Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Thursday, 25 February 2016

YAYE SHUBUHA A KAN ABUBAKAR (RA) (6)

Tahir Umar Sulaiman

* AMSARKA TA FARKO NA YI BAYANINTA A BAYA, A RADDIN DA NA YI WA Shiatu Ali NA FARKO, INDA NA CE:

"LIMANCI ABUBAKAR (RA) 'DAYA NE DAGA CIKIN TARIN FALALOLI DA MATSAYINSA, WA'DANDA SUKA SA AL'UMMA SUKA SALLAMA MASA. DON HAKA BA DOLE BA NE SAI SUN KAFA HUJJA DA JAN SALLAN A K'ASHIN KANSA A SAQIFA – DUK DA CEWA; YANA DAGA CIKIN DARAJOJINSA -, AMMA SAI UMAR (RA) YA DUNK'ULE DARAJOJIN NASA GABA 'DAYANSU – DAGA CIKI AKWAI LIMANCIN – SAI YA CE MA ABUBAKAR (RA):
بل نبايعك أنت، فأنت سيدنا وخيرنا وأحبنا إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم

"A'A, MA KAI ZA MU YI MUBAYA'A, DON KAI NE SHUGABANMU, MAFIFICINMU, KUMA MAFI SOYUWA GA ANNABI (SAW) A KANMU"
DON HAKA WANNAN YA K'UNSHI DUK WATA FALALA DA MATSAYI TA ABUBAKAR (RA), YA NUNA BABU WANDA YA KAI ABUBAKAR (RA) MATSAYI A WAJEN ANNABI (SAW) A CIKIN SAHABBAI. WANNAN KUWA SHI NE K'ARSHEN KAFA HUJJA".

** TAMBAYARKA TA BIYU KUWA; RASHIN NA'DIN DA ANNABI (SAW) YA YI, BA YA HANA WANI YA YI NA'DIN IN AKWAI MASLAHA GA YIN HAKAN, KO KUMA IN YANA TSORON WATA MATSALA IN BAI YI HAKAN BA. ANNABI (SAW) YA YI ISHARA ZUWA GA SAYYIDINA ABUBAKAR (RA), DAGA CIKIN ISHARORIN; YA NA'DA SHI LIMANCI A LOKACIN RASHIN LAFIYANSA NA AJALI, KUMA YA YI NIYYAR YA RUBUTA WASIYYA GARE SHI A RUBUCE, AMMA SAI YA GA HAKAN BA DOLE BA NE, SABODA ISHARORO DA YA YI ZUWA GA ABUBAKAR (RA) 'DIN SUN WADATAR, KUMA SABODA YAK'INI DA YAKE DA SHI A KAN CEWA; ABUBAKAR (RA) NE ZAI ZAMA KHALIFA A BAYANSA, HAR YAKE CEWA:
ويأبى الله والمؤمنون إلا أبا بكر

"ALLAH DA MUMINAI ZA SU K'I KOWA (A MATSAYIN KHALIFA) SAI ABUBAKAR"
BUKHARI DA MUSLIM.
DON HAKA, SABODA YAK'INI DA ANNABI (SAW) YAKE DA SHI, DA KUMA TABBACI NA CEWA; MUSULMAI BA ZA SU RARRABA BA A KAN ZABEN KHALIFA A BAYANSA, INDA ZA SU HA'DU SU YARDA DA ABUBAKAR (RA), TO SHI ABUBAKAR (RA) BA SHI DA WANNAN YAK'ININ. SABODA SHI BA ANNABI BA NE, BA A YI MASA WAHAYI. DON HAKA NA'DA UMAR (RA) DA YA YI YA FI ZAMA MASLAHA, DON KAR A BAYANSA A SAMU SA'BANI WAJEN ZA'BEN KHALIFA, MUSAMMAN GANIN AN SO A SAMU HAKAN A FARKO, BAYAN RASUWAR ANNABI (SAW), LOKACIN DA ANSAR SUKA YI YUNK'URIN ZA'BEN KHALIFA DAGA CIKINSU. TO SABODA KAUCE MA SAKE FARUWAN IRIN WANNAN, KUMA SABODA KASANCEWAR UMAR (RA) YA FI FALALA A KAN KOWA BAYAN ABUBAKAR (RA) SHI YA SA ABUBAKAR (RA) YA NA'DA SHI.
KUMA WANNAN IJTIHADI NE NASA, IN YA YI DADAI YANA DA LADA 2, IN KUMA YA YI KUSKURE YANA DA LADA 1.
KUMA DA MA ANNABI (SAW) YA HORE MU DA BIN SUNNARSA DA KUMA SUNNAR KHALIFOFINSA SHIRYAYYU.

*** AMMA FA'DIN WANI DAGA CIKIN MUTANE:
ماذا تقول لربك إذا وليت علينا فظا غليظا.

TO SHIN BA KA KARANTA RADDIN DA ABUBAKAR (RA) 'DIN YA YI MUSA BA NE??
GA RADDIN DA YA YI MUSA KAMAR HAKA:
قال أبو بكر: أبربي تخوفونني؟ أقول: اللهم استخلفت عليهم خير خلقك.

TO WANNAR ITA CE AMSAR DA ABUBAKAR (RA) ZAI BA MA ALLAH, CEWA; YA NA'DA UMAR (RA) NE SABODA YA FI KOWA CANCANTA KHALIFANCI.

NA 2; AI IRIN WANNAN HATTA A ZAMANIN ANNABI (SAW) YA FARU. SABODA LOKACIN DA ANNABI (SAW) YA NA'DA USAMA BN ZAID (RA) WANI DAGA CIKIN MUTANE YA YI SUKA A KAN HAKA, HAR ANNABI (SAW) YA YI MUSU RADDI:
عن عبد الله بن عمر ، رضي الله عنهما أن رسول الله صلى الله عليه وسلم بعث بعثا وأمر عليهم أسامة بن زيد فطعن الناس في إمارته فقام رسول الله صلى الله عليه وسلم فقال إن تطعنوا في إمارته فقد كنتم تطعنون في إمارة أبيه من قبل وأيم الله إن كان لخليقا للإمارة وإن كان لمن أحب الناس إلي وإن هذا لمن أحب الناس إلي بعده.

DON HAKA DUK ABIN MUTANE ZA SU FA'DA A KAN UMAR (RA), TO LALLAI SHI YA FI KOWA CANCANTAR KHALIFANCI A BAYAN ABUBAKAR (RA). KUMA SUKANSU GA HAKAN, BA SHI DA WANI TASIRI KAMAR YADDA SUKA GA SHUGABANCIN USAMATU BN ZAID (RA) BAI YI WANI TASIRI BA.

INA FATAN KA GAMSU.

No comments:

Post a Comment