Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Thursday, 25 February 2016

YAYE SHUBUHOHI A KAN SULHUN HASSAN (RA) (7)

@GALADIMA NASIRU...

(1) NASIRU YA CE:
GASHI KUMA ALLAH UBANGIJI YANA CEWA ACIKIN LITTAFINSA MAI TSARKI BAI YARDARWA BAYINSA DASUYI KAFIRCI BA :
إِن تَكْفُرُوا فَإِنَّ اللَّهَ غَنِيٌّ عَنكُمْ وَلا يَرْضَى لِعِبَادِهِ الْكُفْرَ
SANNAN KUMA GASHI AMMAR YACE AYYUKAN DA'A DANA SABO DUKA ALLAH NE YAKE KADDARAWA WATO KAMAR SHAN GIYA, SATA, ZINA, DA DAI SAURANSU. ALHALI KUWA SHIMA ALLAH UBANGIJI YAFADA MANA CEWA BAYAYIN UMARNI DA AIKATA ALFASHA :
قُلْ إِنَّ اللَّهَ لاَ يَأْمُرُ بِالْفَحْشَاء

AMMAR:
LALLAI ALLAH BAI YARDA AYI KAFIRCI BA, DUK DA CEWA; SHI YA HALICCI AIKIN KAFIRCIN.
ALLAH YA CE:
والله خلقكم وما تعملون

ALLAH NE YA HALICCEKU DA ABIN DA KUKE AIKATAWA (DUKKAN AIYUKAN BAYI NA ALHERI DA NA SHARRI).
DON HAKA KAMAR YADDA ALLAH YA HALICCI GUMAGUMAN KAFIRCI; SHE'DAN, FIR'AUNA, SAURAN KAFIRAI TO HAKA MA KAFIRCIN ALLAH NE YA HALICCE SHI.
HAKA AIYUKAN ALFASHA MA DUKA ALLAH NE YA HALICCE SU, DOMIN AIYUKAN BAYI NE. GA CAN AYA A KAN HAKA. AMMA ALLAH BAI YI UMURNI DA SU BA.

*** IN AN CE; ALLAH YA HALICCI KAFIRCI DA ALFASHA BA DAIDAI YAKE DA CEWA; YA YARDA DA SU BA, KO KUMA YA YI UMURNI DA SU BA. YARDA DA UMURNI DABAN, HALITTA MA DABAN. KAMAR YADDA ALLAH YA HALICCI SHE'DAN DA KAFIRAI, AMMA KUMA BAI YARDA DA SU BA, YA YI FUSHI DA SU, KUMA YA YI HANI DA BINSU.
ALLAH YA CE:
ولا تتبعوا خطوات الشيطان إنه لكم عدو مبين

*** DON HAKA DUK WANDA BAI YARDA ALLAH NE YA HALICCI AIYUKAN BAYI BA, TO YA FITAR DA WANI ABU DAGA CIKIN HALITTAR ALLAH KENAN, WATO YANA GANIN AKWAI WANI MAHALICCI KOMA BAYAN ALLAH KENAN.
ALHALI ALLAH YA CE:
وخلق كل شيء فقدره تقديرا

KUMA ALLAH SHI YA HALICCI KOMAI, YA KUMA K'ADDARA SHI MATUK'AR K'ADDARAWA.

** DON HAKA KOMAI ALLAH NE YA HALITTA, HAR KAFIRCIN KAFIRI, DA ALFASHAN MAI SA'BO. AMMA KUMA ALLAH BAI YARDA DA SU BA, KUMA BAI YI UMURNI DA SU BA, HASALI MA HANI YA YI A KANSU. YA HALICCE SU, YA YI HANI A KANSU DON YA JARRABI BAYINSA.

(2) NASIRU YA CE:
SANNAN KUMA AMMAR YACE KOMAI NA ALKHAIRI DANA SHARRI DUKANSU DAGA ALLAH NE :
مَّا أَصَابَكَ مِنْ حَسَنَةٍ فَمِنَ اللَّهِ وَمَا أَصَابَكَ مِن سَيِّئَةٍ فَمِن نَّفْسِكَ

AMMAR:
A INA NA FA'DI WANNAR MAGANAR??!

(3) NASIRU YA CE:
DUKA IDAN KATATTARA WADAN NAN MAGAN GANUN WURI GUDA SAIKAGA CEWA AMMAR MUTUM NE DAYAKEYIN TUFKA DA WARWARA ACIKIN MAGANARSA, SABODA GASHI ANAN YANA CEWA: " ALLAH YA K'ADDARA DUKKAN KOMAI DA KOMAI, NA ALHERI DA NA SHARRI DA AIYUKAN BAYI NA 'DA'A DA NA SA'BO DUKA.

AMMAR:
ALLAH NE YA FA'DA BA NI BA. ALLAH YA CE:
وخلق كل شيء فقدره تقديرا

KUMA ALLAH SHI YA HALICCI KOMAI, YA KUMA K'ADDARA SHI MATUK'AR K'ADDARAWA.

*** ALLAH YA CE; KOMAI, BAI WARE WANI ABU BA.
KUMA DU YA CE:
إنا كل شيء خلقناه بقدر

LALLAI MUN HALICCI KOMAI DA K'ADDARA.

