(37) NASIRU YA CE:
AMSA : TO AI SAI KAFARA TABBATAR MANADA ABINDA YASA YAZIDU YAZAMA SHUGABA.
AMMAR:
ABIN DA YA TABBATAR DA SHUGABANCIN YAZIDU SHI NE; KHALIFANTARWAN DA BABANSA SHUGABA MU'AWIYA (RA) YA YI, KAMAR YADDA HASAN (RA) YA NEMI MU'AWIYA (RA) YA KHALIFANTAR DA SHI A BAYANSA.
SA'ANNAN KO DA MUTANE BA SU GOYON BAYAN YAZIDU, TO ANNABI (SAW) YA YI MANA UMURNI DA MU YI HAK'URI, MU YI BIYAYYA KO DA BA MA SO AN FI K'ARFINMU. KAMAR YADDA NA GABATAR MAKA DA HADISAI A KAN HAKA.
DA WANNAN YAZIDU YA ZAMA SHUGABA, WANDA WAJIBI NE A YI MASA 'DA'A, SABODA ANNABI (SAW) YA YI UMURNI DA 'DA'A, KO DA AN SHUGABANCE MU A BISA TILAS.
(38) NASIRU YA CE:
AMMAR : AI NI NE NA YI MUKU WANNAR TAMBAYAR, DON HAKA A WAJENKA AKE NEMAN AMSAR. IN BA KA GANE MAGANAR BA NE, TO KOMA KA SAKE KARANTAWA.
AMSA : KAIMA BAKA FAHIMCI ABINDA KARUBUTABA SHIYASA KAKIDIME AI GA ABINDA KAKE FADA WANDA SHI ZAI NUNA CEWA BATAMBAYRMU KAKEYIBA :
AMMAR:
TO BARI IN MAIMAITA MUKU TAMBAYAR TAMU, GA TA KAMAR HAKA:
A WAJEN 'YAN SHI'A MATSAYIN HASAN (RA) DA HUSAINI (RA) DUKA 'DAYA NE, DUKANSU IMAMAI NE. AMMA SAI AKA SAMU HASAN (RA) YA YI MUBAYA'A MA WANDA BAI CANCANCI SHUGABANCI BA, WATO MU'AWIYA (RA). AMMA SHI KUMA HUSAINI (RA) K'IN YIN BAI'A YA YI GA SHUGABAN ZAMANINSA, WANDA BAI CANCANCI SHUGABANCI BA. DON HAKA MENENE MATSAYIN ABIN DA KOWANNENSU YA AIKATA, TUN DA SUN AIKATA ABUBUWA NE MABANBANTA, SABODA DOLE YA ZAMA 'DAYA YA AIKATA DADAI, 'DAYA KUMA YA AIKATA BA DADAI BA. DON HAKA HUSAINI NE YA YI DADAI, HASAN YA YI KUSKURE, KO KUMA HASAN NE YA YI DADAI HUSAINI YA AIKATA BA DADAI BA??!
*** MALAM NASIRU, A GAMSAR DA MU>>>
(39) NASIRU YA CE:
AMMAR : A INA NA FA'DI WANNAR MAGANAR??
AMSA : SABODA KANUNA CEWA SHI DANTAWAYENE
AMMAR:
TABBAS DAI KA TABBATA MAK'ARYACI MARAS KUNYAN YIN K'ARYA DA SHARRI WA MUTANE. SABODA YIN TAWAYE SHI NE K'IN YIN BAI'A. KUMA BA DOLE IN MUTUM YA YI TAWAYE MA SHUGABA BA SAI YA YAK'E SHI BA.
*** KO DA YAKE, K'ARYA A WAJEN 'DAN SHI'A BA ABIN MAMAKI BA NE!!
(40) NASIRU YA CE:
AMSA : WAYACE SHIMA IMAM HASAN ZAIYI SULHU AMMA DAYA SABAWA HAKAN SHIYASA YAZAMA MAI AIKATA KUSKURE?
AMMAR:
SHI'A NE SUKA CE; IMAMA FARILLA CE, RUKUNI CE TA ADDINI, WANDA YA YI INKARINTA YA ZAMA KAFIRI. KUMA BABU ADDINI GA WANDA YA KASANCE BA A K'ARK'ASHIN IMAMI BA, KUMA ALLAH YA NASSANTA IMAMAI. NA KAWO DALILAI A KAN HAKA. TO DON HAKA ABIN DA HASAN (RA) YA AIKATA DOLE YA ZAMA KUSKURE – A BISA RA'AYIN SHI'A -. SABODA YA JANYE WA MU'AWIYA (RA) YA YI MASA BAI'A, DON HAKA:
(A) BAI YI AIKI DA NASSIN DA ALLAH YA SAUK'AR A KAN IMAMANCINSA BA.
