(25) NASIRU YA CE:
AMSA : KAJI SHIGAR KUSA INCI TARANE ATSAKAR KANKA SHINE YANZU KAKESO KAYIWA MAGANAR TAWILI GA ABINDA KACE " AMMA SHI HASAN (RA) JANYEWA YA YI WA MU'AWIYA (RA) NA HAR ABADA."
AMMAR:
TABBAS, IN NA FA'DI WATA MAGANA SAI KA 'DAUKE TA BA A BISA YADDA NAKE NUFI BA, DOLE NE IN YI MAKA TAWILIN DA ZA KA FAHIMTA.
LALLAI NI LOKACIN DA NA YI MAGANATA TA FARKO, BAN YI TUNANIN ABIN DA ZAI KASANCE A BAYAN MU'AWIYA (RA) BA. KAWAI ABIN DA NAKE NUFI DA "HAR ABADA" SHI NE; HAR ABADA HASAN (RA) YA MIK'A WA MU'AWIYA (RA) KHALIFANCI, TA YADDA BA ZAI SAKE KAR'BA DAGA WAJENSA BA, ALHALI YANA RAYE.
(26) NASIRU YA CE:
KARDAI ABIGE DABATUN SUKAR MUT'A ABUGE DA AIKATA IRINTA WASIGINI MALAMIN RUQYA.
AMMAR:
AI DUK WANDA YA YI ZINA YA SAN ZUNUBI YA AIKATA, YANA FATAN TUBA DA GAFARAR ALLAH. AMMA SHI MAI MUTU'A HALALTA ZINA YA YI, KUMA YANA GANIN KYAKKYAWAN AIKI YAKE YI. ALHALI HALALTA HARAM KAFIRCI NE.
قل هل ننبئكم بالأخسرين أعمالا (103) الذين ضل سعيهم في الحياة الدنيا وهم يحسبون أنهم يحسنون صنعا (104)
(27) NASIRU YA CE:
AMSA :
عَنْ عَائِشَةَ قَالَتْ
قَالَ لِي رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي مَرَضِهِ ادْعِي لِي أَبَا بَكْرٍ أَبَاكِ وَأَخَاكِ حَتَّى أَكْتُبَ كِتَابًا فَإِنِّي أَخَافُ أَنْ يَتَمَنَّى مُتَمَنٍّ وَيَقُولُ قَائِلٌ أَنَا أَوْلَى وَيَأْبَى اللَّهُ وَالْمُؤْمِنُونَ إِلَّا أَبَا بَكْرٍ
MENE MATSAYIN WANNAN HADISIN AWAJENKU? SANNAN KUMA KATABA GANIN ACE ANNABI YAGABATAR DAKAI, SANNAN KAI KUMA WAI SAI KAI KAGABATARDA WADANSU AKANKA?
AMMAR:
MATSAYIN WANNAN HADISI A WAJENMU, INGANTACCE NE. KUMA YANA DAGA CIKIN HUJJOJI MASU K'ARFI DA SUKE ISHARA ZUWA GA KHALIFANCIN ABUBAKAR (RA).
SA'ANNAN SHIN HADISIN YA NUNA AN KIRA ABUBAKAR (RA) 'DIN??
KO AN RUBUTA TAKARDAR??
KO ABUBAKAR (RA) YA SAN DA WANNAN HADISIN??
IN WANNAR MAGANA NASSI CE A KAN ABUBAKAR (RA) NE KHALIFA, KUMA YA SAN DA ITA, A NAN NE ZAI ZAMA ABIN ZARGI, AMMA IN BA NASSI BA CE, KO KUMA BAI SAN DA ITA BA, TO LALLAI BA ZARGI A KANSA.
(28) NASIRU YA CE:
AMSA : KAWO MANA MISALAN HAKA BAWAI MISALI GUDA DAYABA TUNDA ABIN BAI NUNA SAU DAYA BANE ANNABI YATABA FIFITA SHIBA. AYAUSHENE UMAR YAGABATARDA SHI? HABA KANA INA ASANDA UMAR YAKE CEWA:
ألا وإنها كانت فلتة إلا أن الله وقى شرها
AMMAR:
(A) ANNABI (SAW) YA NA'DA SHI AMIRUL HAJJI A SHEKARA TA 9.
