Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Wednesday, 14 December 2011

SAK'O ZUWA GA MASU KORE 'DAUKAKAR ALLAH A KAN AL'ARSHINSA BISA DOGARONSU A KAN HUJJAR HANKALI

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.



LALLAI DUK MAI LAFIYAYYEN HANKALI YA SAN AKWAI TARIN DALILAI NA HANKALI DA SUKE TABBATAR DA SIFFOFIN ALLAH (SWT).
SABODA HANKALI YANA NUNI ZUWA GA CEWA; DUKKAN WATA SIFA DA ALLAH YA SIFFANTA KANSA DA ITA A CIKIN ALK'UR'ANI, KO ANNABI (SAW) YA SIFFANTA SHI DA ITA A CIKIN HADISI, TO SIFA CE TA CIKA DA KAMALA. HANKALI KUMA YANA TABBATAR DA SIFFOFIN KAMALA MA ALLAH (SWT). DON HAKA A HANKALCE BA ZAI TA'BA YIWUWA BA YA ZAMA ALLAH YA SIFFANTA KANSA, KO MANZONSA YA SIFANTA SHI DA SIFAR DA ZA TA NUNA AIBI DA NAK'ASA A GARE SHI.
DON HAKA DUK WATA SIFA DA ALLAH YA SIFANTA KANSA DA ITA A CIKIN ALK'UR'ANI, KO A HADISIN ANNABI (SAW) SIFA CE TA KAMALA MA ALLAH (SAW), BABU TAWAYA A CIKINTA TA KOWACE FISKA. DON HAKA A HANKALCE TABBATACCIYA CE GA ALLAH (SWT). MISALI; SIFAR FISKA, HANAYE 2, K'AFA DA KUMA 'DAUKAKARSA A SAMAN AL'ARSHI, DA SAURAN SIFOFIN DA SUKA ZO A CIKIN ALK'UR'ANI DA HADISI.
ALLAH YA SIFFANTA KANSA DA SIFOFIN ZATINSA, TA HANYAR AMBATONSU DA TABBATAR DA SIFFANTUWANSA DA SU, A CIKIN LITTAFINSA ALK'UR'ANI MAI GIRMA, KO TA HARSHEN MANZONSA (SAW), A CIKIN INGANTATTUN HADISANSA.
LALLAI KAMAR YADDA MUKA GABATAR A BAYA, DUKKAN SIFFAR DA ALLAH YA SIFANTA KANSA DA SHI, SIFA CE TA KAMALA, WACCE TA WAJABA MA ALLAH, SABODA ALLAH BA ZAI SIFFANTA KANSA DA TAWAYA DA NAK'ASA BA. DON HAKA YA WAJABA A KAN BAYI SU YI IMANI SU TABBATAR DA SIFFOFIN DA ALLAH YA SIFFANTA KANSA DA SU.
ALLAH YA SIFFANTA KANSA DA SIFFOFI NA ZATINSA, DAGA CIKINSU AKWAI:
(1) 'DAUKAKAR ZATINSA A SAMAN AL'ARSHI.
(2) RAI.
(3) FISKA.
(4) IDANU GUDA BIYU.
(5) HANNAYE GUDA BIYU.
(6) YATSU.
(7) SAWU.
(8) K'AFA.
DUKA WA'DANNAN SIFOFI, ALLAH NE YA BA DA LABARINSU YANA MAI SIFFANTA KANSA DA SU A CIKIN ALK'UR'ANI, KO A HADISAN ANNABI (SAW). BABU WATA HANYA TA SANIN WA'DANNAN SIFOFI NA ALLAH, SAI TA HANYAR LABARIN DA ALLAH YA BAYAR WA BAYINSA, TA HANYAR WAHAYI DAGA GARE SHI.
SABODA DUKKAN ABUBUWA SUN KASU KASHI BIYU:
(1) ABIN DA YAKE CIKIN TUNANI, BABU SHI A FILI.
(2) ABIN DA YAKE AKWAI SHI A SARARI. WANDA ZA A IYA RISKANSA TA HANYOYI GUDA 5, HANYOYIN SANIN ABU: JI, GANI, SHANSHANAWA, 'DAN'DANAWA, DA TA'BAWA.
DUK ABIN DA BA ZA A IYA RISKANSA TA WA'DANNAN HANYOYI GUDA 5 BA, TO BABU WANNAN ABU. SHI YA SA MALA'IKU DA WASU DAGA CIKIN ANNABAWA SUKA JI MAGANAR ALLAH, KUMA SHI YA SA A LAHIRA MUMINAI DA IDONSU ZA SU GA ALLAH (T).
SU WA'DANNAN ABUBUWA DA SUKE AKWAISU ASARARI, SUN KASU KASHI BIYU:
(1) ABIN DA YAKE BAYYANE NE, ZA MU IYA ISA GARE SHI.
(2) ABIN DA YA 'BUYA GAREMU. BA ZA MU IYA ISA GARE SHI BA. (GAIBI).
ALLAH (SAW) KUWA, SHI NE GAIBI MAFI GIRMA.
TO, ZA A IYA SANIN SIFOFIN ALLAH NE TA HANYOYI GUDA 3 KAWAI BABU NA 4:
(1) IMMA TA HANYAR GANINSA. TO, BABU WANDA YA TA'BA GANINSA A NAN DUNIYA.
(2) KO KUMA TA HANYAR GANIN MAKAMANCINSA (IRINSA). TO, SHI ALLAH BABU WANI ABU DA YAKE KAMA DA SHI.
(3) KO KUMA SHI ALLAH 'DIN YA BA MU LABARI GAME DA KANSA.
LALLAI IN MUN DUBA WA'DANNAN HANYOYI GUDA 3, ZA MU GA BA MU DA WATA HANYA, SAI HANYAR LABARI DAGA ALLAH (T). WATO TA HANYAR WAHAYI. (ALK'UR'ANI DA HADISAN ANNABI (SAW).

