Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Thursday, 25 February 2016

YAYE SHUBUHA A KAN ABUBAKAR (RA) (5)

(16) SHI'ATU YA CE:
KUMA HALA KA MANTA CEWA ABUBAKAR, UMAR BIN KHATTAB DA ABU UBAIDA IBN AL-JARRA DUK SUN KASANCE A QARQASHIN JAGORANCIN AMR BIN AL-AAS A LOKACIN YAKIN DHAT AS-SALASIL KUMA SUN DAUKI TSAWON LOKACI SUNA YIN SALLA A BAYANSA? KAGA A NAN MAI HANKALI ZAI GANE CEWA TUN DA SHUGABA YA GABATAR DA AMR BIN AAS AKAN WADANNAN MUTANE KUMA YAYI MASU LIMANCIN SALLA (AIKI MAFI MUHIMMANCI )NA TSAWON LOKACI, TO LALLAI, TANA ISHARA GA FIFIKON AMR AKANSU DA KUMA CANCANTARSA GA KHALIFANCI FIYE DA SU.

AMMAR:
LALLAI BABU GASKIYA A CIKIN WANNAN LABARI, SABODA MALAMAN TARIHI BA SU RUWAITO SHI DA ISNADI BA SAI AL- WAQIDIY, SHI KUMA MAK'ARYACI BA A KAR'BAN LABARINSA.
KA DUBA COMMENT 'DINA DA NA YI WA Bello Abubakar, WANDA YA KAWO LABARIN KASANCEWAR ABUBAKAR (RA) A CIKIN RUNDUNAR USAMA BN ZAID (RA).

(17) SHI'ATU YA CE:
GA RUWAYAR MUWATTA INDA ANNABI (S.A.W.A) YAQI YAYIWA ABUBAKAR SHAIDA A LOKACIN DA YAKE YIN SHAIDA WA SHAHIDAN UHUD, YANA MAI CEWA DASHI “BAN SAN ABINDA ZAKU AIKATA A BAYANA BA”:
وَحَدَّثَنِي عَنْ مَالِكٍ، عَنْ أَبِي النَّضْرِ، مَوْلَى عُمَرَ بْنِ عُبَيْدِ اللَّهِ أَنَّهُ بَلَغَهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ لِشُهَدَاءِ أُحُدٍ " هَؤُلاَءِ أَشْهَدُ عَلَيْهِمْ " . فَقَالَ أَبُو بَكْرٍ الصِّدِّيقُ أَلَسْنَا يَا رَسُولَ اللَّهِ بِإِخْوَانِهِمْ أَسْلَمْنَا كَمَا أَسْلَمُوا وَجَاهَدْنَا كَمَا جَاهَدُوا . فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم " بَلَى وَلَكِنْ لاَ أَدْرِي مَا تُحْدِثُونَ بَعْدِي " . فَبَكَى أَبُو بَكْرٍ ثُمَّ بَكَى ثُمَّ قَالَ أَئِنَّا لَكَائِنُونَ بَعْدَكَ

AMMAR:
WANNAN HADISIN MAI RAUNI NE, BAI TABBATA BA. SABODA ISNADINSA A YANKE YAKE, "MURSALI" NE. IBNU ABDIL BARR YA CE:
حديث رابع عشر لأبي النضر
مالك عن أبي النضر مولى عمر بن عبيد الله أنه بلغه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال لشهداء أحد "هؤلاء أشهد عليهم" فقال أبو بكر الصديق ألسنا يا رسول الله بإخوانهم أسلمنا كما أسلموا وجاهدنا كما جاهدوا فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم "بلى ولكن لا أدري ما تحدثون بعدي" قال فبكى أبو بكر وقال أئنا لكائنون بعدك.
هذا الحديث مرسل هكذا منقطع عند جميع الرواة للموطأ.

SABODA SHI IMAMU MALIK CEWA YA YI:
عَنْ أَبِي النَّضْرِ، مَوْلَى عُمَرَ بْنِ عُبَيْدِ اللَّهِ أَنَّهُ بَلَغَهُ

DA KA SAN ILMIN HADISI, DA KA SAN CEWA; WANNAN HADISIN YANA CIKIN "BALAGAATU MALIK". WA'DANDA BA SU INGANTA HAR SAI ISNADINSU YA SADU, KUMA MARUWAICIN YA ZAMA "THIQA". TO DA MA SHI AL- IMAM IBNU ABDIL BARR YA SADAR DA "BALAGAATU MALIK", A CIKIN LITTAFINSA "AL- TAMHID", AMMA SHI WANNAN HADISI BAI SAMU SADADDEN ISNADINSA BA, SHI YA SA YA CE MAKA:
هذا الحديث مرسل هكذا منقطع عند جميع الرواة للموطأ.
DON HAKA HADISIN MAI RAUNI NE, SABODA "MURSALI" NE, "MUNQA'DI'I".
DON HAKA BA KA DA HUJJA A CIKIN "MUWA'D'DA", SAI KA NEMO WANI.

*** MALAM SHI'ATU, YA KAMATA KA KULA DA WANI ABU GUDA; DUK TAMBAYOYIN DA NA YI MAKA, KO IN NA KORE WANI ABU DA KA KAWO, TO DOLE FA KA BA NI AMSOSHINSU. IN BA HAKA BA, BA ZA MU FITA DA NATIJA BA.

ALLAH YA SA MU DACE.

No comments:

Post a Comment