*** ALLAH YA CE; KOMAI, BAI WARE WANI ABU BA.

(4) NASIRU YA CE:
AMMA KUMA ACAN BAYA KAI KACE BASHI BANE YAKE CEWA : " SHE'DAN DA MUSHRIKAI NE SUKE KAFA HUJJA DA K'ADDARA. DAMAN HAKA ABIN YAKE BAZAKA TABA DORA KALMAR KAFIRCI AKAN WANDA BATA CAN-CANTA BA FACE SAI KALMAR TAKOMO KANKA.

AMMAR:
ALLAH SARKI, K'ARAMIN SANI ….
AI MAGANAR KAFA HUJJA DA K'ADDARA ITA CE ASALIN MAGANARMU, AMMA SAI KA SHIGA TSILLA – TSILLA, DON KA SAMU MAFAKA. SA'ANNAN KUMA AI NA KAWO MAKA MAGANAR WANI DAGA CIKIN MALAMANKU AL- ALLAMATUL MUHAQQIQ JA'AFAR AL- SUBHANIY. DON HAKA YANZU KAM KAI DA MALAMINKA, SHI NE YA CE; KAFA HUJJA DA K'ADDARA A KAN SA'BO AIKIN JAHILIYYA NE.

*** ABIN DA KAI BA KA SANI BA SHI NE; YIN IMANI DA K'ADDARA WAJIBI NE, AMMA KUMA KAFA HUJJA DA K'ADDARA A KAN SA'BO HARAMUN NE, AIKI NE NA SHE'DAN DA MUSHRIKAI. DON HAKA ANA YIN IMANI DA K'ADDARA NE, AMMA BA A KAFA HUJJA DA SHI A KAN SA'BO. DON HAKA KAFA HUJJA DA QADDARA DA KA YI A KAN BARIN IMAMA TA FARILLA (BARIN FARILLA SA'BO NE), WANNAN AIKI NE NA JAHILIYYA INJI MALAMINKA AL- SUBHANIY.

(5) NASIRU YA CE:
AMSA : TO YANZU MUTUMINDA YAYI IMANI DA IRIN WADAN NAN ZANTUTTUKA NASA TO DON MEYASA ACAN BAYA YAKE CEWA : " SHE'DAN DA MUSHRIKAI NE SUKE KAFA HUJJA DA K'ADDARA."
KUNGA IDAN MUN DUBA WANNAN ZANCE NA AMMAR YANUNA MANA CEWA BABU WATA HIKIMA ACIKIN TURO ANNABAWA DOMIN SUZO SUHANA AIKATA SABO DAKUMA HADA ABOKIN TARAYYA GA ALLAH, SABODA ANAN ZAKAGA IDAN ALLAH BAI GADAMA SABONSA DAKUMA YIMASA SHIRKA DUKA DABAZAI FARUBA, GASHI KUMA DAI ALLAH YANA CEWA :
وَلا يَرْضَى لِعِبَادِهِ الْكُفْرَ

AMMAR:
LALLAI ALLAH SHI NE MAHALICCIN KOWA DA KOMAI, KUMA SHI YA K'ADDARA KOMAI, HAR DA AIYUKAN BAYI. KAMAR YADDA NA KAWO AYOYI A KAN HAKA. AMMA KUMA BA ZA KA KAFA HUJJA DA K'ADDARAN ALLAH A KAN WANI AIKINKA NA SA'BO BA.
MISALI; IN KA YI SATA, BA ZA KA CE; AI ALLAH NE YA K'ADDARA MINI BA. IN KA FA'DI HAKA, SAI MU CE MAKA; EH HAKA NE, ALLAH NE YA K'ADDARA AMMA KUMA YA HANAKA YIN SATA, KUMA YA BA KA IKO DA DAMAR K'IN AIKATA SATAR, AMMA SAI KA BIYE SON ZUCIYARKA KA YI SATA. TO KADA KA ZARGI KOWA SAI KANKA. TUN DA ALLAH YA BA KA K'ARFI DA IKO DA ZA'BI. KANA DA ZA'BIN KAR KA AIKATA, AMMA SAI KA BIYE SON ZUCIYARKA KA AIKATA.

LALLAI K'ADDARA AIYUKAN BAYI BA YA HANA AIKO MANZANNI. SABODA ALLAH YA HALITTA MA BAYI IKO DA GANIN DAMA. IN SUN AIKATA ABU SUN AIKATA NE A BISA ZA'BIN DA IKONSU, HAKA MA IN SUN BARI, AMMA DUKA BISA GANIN DAMA CE TA ALLAH. KAMAR YADDA ALLAH YA CE:
وما تشاؤون إلا أن يشاء الله رب العالمين

DON HAKA MANZANNI SUN ZO NE DON SU YI BAYANIN TAUHIDI DA SHARI'A, BAYAN ALLAH YA K'ADDARA DUKKAN AIYUKAN BAYI, DON YA JARABESU.
ALLAH YA CE:
ولو شاء الله لجعلكم أمة واحدة ولكن ليبلوكم في مآ آتاكم
YA CE:
وهو الذي خلق السماوات والأرض في ستة أيام وكان عرشه على الماء ليبلوكم أيكم أحسن عملا
YA CE:
الذي خلق الموت والحياة ليبلوكم أيكم أحسن عملا

KUMA ALLAH SHI YAKE SHIRYAR DA WANDA YAKE SO, KUMA YAKE 'BATAR DA WANDA YAKE SO. ALLAH YA CE:
ولو شاء الله لجعلكم أمة واحدة ولكن يضل من يشاء ويهدي من يشاء ولتسألن عما كنتم تعملون

No comments:

Post a Comment