DON HAKA, MU DA MUKE TABBATAR MA ALLAH SIFOFIN ZATINSA WA'DANDA YA TABBATAR MA KANSA, IN AN TAMBAYEMU; TA WACE HANYA MUKA SAN ALLAH YA SIFFANTU DA WA'DANNAN SIFOFI NA ZATIN NASA??
SAI MU CE: MUN SAN ALLAH YA SIFFANTU DA SU NE TA HANYAR LABARIN DA YA ZO MANA DAGA GARE SHI.

MU KUMA SAI MU TAMBAYI MASU KORE MASA WA'DANNAN SIFOFI; TA WACE HANYA KUKA SAN CEWA; WA'DANNAN SIFOFI SUN KORU GA ALLAH??
SHIN KUN TA'BA GANIN ALLAHN NE, SAI KUKA SAN BA SHI DA WA'DANNAN SIFOFIN??
KO KUMA KUN TA'BA GANIN WANI MAI KAMA DA SHI NE, SAI KUKA SAN CEWA; BA SHI DA SU??

TO, MU DA SU DUKA MUN YI ITTIFAK'I A KAN BA SU DA 'DAYA DAGA CIKIN HANYOYI GUDA BIYUN NAN!!
SAURA HANYA TA UKU KAWAI!!
TO SAI MU CE: MUNA BUK'ATAR KU KAWO MANA INDA KUKA SAMU LABARIN CEWA; WA'DANNAN SIFOFI SUN KORU GA ALLAH (STW)!!!!!!!

