ALLAH YA CE:
إنما وليكم الله ورسوله والذين آمنوا الذين يقيمون الصلاة ويؤتون الزكاة وهم راكعون
SURATUL MA'IDA AYA TA 55.
IBNUL MU'DAHHAR AL- HILLIY YA CE:
المنهج الثاني في الأدلة المأخوذة من القرآن والبراهين الدالة على إمامة علي عليه السلام من الكتاب العزيز، [ وهي ] أربعون برهانا:
الأول قوله تعالى: (إنما وليكم الله ورسوله والذين آمنوا الذين يقيمون الصلاة ويؤتون الزكاة وهم راكعون)، وقد أجمعوا على أنها نزلت في علي عليه السلام.
DALILI NA FARKO DAGA CIKIN DALILAI DA HUJJOJI 40 A KAN IMAMANCIN ALIYU (RA) DAGA ALQUR'ANI MAI GIRMA, SHI NE WANNAR AYAR. SABODA MALAMAI SUN YI IJMA'I A KAN CEWA; AYAR TA SAUK'A NE GAME DA ALIYU (AS).
TO ABUBUWAN TAMBAYA A NAN SU NE KAMAR HAKA:
1. SHIN DA GASKE NE MALAMAI SUN YI IJMA'I A KAN CEWA; A KAN ALIYU (RA) AYAR TA SAUK'A?
2. 'YAN SHI'A SUN YARDA CEWA; AYAR TA SAUK'A NE SABODA ALIYU (RA) YA YI SADAKA DA ZOBE A CIKIN RUKU'U YANA SALLA. ALHALI ALLAH YA YABI MASU KHUSHU'I A CIKIN SALLAH, ALLAH YA CE:
قد أفلح المؤمنون (1) الذين هم في صلاتهم خاشعون (2)
TO, CIRE ZOBE DAGA YATSAR HANNU DA MIK'A SHI GA MAI BARA SHIN BA YA KORE NITSUWA DA KHUSHU'I A CIKIN SALLAH??
3. AMMA A CIKIN AYAR ALLAH YA YI MAGANA NE DA JAM'IN MASU IMANI BA MUTUM 1 BA, ALLAH YA CE:
والذين آمنوا
DON HAKA SHIN ZAI YIWU A TAK'AITA AYAR A KAN ALIYU (RA) KAWAI??
4. IN AN TAK'AITATA A KAN ALIYU (RA) KAWAI, TO LALLAI TANA TAK'AITA IMAMANCI A KAN ALIYU (RA) NE KAWAI, BAN DA SAURAN IMAMAI 11 NA BAYANSA. DON HAKA KENAN AYAR TANA RUSHE IMAMANCIN SAURAN IMAMAI 11, TANA TAK'AITA IMAMANCIN GA ALIYU (RA) KAWAI. SABODA AYAR TANA 'DAUKE NE DA USLUBIN "HASR KO K'ASR". ALLAH CEWA YA YI:
إنما وليكم الله ورسوله والذين آمنوا
KALMAR "INNAMA" TANA ZUWA NE DA USLUBIN "HASR", (TAK'AITA HUKUNCI). DON HAKA HUKUNCIN AYAR YA TAK'AITA NE A KAN ALLAH DA ANNABI (SAW) DA ALIYU (RA) KAWAI, TA RUSHE IMAMANCIN SAURAN IMAMAI 11.
5. 'YAN SHI'A SUNA DA'AWAR CEWA; ALIYU (RA) YA SAKI DUNIYA, (YA YI MATA SAKI), DON HAKA BA SHI DA DUKIYA, SHI YA SA YAKE SA GAJEREN KAYA, YAKE CIN GURASA.
IBNUL MU'DAHHAR YA CE:
أنه عليه السلام كان أزهد الناس بعد رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم، وطلق الدنيا ثلاثا، وكان قوته جريش الشعير، وكان يختمه لئلا يضع الإمامان عليهما السلام فيه أدما وكان يلبس خشن الثياب، قصيرها، ورقع مدرعته حتى استحيى من راقعها، وكان حمائل سيفه من الليف، وكذا نعله.
TO AMMA IN MUN DUBA AYAR SAI MU GA TANA MAGANA NE A KAN ZAKKA, ALHALI ZAKKA KUWA BA TA KASANCEWA SAI GA MAI DUKIYA, TO TA YAYA AYAR NAN ZA TA DACE DA ALIYU (RA)??
6. KOWA YA SAN CEWA; ZAKKA BA A BAYAR DA ITA SAI DUKIYAR TA KAI NISABI, KUMA TA SHEKARA GUDA, SA'ANNAN A FITAR DA GWARGWADON ABIN DA ZA A BAYAR, TO SHIN WANNAN ZOBEN SHI YA KAI K'IMAR ABIN DA ZA A BA DA ZAKKAN, KUMA YA FITAR NE DAGA NISABIN DA YA SHEKARA??
7. ALLAH YA SIFFANTA K'UNGIYAR DA SUKA JI'BINCI SHI WANNAN IMAMI DA K'UNGIYA MAI CIN GALBA MASU RINJAYE, ALLAH YA CE:
ومن يتول الله ورسوله والذين آمنوا فإن حزب الله هم الغالبون (56)
TO ABIN TAMBAYA A NAN SHI NE:
a. ME YA SA 'YAN SHI'A BA SU CI GALBA A KAN DAULOLIN ZAMUNANSU (DAULOLIN BANU UMAYYA DA ABBASIYYA DA SAURANSU) BA, SU K'WACE KHALIFANCI SU KAFA DAULAR SHI'ANCI??
b. ME YA SA A KOWANE ZAMANI 'YAN SHI'A SU NE MARASA RINJAYE A CIKIN AL'UMMAR MUSULMI??
*** INA KIRA GA MASU HANKALI A CIKIN 'YAN SHI'A DA SU TAYA NI NAZARI A CIKIN WANNAR AYAR, TA YIWU MU ISA GA HAK'IK'ANIN LAMIRI.
ALLAH YA SA MU DACE.
No comments:
Post a Comment