(10) NASIRU YA CE:
IDAN GASKIYANE ABINDA KUKE FADA CEWA ANNABI YAYI ISHARORI GA ABUBAKAR YAZAMA KHALIFANSA ABAYANSA, MEYASA ASAKIFA ABUBAKAR YACE AZABI UMAR KO ABU UBAIDAH?
AMMAR:
ABIN DA YA SA SABODA ANNABI (SAW) BAI NASSANTA SUNANSA BA. DON HAKA SHI YA SA. KUMA WURI NE NA ZA'BE, MUTUM BA YA ZA'BAN KANSA, SABODA A CIKIN HAKAN AKWAI "TAZKIYA" MA KAI, ALHALI ALLAH YA CE:
فلا تزكوا أنفسكم هو أعلم بمن اتقى
SAI DAI IN AN NASSANTA SUNAN MUTUM. TO A NAN NE ZAI NUNA KANSA. AMMA SU SAHABBAI DA YAKE SUN SAN CEWA; ANNABI (SAW) YA KASANCE YANA GABATAR DA ABUBAKAR (RA) A KAN KOWA A CIKIN SAHABBAI, AI KA GA DAGA GABATAR DA SHI DA UMAR (RA) YA YI, BABU WANDA YA YI MUSU HAR YAU SAI DA ABDULLAHI 'DAN SABA'I YA BAYYANA TUKUNA.
(11) NASIRU YA CE:
AMSA : KACE SUNNAH KANA NUFIN ASUNNAR ANNABI? IDAN HAKANE KAWO HADISIN MUGANI.
AMMAR:
ANNABI (SAW) NE YA CE:
عن جنادة بن أبي أمية قال دخلنا على عبادة بن الصامت وهو مريض قلنا أصلحك الله حدث بحديث ينفعك الله به سمعته من النبي صلى الله عليه وسلم قال : دعانا النبي صلى الله عليه وسلم فبايعناه.
7056 - فقال فيما أخذ علينا أن بايعنا على السمع والطاعة في منشطنا ومكرهنا وعسرنا ويسرنا وأثرة علينا ، وأن لا ننازع الأمر أهله إلا أن تروا كفرا بواحا عندكم من الله فيه برهان
MUSLIM
عن نافع عن ابن عمر عن النبى -صلى الله عليه وسلم- أنه قال « على المرء المسلم السمع والطاعة فيما أحب وكره إلا أن يؤمر بمعصية فإن أمر بمعصية فلا سمع ولا طاعة ».
MUSLIM
عن أبى هريرة قال قال رسول الله -صلى الله عليه وسلم- « عليك السمع والطاعة فى عسرك ويسرك ومنشطك ومكرهك وأثرة عليك ».
MUSLIM
عن يحيى بن حصين عن جدته أم الحصين قال سمعتها تقول حججت مع رسول الله -صلى الله عليه وسلم- حجة الوداع - قالت - فقال رسول الله -صلى الله عليه وسلم- قولا كثيرا ثم سمعته يقول « إن أمر عليكم عبد مجدع - حسبتها قالت - أسود يقودكم بكتاب الله فاسمعوا له وأطيعوا ».
SA'ANNAN KUMA IN MUN CE MAKA SUNNA, TO TA K'UNSHI AL- QUR'ANI DA SUNNAR ANNABI (SAW) DA SUNNAR KHALIFOFINSA 4 A BISA FAHIMTAR SAHABBAI DA TABI'AI DA MALAMAN WANNAR AL'UMMA IRINSU MALIK, SHAFI'IY, AHMAD DA SAURANSU.
(12) NASIRU YA CE:
WATO ADDINI YA YARDA DAYAN MULKIN GURGUZANCI KO?
AMMAR:
A'A, AI BA A KAN TSARI SHUGABANCI MUKE MAGANA BA. TSARI KAM TSARIN ADDININ MUSLUNCI NE, AMMA KUMA YANAYIN HAWAN SHUGABAN NE YA ZAMA DA K'ARFI. TO ZA MU BISU A BISA BIN ALLAH DA MANZONSA. IN KUMA SUN YI UMURNI DA SA'BANIN HAKA TO BABU 'DA'A GARESU. KAMAR YADDA KA GANI A HADISAN DA NA AMBATA A SAMA.
