(6) KAMAR YADDA ALLAH YA K'ARFAFI ADDININSA DA ALIYU (RA), HAKA YA K'ARFAFE SHI DA SAURAN MUHAJIRUNA DA ANSAR. KAI, K'ARFAFAN DA ALLAH YA YI WA ANNABI (SAW) DA "AL- SABIQUNAL AUWALUNA MINAL MUHAJIRINA WAL ANSAR", DA YAWANSU SUN FI ALIYU (RA) TAIMAKON ANNABI (SAW) DA ADDININ ALLAH GA WANDA YA SA "SIRAN" ANNABI (SAW). DON HAKA ALIYU (RA) YANA CIKIN WAZIRAN ANNABI (SAW), WA'DANDA SUKA TAIMAKI ANNABI (SAW) DA ADDININ ALLAH, AMMA DA YAWA DAGA CIKIN SAHABBAI SUN FI SHI TAIMAKON ANNABI (SAW) DA K'ARFAFA SHI. DON HAKA KAWO WANNAR AYAR DA SIFFANTATA DA ALIYU (RA) KAWAI SHACI - FA'DI NE.
(7) WANNAR AYAR DA KA KAWO
وَأَشْرِكْهُ فِى أَمْرِى
BA TA DA MUNASABA DA ALIYU (RA), SABODA ANNABI MUSA (AS) YANA ROK'ON ALLAH NE DA YA HA'DA HARUNA (AS) YA ZAMA TARE DA SHI WAJEN ISAR DA SAK'ON ALLAH GA FIR'AUNA, DON YA SAMU NITSUWA, DA K'ARFIN ZUCIYA.
DON HAKA, SHIN ALLAH YA HA'DA ALIYU (RA) DA ANNABI (SAW) WAJEN ISAR DA MANZANCI??!
SA'ANNAN BA TA DA ALAK'A DA AYAR "MUBAHALA", DUK WANDA YA SAN LARABCI YA SAN HAKA. SABODA KALMAR أنفسنا ANA AMFANI DA ITA GA WANDA ZAI YI MAGANA GA KANSA DA WA'DANDA SUKE TARE DA SHI A JINSINSA. KUMA KASANCEWAR MUBAHALA TANA KASANCEWA NE DA DANGI, DON HAKA BA TANA NUFIN SUNA TARE A ZATINSA BA NE
.
** KA KAWO WANI HADISI KAMAR HAKA:
“ANA MIN ALIYUN WA ALIYUN MINNI” (BUKHARI).
BAN SAME SHI A CIKIN BUKHARI BA. DON HAKA KA YI MINI BAYANIN INDA ZAN SAME SHI A LITTAFIN??
KUMA WANNAN BA ABU NE DA ALIYU (RA) YA KE'BANTA DA SHI SHI KA'DAI BA. ANNABI (SAW) YA FA'DI IRIN WANNAN GA MUTANE MASU YAWA:
1. 'YAR HAMZA:
{ أنت مني وأنا منك }
2. ZAIDU BN HARITHA:
{ أنت أخونا ومولانا }
3. ASH'ARIYAWA:
{ الأشعريون هم مني وأنا منهم }
4. JULAIBIB:
{ أنت مني وأنا منك }
5. SAURAN MUMINAI WA'DANDA BA SU YIN GISHSHU, DA YAK'AR MUSULMI.
{ من غشنا فليس منا ومن حمل علينا السلاح فليس منا }
*** DON HAKA IN KANA GANIN WANNAR AYAR:
وَأَشْرِكْهُ فِى أَمْرِى
TA DA CE DA ALIYU (RA) DON ANNABI (SAW) YA CE MASA:
أنت مني وأنا منك
TO SU MA WA'DANCAN DA ANBATA ANNABI (SAW) YA FA'DI IRIN HAKA GARESU, SU MA SUN YI TARAYYA DA SHI ANNABIN (SAW), DON HAKA BA TA TAK'AITA A KAN ALIYU (RA), SU MA SAURAN DUKKANSU WAZIRAN ANNABI (SAW) NE.
(8) SHI'ATU ALI YA CE:
"(D) KARA DA CEWA BANU ISRA’ILA SUN KAUDA KAI DAGA BIN HARUNA (A.S) BAYAN TAFIYAR ANNABI MUSA (A.S) KAMAR YADDA YAN SAQIFA SUKA KAUDA KAI DAGA BIN IMAM ALI (A.S) BAYAN WAFATIN MANZON ALLAH (S.A.W.A)."
