATSAYIN AMIRUL HAJJI TUN DAGA MADINA, DON YA TSAYAR DA SUNNA, YA KUMA SHAFE TSARIN JAHILIYYA. LALLAI WANNAN YANA DAGA CIKIN KE'BANTATTUN FALALOLINSA.
HAKA NAN FA'DINSA (SAW) A CIKIN HADISI INGANTACCE:
((أُدع لي أباك أو أخاك حتى أكتب لأبي بكر كتابا لا يختلف عليه الناس من بعدي))
KI KIRA MINI BABANKI (YA FA'DI MA A'ISHA (RA) DA 'DAN UWANKI DON IN RUBUTA MA ABUBAKAR TAKARDA, DON KAR MUTANE SU SA'BA MASA A BAYANA.
SAI ANNABI (SAW) YA CE:
((يأبى الله والمؤمنون إلا أبا بكر))
ALLAH DA MUMINAI ZA SU K'I KOWA SAI ABUBAKAR.
MAKAMANTAN WA'DANNAN HADISAN SUNA DA YAWA, SUNA BAYYANA CEWA; BABU WANI DAGA CIKIN SAHABBAI DA YAKE DADAI DA ABUBAKAR (RA).
JAWABI A KAN FALALOLIN ALIYU (RA) WA'DANDA WASU SUKA RIK'E DON FIFITA SHI A KAN KHALIFOFI GUDA 3; ABUBAKAR, UMAR, USMAN (RA):
AMMA FA'DIN ANNABI (SAW):
((أنت مني وأنا منك))
KAI DAGA GARENI KAKE, NI MA DAGA GAREKA NAKE.
WANNAR MAGANA ANNABI (SAW) YA FA'DETA GA WANIN ALIYU (RA) DAGA CIKIN MUMINAI. KAMAR YADDA YA FA'DI MA JULAIBIB (RA), WANDA YA KASHE DA YAWA DAGA KAFIRAI:
((هذا مني وأنا منه))
WANNNAN DAGA GARENI YAKE, NI MA DAGA GARE SHI NAKE.
YA ZO A CIKIN BUKHARI DA MUSLIM:
(إن الأشعريين إذا كانوا في السفر ونقصت نفقة عيالهم بالمدينة جمعوا ما كان معهم في ثوب واحد ثم قسموه بينهم بالسويّة؛ هم مني وأنا منهم))
''LALLAI ASH'ARIYYAWA SUN KASANCE IN SUN YI TAFIYA, SAI ABINCI IYALANSU YA YI K'ARANCI A MADINA, SUKAN TARA ABIN DA KE TARE DA SU NA ABINCI A TUFAFI GUDA 'DAYA, SAI SU RABA SHI A TSAKANINSU DADAI - DA - DADAI. SU DAGA GARENI SUKE, NI MA DAGA GARESU NAKE''.
SAI ANNABI (SAW) YA SANYA ASH'ARIYYAWA; ABU MUSA, DA ABU AMIR DA WASUNSU DAGA GARE SHI, SHI MA DAGA GARESU. KAMAR YADDA YA GAYA MA ALIYU (RA):
((أنت مني وأنا منك))
KAI DAGA GARENI KAKE, NI MA DAGA GAREKA NAKE.
KUMA ALLAH YA CE:
{ والذين ءامنوا من بعدُ وهاجروا وجهدوا معكم فأولئك منكم }
WA'DANDA SUKA YI IMANI DAGA BAYA, SUKA YI HIJIRA, KUMA SUKA YI JIHADI TARE DA KU WA'DANNAN SUNA DAGA GAREKU.
KUMA ALLAH YA CE:
{ ألم تَرَ إلى الذين تولَّوا قوماً غضب اللهُ عليهم ما هم منكم ولا منهم }
SHIN BA KA GA WA'DANDA SUKA YI SOYAYYA WA MUTANEN DA ALLAH YA YI MUSU FUSHI BA NE, SU BA SA DAGA GAREKU KUMA BA SA DAGA GARESU...
KUMA ALLAH YA CE:
{ ويحلِفون بالله إنَّهم لمنكم وما هم منكم }
KUMA SUNA RANTSUWA DA ALLAH A KAN LALLAI SUNA DAGA GARE KU, ALHALI BA SA DAGA GAREKU..
DA FA'DINSA (SAW):
((من غشنا فليس منا، ومن حمل علينا السلاح فليس منا))
DUK WANDA YA YI MANA ALGUS BA YA DAGA GAREMU, HAKA DUK WANDA YA 'DAUKI MAKAMI A KANMU BA YA DAGA GAREMU.
DA MAKAMANTA WA'DANNAN.
WANNAN YANA NUNA DUK WANDA YA KU'BUTA DAGA WA'DANNAN KABA'IRAI ZAI KASANCE DAGA GAREMU.
IRIN WANNAR MAGANA ANA FA'DINTA NE GA ABIN DA SUKE NAU'I 'DAYA, SAI A CE: WANNAN DAGA WANNAN YAKE, IDAN A NAU'INSA YAKE. DON HAKA DUK WANDA YA KASANCE DAGA CIKIN MUMINAI MASU CIKAKKEN IMANI, TO YANA DAGA ANNABI (SAW), ANNABI MA YANA DAGA GARE SHI.
DA FA'DIN ANNABI (SAW) A K'ISSAR 'YAR HAMZA:
((أنت مني وأنا منك))
KE DAGA GARENI KIKE, NI DAGA GAREKI NAKE.
KAMAR FA'DINSA GA ZAIDU 'DAN HARITHA (RA):
((أنت أخونا ومولانا))
KAI 'DAN UWANMU NE, KUMA MAULANMU.
SANANNE NE CEWA; WANNAN BAI KE'BANTA DA ZAIDU BA, KAI, DUKKAN WANDA YA KASANCE A CIKIN MAULOLINSA, ZAI FA'DA MASA IRIN WANNAR MAGANA, SABODA FA'DIN ALLAH (T):
{ فإن لم تَعلموا ءاباءهم فإخوانكم في الدين ومواليكم }
IDAN BA KU SAN IYAYENSU BA, TO 'YAN UWANKU NE A CIKIN ADDINI, KUMA MAULOLINKU NE.
TO KAMAR HAKA FA'DINSA GA ALIYU (RA) YAKE:
((أنت مني وأنا منك))
KAI DAGA GARENI KAKE, NI MA DAGA GAREKA NAKE.
WANNAN BA YA DAGA CIKIN ABUBUWAN DA YA KE'BANTA DA SU. KAI, DUK WANDA YA DACE DA ANNABI (SAW) A CIKAN IMANI, YA KASANCE DAGA ANNABI (SAW), ANNABI KUMA DAGA GARE SHI.
AKWAI CIGABA, SAI A BIYO MU A HANKALI.
ALLAH YA SA MU DACE!!
No comments:
Post a Comment