(31) NASIRU YA CE:
AMSA : NAYI MAKA TAMBAYA AKAN ME AKE NUFIDA SHAWARA AMMA BAKA BANI AMSABA.
AMMAR:
BAN SAN ABIN DA AKE NUFI DA SHAWARA BA, FIYE DA MA'ANARTA TA SHAWARA. IN KAI KANA DA WATA MA'ANA TA DABAN SAI KA KAWO MANA ITA.
(32) NASIRU YA CE:
TAMBAYA WANNAN MAGA DAKA KAWO KAINE KA KIRKIRA KO KUMA HAKA TAZO ACIKIN LITTAFI ARUBUCE, IDAN HAKA TAZO ACIKIN LITTAFI SAI KAKAWO SUNAN LITTAFIN DAKUMA WURIN MUGANI.
AMMAR:
BUKHARI NE YA RUWAITO:
عن عروة بن الزبير ، عن عائشة ، رضي الله عنها ، زوج النبي صلى الله عليه وسلم أن رسول الله صلى الله عليه وسلم مات ، وأبو بكر بالسنح- قال إسماعيل يعني بالعالية - فقام عمر يقول والله ما مات رسول الله صلى الله عليه وسلم قالت وقال عمر والله ما كان يقع في نفسي إلا ذاك وليبعثنه الله فليقطعن أيدي رجال وأرجلهم فجاء أبو بكر فكشف عن رسول الله صلى الله عليه وسلم فقبله قال بأبي أنت وأمي طبت حيا وميتا والذي نفسي بيده لا يذيقك الله الموتتين أبدا ثم خرج فقال أيها الحالف على رسلك فلما تكلم أبو بكر جلس عمر. فحمد الله أبو بكر وأثنى عليه وقال ألا من كان يعبد محمدا صلى الله عليه وسلم فإن محمدا قد مات ، ومن كان يعبد الله فإن الله حى لا يموت وقال : {إنك ميت وإنهم ميتون} وقال : {وما محمد إلا رسول قد خلت من قبله الرسل أفإن مات ، أو قتل انقلبتم على أعقابكم ، ومن ينقلب على عقبيه فلن يضر الله شيئا وسيجزي الله الشاكرين} قال فنشج الناس يبكون قال : واجتمعت الأنصار إلى سعد بن عبادة في سقيفة بني ساعدة فقالوا منا أمير ومنكم أمير فذهب إليهم أبو بكر وعمر بن الخطاب ، وأبو عبيدة بن الجراح فذهب عمر يتكلم فأسكته أبو بكر ، وكان عمر يقول والله ما أردت بذلك إلا أني قد هيأت كلاما قد أعجبني خشيت أن لا يبلغه أبو بكر ثم تكلم أبو بكر فتكلم أبلغ الناس فقال في كلامه نحن الأمراء وأنتم الوزراء فقال حباب بن المنذر لا والله لا نفعل منا أمير ومنكم أمير فقال أبو بكر لا ولكنا الأمراء وأنتم الوزراء هم أوسط العرب دارا وأعربهم أحسابا فبايعوا عمر ، أو أبا عبيدة فقال عمر بل نبايعك أنت فأنت سيدنا وخيرنا وأحبنا إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم فأخذ عمر بيده فبايعه وبايعه الناس فقال قائل قتلتم سعد بن عبادة فقال عمر قتله الله.
(33) NASIRU YA CE:
SAIDAI KUMA KASANI CEWA KAWO NUQDAR KARSHE DAKAYI BAISA ZABEN YAZAMA BA " FALTATAN" BA.
AMMAR:
AI BA MAKAWA KO DAI KA HA'DA JUMLOLIN 2 KA FASSARA KO KUMA KA BARSU DUKA 2.
NA CE:
SA'ANNAN KUMA LALLAI UMAR (RA) YA CE:
ألا وإنها كانت فلتة إلا أن الله وقى شرها
TO AMMA YAYA ZA KA YI DA FA'DINSA:
ليس فيكم من يقطع إليه الأعناق مثل أبي بكر??
DOLE SAI DAI KA HA'DASU KA FASSARASU TARE. IN KA 'DAUKI 'DAYA KA BAR 'DAYA YA ZAMA SON ZUCIYA KENAN!!
(34) NASIRU YA CE:
AMSA : NIFA INA KAFA MAKA HUJJANE DACEWA WANCAN SULHUNDA AKAYISHI DA MU'AWIYA BAHAKA AKAYISHI SAKA-KABA AN KULLASHINE TAREDA SHARADI, TO SHINE NAKE TAMBAYARKA AKN CEWA SHIN MU'AWIYA YACIKA SHARADIN, SANNAN KUMA MAI NENE MATSAYIN WANDA YAKAR SHARADIN?
AMMAR:
QISSAR DA KA KAWO NA SHARA'DIN SULHUN, MENENE INGANCINTA??!
IN TA TABBATA SAI MU BA KA AMSA, IN KUMA TA K'ARYA CE, TO BA BUK'ATAR KA NEMI AMSAR TAMBAYARKA.
(35) NASIRU YA CE:
AMSA : UMAR DAN KHATDABINE YAKE FADA SAURA KUMA KASAKE JEFA MAGANARSA AKWANDON SHARA :
فلانا فمن بايع امرأ من غير مشورة من المسلمين فإنه لا بيعة له ولا للذي بايعه
AMMAR:
HAKA NE, MAGANAR UMAR (RA) TA TABBATAR DA KASANCEWAR SHURA 'DAYA CE DAGA CIKIN HANYOYIN ZA'BAN SHUGABA, KAMAR YADDA ANNABI (SAW) YA UMURCE MU DA YIN HAK'URI IN AN SHUGABANCE MU A BISA TILAS DA YIN GALABA A KANMU.
(36) NASIRU YA CE:
AMMAR : TABBATAR DA INGANCINSA TUKUNA KAFIN KA YI TAMBAYA A KANSA. SABODA MU GINA ABUBUWAN A KAN DALILAI MASU INGANCI.
AMSA :
قال بن أبي خيثمة حدثنا هارون بن معروف حدثنا ضمرة عن ابن شوذب قال: لما قتل علي سار الحسن في أهل العراق ومعاوية في أهل الشام فالتقوا فكره الحسن القتال وبايع معاوية على أن يجعل العهد له من بعده
الاصابة
AMMAR:
DUK DA CEWA; KA KASA TABBATAR MANA DA INGANCI KO RASHIN INGANCIN WANNAR MAGANA, AMMA MAGANAR BA TA NUNA CEWA; MU'AWIYA (RA) YA WARWARE SHARA'DIN DA SUKA YI DA HASAN (RA). DON BA KA ISA KA CE; MU'AWIYA (RA) YA WARWARE ALK'AWARI BA, HAR SAI IN YA RIGA HASAN (RA) RASUWA. AMMA YADDA ABIN YA KASANCE AKASIN HAKA NE. TUN DA HASAN (RA) YA RIGA MU'AWIYA (RA) RASUWA, TO GAWARSA CE ZA TA YI SHUGABANCIN IN MU'AWIYA (RA) YA BA SHI SHUGABANCIN??!
*** DON HAKA BABU MAI DA'AWAR MU'AWIYA (RA) YA WARWARE ALKAWARIN DA YA YI MA HASAN (RA) SAI MARAS HANKALI!!
No comments:
Post a Comment