(13) NASIRU YA CE:
SANNAN KUMA KANA NUFIN KACE WACCAN MAGANARDA UMAR YAFADA CEWA WANDA DUK AKA ZABESHI BATAREDA SHAWARAR MUSULMI BASHIDA BAI'A MGANACE ABARYIN WATSI DA ITA?
AMMAR:
TABBAS MAGANAR UMAR (RA) BA ABIN WATSI BA CE. AMMA AKWAI LOKACIN DA WANI ZAI FI K'ARFIN MUTANE YA YI GALBA A KANSU, TO SHI KENAN YA ZAMA SHUGABA, SAI A K'YALE SHI A BABIN NEMAN MASLAHA DA SULHU, KAMAR YADDA HASAN (RA) YA YI SULHU DA MU'AWIYA (RA), KUMA ANNABI (SAW) YA YABE SHI A KAN HAKAN.
(14) NASIRU YA CE:
AMSA : ME AKE NUFI DAYIN SHAWARA KUMA YAUSHE AKAYI SHAWARA AKAN ZABEN ABUBAKAR, SUWAYE SUKAYI SHAWARAR ZODA WAJEN MUGANI BAWAI HASHASHENKA BA. SANNAN KUMA KANA NUFI WANNAN MAGANA TA UMAR ABAR AJEFA MASA KAYANSACE ?
ألا وإنه بلغني أن فلانا قال لو قد مات عمر بايعت فلانا فمن بايع امرأ من غير مشورة من المسلمين فإنه لا بيعة له ولا للذي بايعه فلا يغترن
أحد فيقول إن بيعة أبي بكر كانت فلتة ألا وإنها كانت فلتة إلا أن الله وقى شرها
AMMAR:
ZA'BEN ABUBAKAR (RA) YA FARU NE BAYAN SHURA (TATTAUNAWA) A TSAKANIN JAGORORIN ANSAR DA MUTUM 3 MANYA DAGA CIKIN MUHAJIRUNA A "SAQIFATU BANI SA'IDA".
SA'ANNAN KUMA LALLAI UMAR (RA) YA CE:
ألا وإنها كانت فلتة إلا أن الله وقى شرها
TO AMMA YAYA ZA KA YI DA FA'DINSA:
ليس فيكم من يقطع إليه الأعناق مثل أبي بكر??
(15) NASIRU YA CE:
(1) ABIN TAMBAYA SHIN MU'AWIYA YACIKA WANNAN SHARADI DA AKA KULLA DASHI, SANNAN KUMA MAI NENE MATSAYIN WARWARE WANNAN SHARADIN DASHI MU'AWIYA YA AIKATA?
AMMAR:
KA GINA WANNAR TAMBAYAR CE A KAN WANNAR MAGANAR:
بسم الله الرحمن الرحيم هذا ما صالح عليه الحسن بن علي رضي الله عنهما معاوية بن أبي سفيان
صالحه على أن يسلم إليه ولاية المسلمين على أن يعمل فيهم بكتاب الله تعالى وسنة رسول الله وسيرة الخلفاء الراشدين المهديين وليس لمعاوية بن أبي سفيان أن يعهد إلى أحد من بعده عهدا بل يكون الأمر ...من بعده شورى بين المسلمين
TO ZA KA SAMU AMSA NE IN KA TABBATAR MINI DA INGANCIN WANNAR MAGANA.
(16) NASIRU YA CE:
(2) DAFARKO YAKAMATA MUSAN CEWA YAZIDU BASHUGABA BANE SABODA BAMU SAN SANDA AKACE AHLUSH-SHURANE SUKA NADASHIBA, IDAN KUMA DA AKWAI WAJEN SAI AZO DASHI SANNAN KUMA MUSAN SUWANE AHLU SHURADINDA SUKA NADASHI.
AMMAR:
WA YA GAYA MAKA TA HANYAR SHURA KAWAI AKE ZAMA SHUGABA??!
KA KAWO INDA AKA FA'DI HAKAN??!
(17) NASIRU YA CE:
(3) NABIYU NAFADA MUKU DAGA ABINDA YAGABATA CEWA ANSHAR DANTAWA MU'AWIYA CEWA BAZAI NADA WANIBA AMMA SAIGA TARIHI YATABBATARDA CEWA MU'AWIYA YANADA DANSA YAZID.
AMMAR:
TABBATAR DA INGANCINSA TUKUNA KAFIN KA YI TAMBAYA A KANSA. SABODA MU GINA ABUBUWAN A KAN DALILAI MASU INGANCI.
No comments:
Post a Comment