(B) YA GABATAR DA SHI SALLA A RASHIN LAFIYANSA NA AJALI.
(29) NASIRU YA CE:
TO NIDAI NAYI IYAKAR KOKARINA ACIKIN WANNAN HADISIN DOMIN NAGANO INDA ANNABI YAHALATTA MULKIN MUTUMINDA YAZUBDA JININ MUSULMAI ABIN YACI TURA BANGANIBA, KOSHIYASA YAKI YAFASSARA HADISIN?
AMMAR:
NI GA ABIN DA NA CE:
" AI MU A SUNNA, DUK WANDA YA YI GALBA A KAN MUTANE YA ZAMA SHUGABA"
A HADISIN SAI AKA CE:
في منشطنا ومكرهنا وعسرنا ويسرنا وأثرة علينا
DUK LOKACIN DA AKA KIRA "GALBA" TO A HALI NE NA RASHIN SO, KO TSANANI, KO FIFITA WASU A KAN WASU. TO HADISIN YA AMBACI WA'DANNAN ABUBUWA GUDA 3:
• ومكرهنا
• وعسرنا
• وأثرة علينا
(30) NASIRU YA CE:
AISHI UMAR BAICE BANDA LOKACI KAZABA WANNAN KIRKIRAR KACE GADAI ABINDA YAKE CEWA :
فمن بايع امرأ من غير مشورة من المسلمين فإنه لا بيعة له ولا للذي بايعه
ANAN UMAR YANA LALATA SHUGABANCIN MUTUMINDA AKA ZABESHI BADA SHAWARA TA MUSULMAIBA INAKUMA GA MUTUMINDA KWATA YAYI DABAKIN TAKOBI? TO KASANI KODA BAKIN MENE YAKWATA UMAR YACE AKASHE SHI BAWAI AKYALE SHIBA.
AMMAR:
ANA HA'DA NASSOSHI NE AYI AIKI DA SU GABA 'DAYA. BA A JEFAR DA WANI A 'DAUKI WANI BA, MATUK'AR ZA A IYA HA'DASU DUKA AYI AIKI DA SU. DON HAKA IN MUN HA'DASU, SAI MAGANAR UMAR (RA) TA YI AIKIN A HALIN ZAMAN LAFIYA DA KWANCIYAR HANKALI. SAI AYI SHURA WAJEN ZA'BEN SHUGABA. IN KUMA A HALIN TASHIN HANKALI NE, TO WANDA YA YI GALBA YA ZAMA SHUGABA, KO DA KUWA BA SHI YA FI CANCANTA BA.
MALAMAN USULUL FIQHI SUN TABBATAR DA CEWA; BA A TAFIYA GA "TARJIHI" A TSAKANIN NASSOSHI GUDA 2, SAI IN BA ZAI YIWU AYI "JAM'INSU" BA. HAKA BA A TAFIYA GA "NASKHU" SAI IN BA ZA A IYA TARJIHINSU BA. DON HAKA TUN DA ZA A IYA JAM'IN MAGANAR UMAR (RA), DA TAKE NUNA AYI SHURA, DA HADISAN ANNABI (SAW) DA SUKE NUNA AYI 'DA'A MA WANDA YA ZAMA SHUGABA KO DA A HALIN RASHIN SO KO TSANANI KO FIFIKO, BA ZA A TAFI GA "TARJIHIN" MAGANAR UMAR (RA) A KAN SAURAN NASSOSHIN BA. A'A, DUKA ZA MU HA'DASU MU YI AIKI DA SU GABA 'DAYA, GWARGWADON YADDA HALI YA DACE DA KOWANNE.
IN KA KARANTA USULUL FIQHI LA'ALLA KA SAN WANNAN, IN KUMA BA KA SANI BA, ZA MU IYA GUTSURO MAKA DAGA LITTATAFAN MALAMANKA NA SHI'A, MU KAFA MAKA HUJJA DA SU.
No comments:
Post a Comment