Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Thursday, 25 February 2016

YAYE SHUBUHA A KAN ABUBAKAR (RA) (7)

Tahir Umar Sulaiman, BA A BA KA AMSA BA, KO KUMA BA KA GAMSU BA??

* NA RINJAYAR DA MAGANAR ABUBAKAR (RA) NE SABODA ALIYU (RA) YA CE:
خير هذه الأمة بعد نبيها أبو بكر ثم عمر

"MAFIFICIN WANNAR AL'UMMAR BAYAN ANNABINTA SHI NE ABUBAKAR, SAI UMAR".

** KANA CEWA; "SAURAN SAHABBAI...."
ALHALI WA'DANDA SUKA YI MAGANAR BA SU WUCE MUTUM 1 NE KO 2 ZUWA 3.
DON HAKA YANA DA KYAU KA RINK'A KIYAYE LAFUZAN DA ZA KANA AMFANI DA SU. DON IN KA CE: "sauran sahabban", KA NUNA ABUBAKAR (RA) NE KAWAI SHI KA'DAI YAKE DA RA'AYIN NA'DA UMAR (RA), SAURAN SAHABBAI KUMA GABA 'DAYA BA SU YARDA BA. ALHALI KUMA ABIN BA HAKA BA NE, 'YAN TSIRARUN MUTANE NE KAWAI SUKE DA WANNAN RA'AYI.

*** ABIN DA YA HANA WA'DANDA SUKA YI WACCAR MAGANAR SU FAHIMCI ABIN DA ABUBAKAR (RA) YA FAHIMTA GAME DA UMAR (RA), SHI NE BANBANCIN FAHIMTA. SABODA ABU NE DA BABU NASSI A KAI, KOWA YANA DA DAMAN YA BAYYANA FAHIMTARSA. DUK DA CEWA; KOWA YA SAN CEWA; UMAR (RA) YA FI FALALA, AMMA SAI DAI YANA DA TSANANI, TO SHI ABUBAKAR (RA) YANA FAHIMTAR CEWA; TSANANINSA AKWAI MASLAHA A CIKI, MUSAMMAN A MATSAYI NA SHUGABA. AMMA SHI KUMA DA YA YI WACCAR MAGANAR, YANA FAHIMTAR CEWA; MAI TSANANI BAI DACE DA SHUGABANCI BA, KOMAI FALALARSA. AMMA BA YA INKARIN CEWA; UMAR (RA) YA FI KOWA FALALA A BAYAN ABUBAKAR (RA).

*** LALLAI RASHIN NA'DI DA ANNABI (SAW) YA YI BA YA HANA KHALIFOFINSA YIN NA'DIN. SABODA SHI ANA YI MASA WAHAYI, YA SAN ABIN DA BA SU SANI BA. SA'BANIN SU. KUMA YA CE; AYI RIK'O DA SUNNARSU. DON HAKA MATSAYINSU DA BANBANCI, DON HAKA TA YAYA ZA KA HA'DASU, BARE KA TAMBAYE NI WANDA YA FI A WAJENA??!
DON HAKA ABIN DA ANNABI (SAW) YA YI SUNNA CE, ABIN DA ABUBAKAR (RA) MA YA YI SUNNA CE. KUMA ASALIN SUNNAR ABUBAKAR (RA) SHI NE ISHARA DA ANNABI (SAW) YA YI ZUWA GA A ZA'BI ABUBAKAR (RA), SHI YA SA ABUBAKAR (RA) YA FAHIMCI SHUGABA ZAI IYA GABATAR DA WANDA YA FI SAURAN MUTANE FALALA DA ALHERI.

*** KA KAWO MAGANAR IBNU UMAR (RA), ALHALI INA GANIN MAGANAR ABDULLAHI 'DAN ABBAS (RA) CE, BA TA IBNU UMAR (RA) BA.
LALLAI WANNAR MAGANA BA TA KARO DA ABIN DA MUKE MAGANA A KANSA, SABODA WANNAR MAGANA AN YI TANE GA ABIN DA AKWAI NASSI K'ARARA A KAI DAGA MANZON ALLAH. AMMA ITA WANNAR MAGANA TA ZA'BEN KHALIFA BABU NASSI K'ARARA A KANTA. ANNABI (SAW) BAI AYYANA MANA WATA HANYA GUDA TILO DA ZA A BI WAJEN ZA'BEN SHUGABA BA, FACE GABATAR DA WANDA YA FI A CIKIN AL'UMMA. KUMA BAI YI HANI GA KHALIFA YA NA'DA WANDA YAKE GANIN YA FI CANCANTA BA.
WANNAR MAS'ALA DA MUKE MAGANA A KANTA, MAS'ALA CE TA MU'AMALA, IJTIHADI YANA IYA SHIGA CIKINTA, SA'BANIN MAS'ALAR IBADA, WANDA SAI AKWAI NASSI. ITA WACCAR MAGANA TA IBNU ABBAS (RA) A KAN MAS'ALA TA IBADA CE, BA TA MU'AMALA BA.
SA'ANNAN KUMA AI ANNABI (SAW) YA UMURCE MU DA MU YI RIK'O DA SUNNAR KHALIFOFINSA. DON HAKA AIKIN ABUBAKAR (RA) NA NA'DA UMAR (RA) A MATSAYIN KHALIFA A BAYANSA SUNNA CE DA ANNABI (SAW) YA YI UMURNI DA AYI RIK'O DA ITA, SABODA SUNNAR KHALIFANSA NE.

*** NA KAFA HUJJA NE DA LITTATAFANMU DON BAYANIN GASKIYA. SABODA BA A KAFA HUJJA DA K'ARYA A KAN GASKIYA. AMMA IN KA GA MUN KAWO MUKU MAGANA DAGA LITTAFINKU, MUN YI NE A BABAIN YI MUKU "ILZAMI", BA DON MUN YARDA DA SHI BA.

INA FATAN KA GAMSU.

No comments:

Post a Comment