(B) YA BAR RUKUNI DAGA CIKIN RUKUNAN ADDINI.
(C) YA BAR MUTANE SUN 'BATA ADDININSU, SABODA DUK ADDININ DA MUSULMAI SUKA YI A TSAWON ZAMANIN MU'AWIYA (RA) AIKIN BANZA NE.
(D) KOWANE 'DAYA DAGA WA'DANNAN ABUBUWA GUDA 3 SA'BA MA ALLAH NE. DON HAKA - A BISA K'A'IDAR SHI'A – HASAN (RA) YA YI KUSKURE MAI GIRMA. KUMA WANNAN DOLE YA WARWARE MASA "ISMARSA", DON HAKA SHI BA MA'ASUMI BA NE.
(41) NASIRU YA CE:
SANNAN KUMA TAYAYA YAZAMA- A BISA K'A'IDOJIN SHI'A - IN 'DAYA YA YI DADAI, TO 'DAYA YA YI KUSKURE.?
AMMAR:
NA GABATAR MAKA DA K'A'IDAR SHI'A A KAN IMAMA. RUKUNI CE TA ADDINI, INKARINTA KAFIRCI NE, BABU ADDINI GA WANDA YA YI ADDINI BA TARE DA IMAMI BA. WANNAN SHI NE K'A'IDAR SHI'A DA NAKE FA'DI.
A HAKA SAI AKA SAMU HASAN (RA) YA SAUKA DAGA WANNAN MATSAYI NA IMAMA, TO SHIN HASAN (RA) YA YI LAIFI??!
IN KUMA SULHUN DA HASAN (RA) YA YI NE DADAI, TO SHI HUSAINI DON ME YA SA YA YI TAWAYE??!
BARIN HUSAINI GA AIKATA SULHU IRIN NA HASAN (RA), ALHALI SHI NE DADAI, SHI YAKE TABBATAR DA KUSKUREN AIKINSA.
*** INA FATA DA MAI HANKALI NAKE MAGANA, BA DA WAWA BA!!
SABODA BABU WANDA BA ZAI FAHIMCI WANNAN BA, SAI WAWA MARAS HANKALI.
(42) NASIRU YA CE:
(9) ANAN WAJEN AMMAR YANA RUSA MANA KHALIFANCIN UMAR DANA USMANU SABODA TUSHENSU SHINE ABUBAKAR, ABUBAKARNE YAZABI UMAR SHIKUMA UMAR YAKAFA KWAMITI NA MUTUM SHIDA YACE DUK WANDA AKA ZABA ACIKINSU DAI-DAINE SAI AKA ZABI USMANU.
AMMAR : INA DALILI??!
NASIRU: AMSA : AI NABAKA DALILI KOMAWA ZAKAYI KASAKE KARANTASHI ACIKIN NUTSUWA GABANKA YADAINA FADUWA.
AMMAR:
WANNAN ZILLIYAR TAKA BA ZA TA KAIKA KO INA BA, KA KAWO DALILI KAWAI MALAM!!
MASU IYA MAGANA SUKA CE:
والدعاوى ما لم يقيموا عليها *** بيّنات أصحابها أدعياء
*** ABIN LURA:
NASIRU BA YA IYA YIN JAWABI A KAN AYOYIN DA MUKE KAWOWA, KUMA BA IYA YIN JAWABI A KAN RUWAYOYIN IMAMANSU DA MAGANGANUN MALUMANSU DA MUKE KAWO MASA. YA KAMATA KA RINK'A WARWARE MANA MATSALOLIN DAKE CIKINSU, DA BAYANIN ABIN DA SUKA K'UNSA.
*** MUN NEMI NASIRU DA YA DENA SHIGO DA ABIN DA BAI SHAFI MAUDHU'INMU BA KAI TSAYE, AMMA DA YAKE SHI GALADIMA NE A TSILLA – TSILLA BA ZAI TA'BA IYA DENA YIN ABIN NASA BA.
*** TO KA SANI; MUN YI KUSAN DAWOWA GABA 'DAYA KAN MAUDHU'INMU KAWAI. DON HAKA NAN BA DA JIMAWA BA, ZA MU TAK'AITA MAGANGANUNMU A KAN ASALIN MAUDHU'I. TSILLA – TSILLAR TA ISA HAKA. DON HAKA KA YI K'OK'ARI KA BA MU ABIN DA MUKA NEMA DAGA GAREKA, WATO GAMSASSHIYAR AMSA A KAN TAMBAYOYINMU DA MUKA GABATAR TUN A FARKON POST.
ALHAMDU LILLAH.
ALLAH YA SA MU DACE.
No comments:
Post a Comment