LALLAI ALLAH (SAW) YA SIFFANTA KANSA DA SIFFOFI NA ZATINSA A CIKIN AYOYI MASU YAWA NA ALK'UR'ANI. DAGA CIKINSU AKWAI:
(1) 'DAUKAKAR ZATINSA A SAMAN AL'ARSHI.
(2) RAI.
(3) FISKA.
(4) IDANU GUDA BIYU.
(5) HANNAYE GUDA BIYU.
(6) YATSU.
(7) K'WABRI.
(8) K'AFA.
DA SAURANSU.
SA'ANNAN LALLAI ALLAH (SWT) YA SIFFANTA KANSA DA CEWA; YA YI BAYANIN LAMURAN ADDINI WA BAYINSA MATUK'AR BAYANI. KUMA YA UMURCI MANZONSA DA YIN BAYANI. KUMA YA BA DA LABARIN CEWA; YA SAUK'AR DA LITTAFINSA NE DON YA YI BAYANI WA MUTANE. TO SHI WANNAN BAYANI DA ALLAH YA 'DAUKI NAUYIN YINSA WA BAYINSA, KUMA HAR YA UMURCI MANZONSA (SAW) DA SHI, IMMA YA KASANCE, ABIN DA AKE NUFI DA WANNAN BAYANI SHI NE; BAYANIN LAFAZIN AYOYIN ALK'UR'ANI NE KAWAI BAN DA MA'ANARSA. KO KUMA YA ZAMA BAYANIN MA'ANONIN NE KAWAI BAN DA LAFAZIN AYOYIN (KARANTA HARUFANSA). KO KUMA BAYANI NE NA LAFAZIN AYOYIN TARE DA BAYANIN MA'ANONIN DA SUKA K'UNSA.
A HANKALCE BAI HALATTA A CE; BAYANIN LAFAZIN AYOYIN KAWAI AKE NUFI BA. DOMIN WANNAN BA SHI DA FA'IDA GAME DA MANUFAR MANZANCI. DOMIN BA ZA A SAMU CIMMA MANUFAR AIKO MANZON BA (SAW).
IN KUMA AKA CE; BAYANIN MA'ANA AKE NUFI KAWAI BAN DA LAFAZIN AYOYIN, LALLAI A HANKALCE BA ZAI YIWU BA, SABODA LAFAZI SHI NE YAKE NUNI ZUWA GA MA'ANA, DON HAKA MA'ANA BA ZA TA SAMU BA, BA TARE DA LAFAZIN BA.
SABODA HAKA KAI TSAYE SAI MUKA TABBATAR DA CEWA; BAYANIN DA ALLAH YAKE NUFI NA LAFAZIN AYOYIN ALK'UR'ANI NE TARE DA MA'ANONINSU GABA 'DAYA.
DON HAKA ALLAH YA SAUK'AR DA LITTAFINSA, LAFAZINSA DA MA'ANARSA, KUMA YA AIKO MANZONSA DA BAYANIN LAFAZIN TARE DA MA'ANAR. DON HAKA MUN TABBATAR DA CEWA; MANZON ALLAH (SAW) YA ISAR DA BAYANIN MA'ANONIN AYOYIN SIFFOFIN ALLAH KAMAR YADDA YA ISAR DA LAFAZINSU. KAI, KULAWARSA DA BAYANIN MA'ANAR MA YA FI KULAWARSA DA BAYANIN LAFAZIN, SABODA MA'ANAR ITA CE MAK'SUDI, WATO MAFI MUHIMMANCI.
DON HAKA IN ZAI YIWU ACE; ANNABI (SAW) BAI ISAR DA SASHE NA MA'ANONIN AYOYIN ALK'UR'ANI BA, TO ZAI YIWU KENAN A CE; BAI ISAR DA WANI SASHE NA LAFAZIN ALK'UR'NIN BA. WANNAN KUWA SUKA NE GA MANZANCI ANNABI (SAW).
IN KUMA AKA CE; AI AYOYIN BA ZAHIRINSU AKE NUFI BA, WATO SA'BANIN HAK'IK'ANINSU SUKE, YA ZAMA ANNABI (SAW) BAI YI BAYANI WA AL'UMMARSA BA KENAN, WATO YA 'BOYE SASHE NA SAK'ON DA AKA AIKO SHI BA SHI, TO WANNAN SUKA NE GA MANZANCIN ANNABI (SAW), DA KUMA ISMARSA. KUMA BU'DE K'OFA NE GA ZINDIK'AI MASU SUKAN ADDININ MUSLUNCI, KUMA YANA KORE IMANI DA MANZON ALLAH (SAW) DA KUMA MANZANCINSA.
DON HAKA, AYOYIN SIFFOFIN ALLAH (SWT), KAMAR YADDA ANNABI (SAW) YA ISAR DA LAFUZANSU, HAKA YA ISAR DA MA'ANONINSU WA AL'UMMARSA. BA SA BUK'ATAR WANI TAWILIN MASU TAWILI.
ALLAH YA SA MU DACE.

No comments:

Post a Comment