(18) NASIRU YA CE:
(4) WANNAN SHINE ABINDA IBN TAIMIYYA YAKE FADA ACIKIN MINHAJU DINSA (4/42) CEWA IMAM HUSAIN BAI FITABA YANA MAI NUFIN YAKI BA, ….
AMMAR:
AI DA MA ABIN DA AKA CE YA YI SHI NE TAWAYE (KHURUJI) MA SHUGABA MAI RINJAYE.
(19) NASIRU YA CE:
(5) KAI KUMA DAGA INA KASAMO CEWA "SAYYIDINA HUSAINI (RA) YA YI TAWAYE GA SHUGABA YAZIDU 'DAN MU'AWIYA.
AMMAR:
SABODA BAI YI BAI'A WA YAZIDU BA, HAR YA FITA KUFA DON SHI AYI MASA BAI'A.
(20) NASIRU YA CE:
(6) DAGA INANE KASAMO CEWA IMAM HUSAI YA AIKATA KUSKURE.
AMMAR:
AI NI NE NA YI MUKU WANNAR TAMBAYAR, DON HAKA A WAJENKA AKE NEMAN AMSAR. IN BA KA GANE MAGANAR BA NE, TO KOMA KA SAKE KARANTAWA.
(21) NASIRU YA CE:
(7) DAGA INANE KAGANO CEWA IMAM HUSAI YAFITANE SABODA YAYAKI YAZIDU?
AMMAR:
A INA NA FA'DI WANNAR MAGANAR??
(22) NASIRU YA CE:
(8) DAGA INANE KASAMO CEWA KO IMAM HASAN KO IMAN HUSAIN DOLE DAYA DAGA CIKINSU YAKAUCEMA HANYA?
AMMAR:
SABODA MATSAYINSU 'DAYA NE, AMMA KUMA SUKA AIKATA AIYUKA KISHIYOYIN JUNA. DON HAKA – A BISA K'A'IDOJIN SHI'A - IN 'DAYA YA YI DADAI, TO 'DAYA YA YI KUSKURE. IN HASAN (RA) NE YA YI DADAI DON YA BAR IMAMA TA FARILLA TO HUSAINI (RA) YA YI KUSKURE, SABODA YA K'I AIKATA IRIN NA HASAN. IN KUMA HUSAINI (RA) NE YA YI DADAI SABODA YA K'I BARIN IMAMA TA FARILLA TO HASAN (RA) YA YI KUSKURE, DON SHI YA BARI.
(23) NASIRU YA CE:
(24) (9) ANAN WAJEN AMMAR YANA RUSA MANA KHALIFANCIN UMAR DANA USMANU SABODA TUSHENSU SHINE ABUBAKAR, ABUBAKARNE YAZABI UMAR SHIKUMA UMAR YAKAFA KWAMITI NA MUTUM SHIDA YACE DUK WANDA AKA ZABA ACIKINSU DAI-DAINE SAI AKA ZABI USMANU.
AMMAR:
INA DALILI??!
*** HAUSAWA SUKA CE; WANI IN YA YI RAWA AKA BA SHI KU'DI, TO WANI KUMA IN YA YI DUKA ZAI SHA!!
ستدفع الثمن غاليا!!
*** SHAWARA:
INA BA DA SHAWARA WA MALAM NASIRU AMINU YA TSAYA A WAJE 'DAYA, A KAN MAUDHU'IN TATTAUNAWA, BAN DA TSILLA – TSILLA. DON MU ISA ZUWA GA NATIJA MAI FA'IDA, MU DA MASU BIBIYARMU. AMMA BAI KAMATA KA CIGABA DA FA'DADAWA A KAN MAGANAR K'ADDARA BA, KUMA BAI KAMATA KA SHIGO DA MAGANAR KHALIFANCIN ABUBAKAR (RA) BA, SABODA BA A KAI MUKE TATTAUNAWA BA. LALLAI YANA DA KYAU MUTUM YA ZAMA MAI TSARI A TATTAUNAWARSA, SAI YA FA'IDANTAR DA YAWA, BA MAI TSILLA – TSILLA BA, MAI 'BATA WA MUTANE LOKACI.
ALLAH YA SA MU DACE.
No comments:
Post a Comment