WANNAN K'ARYA NE, KWATANCEN BAI YI BA. AI BANU ISRA'ILA BA SUN K'I BIN HARUNA BA NE A BAYAN RASUWAR MUSA (AS), BARE KA KAMANTA SHI DA ZA'BEN ABUBAKAR (RA) A BAYAN RASUWAR ANNABI (SAW).
WANDA ZA SU YI DAIDAI SHI NE; IN AN K'I BIN ALIYU (RA) A LOKACIN DA ANNABI (SAW) YA WAKILTA SHI A MADINA A YAK'IN TABUKA, SHI NE ZAI DACE DA TAWAYEN BANU ISRA'ILA A LOKACIN DA ANNABI MUSA (AS) YA WAKILTA HARUNA (AS) A CIKINSU A BAYAN YA TAFI MIQATI.
*** YA KAMATA KU RINK'A AUNA ABUBUWA DA INGANTACCEN MA'AUNI, BA KAWAI DA SON RAI BA.
(9) TO IN ANNABI (SAW) YANA SANE DA WA'DANNAN AYOYIN, DON ME YA SA BAI FA'DE SU A LOKACIN DA YA FA'DI HADISIN BA??!
(10) LALLAI WAKILCIN ALIYU (RA) A MADINA YA K'ARE A LOKACIN DA ANNABI (SAW) YA DAWO. AMMA FA'DIN ANNABI (SAW):
إلا أنه لا نبي بعدي
KAWAI YANA NUNA BANBANCIN DA KE TSAKANIN HARUNA (AS) DA ALIYU (RA) NE, DUK DA CEWA; SUN YI TARAYYA A WAKILCIN ANNABAWA, SHI HARUNA YA WAKILCI ANNABI MUSA (AS) A LOKACIN TAFIYARSA MIQATI, SHI KUMA ALIYU (RA) YA WAKILCI MANZON ALLAH (SAW) A LOKACIN YAK'IN TABUKA.
MA'ANA; SHI HARUNA ANNABI NE, AMMA ALIYU (RA) BA ANNABI BA NE, SABODA BABU WANI ANNABI A BAYAN MANZON ALLAH (SAW).
DON HAKA WAKILCIN ALIYU (RA) YA K'ARE A BAYAN DAWOWA DAGA TABUKA, KAMAR YADDA WAKILCIN HARUNA (AS) YA K'ARE A BAYAN DAWOWAN ANNABI MUSA (AS) DAGA MIQATI.
*** DON HAKA, ABIN DA YA SA WAKILCIN ALIYU (RA) BAI CIGABA BA, SABODA SHI MA HARUNA (AS) WAKILCINSA BAI CIGABA BA, KAI, HASALI MA HARUNA (AS) RASUWA YA YI KAFIN MUSA (AS), YUSHA'U NE YA ZAMA KHALIFANSA, KAMAR YADDA ABUBAKAR (RA) YA ZAMA KHALIFAN ANNABI (SAW) A BAYANSA.
*** TUN DA ANNABI (SAW) BAI KAMANTA ALIYU (RA) DA YUSHA'U BA, TO ANNABI (SAW) BA KHALIFANCI A BAYAN WAFATINSA YAKE NUFI BA A HADISIN "MANZILA".
(11) DON ME YA SA ALIYU (RA) BAI KAFA WA SU ABUBAKAR (RA) HUJJA DA WANNAN HADISI BA, BAYAN AN ZA'BI ABUBAKAR (RA) A MATSAYIN KHALIFAN ANNABI (SAW), DON YA NUNA CEWA; SHI YA CANCANCI WANNAN MATSAYI??!
HAKA A BAYAN RASUWAR ABUBAKAR (RA) A LOKACIN FARA KHALIFANCI UMAR (RA), DA KUMA BAYAN RASUWAR UMAR (RA) A LOKACIN DA AKA SA SHI ALIYUN (RA) A CIKIN KOMITIN ZA'BEN KHALIFA, DON ME YA SA BAI KAFA MUSU HUJJA DA WANNAN HADISIN BA??!
ALLAH YA SHIRYEKA DA SAURAN 'YAN SHI'A.
No comments:
Post a Comment