(12) SHI'ATU YA CE:
“BA MAI SON ALI SAI MUMINI KUMA BA MAI KIN ALI SAI MUNAFUKI”
AMMAR:
A LAL HAK'IK'A WANNAN GASKIYA NE, KAMAR YADDA "BABU MAI K'IN ANSAR SAI MUNAFUKI" KUMA BABU MAI K'IN ABU HURAIRA SAI MUNAFUKI. DUK MAI K'IN WA'DANNAN MUNAFUKI NE. AMMA SU WA'DANDA SUKA YAK'I ALIYU (RA) SHIN DON K'IYAYYA SUKA YAK'E SHI??!
KOWA YA SAN CEWA; BA K'IYAYYA BA CE TA SA SUKA YI YAK'I DA ALIYU (RA). BABU MAI FA'DIN HAKA SAI WANDA YA JAHILCI SABUBAN YAK'IN JAMAL DA SIFFIN.
(13) SHI'ATU YA CE:
“BA MAI SON ALI SAI MUMINI KUMA BA MAI KIN ALI SAI MUNAFUKI” YANA NUNI NE DA CEWA BA SANDA ZA’A SAMI ALI (A.S) BA AKAN TAFARKIN ALLAH BA, WANNAN KUWA SHINE MA’ANAR ISMA.
AMMAR:
HABA MALAM SHI'ATU, YANZU KA RASA NASSI GUDA A KAN "ISMA" SAI WANNAN HADISIN??!
TO IN KA FA'DI HAKA, SAI MU CE: ASHE DUKKAN AL'ANSAR MA MA'ASUMAI NE, SABODA ANNABI (SAW) YA CE:
الأنصار لا يحبهم إلا مؤمن ، ولا يبغضهم إلا منافق فمن أحبهم أحبه الله ، ومن أبغضهم أبغضه الله.
BUKHARI DA MUSLIM.
HAKA ABU HURAIRA (RA) MA, SHI DA MAHAIFIYARSA DUKA MA'ASUMAI NE, ABU HURAIRA (RA) YA CE:
قلت يا رسول الله ادع الله أن يحببني أنا وأمي إلى عباده المؤمنين ويحببهم إلينا - قال - فقال رسول الله -صلى الله عليه وسلم- « اللهم حبب عبيدك هذا - يعنى أبا هريرة وأمه - إلى عبادك المؤمنين وحبب إليهم المؤمنين ».
SAHIHU MUSLIM.
DON HAKA DUKKAN MAK'IYINSU MUNAFUKI NE, KUMA SU MA'ASUMAI NE – A BISA K'A'IDARKA-!!
(14) SHI'ATU YA CE:
HAKA KUMA CEWA: “FATIMA ZOKAN JIKI NANE, DUK WANDA YA BATA MATA YA BATA MINI” ALHALI ALLAH (SWT) YANA CEWA:
وَمَن يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَـلاً مُّبِيناً
AMMAR:
ANNABI (SAW) YA FA'DI WANNAN HADISIN NE A LOKACIN DA ALIYU (RA) YA YI NIYYAN AUREN 'YAR ABU JAHL:
عن الزهري ، قال : حدثني علي بن حسين أن المسور بن مخرمة قال إن عليا خطب بنت أبي جهل فسمعت بذلك فاطمة فأتت رسول الله صلى الله عليه وسلم فقالت يزعم قومك أنك لا تغضب لبناتك هذا علي ناكح بنت أبي جهل فقام رسول الله صلى الله عليه وسلم فسمعته حين تشهد يقول أما بعد أنكحت أبا العاص بن الربيع فحدثني وصدقني وإن فاطمة بضعة مني وإني أكره أن يسوءها والله لا تجتمع بنت رسول الله صلى الله عليه وسلم وبنت عدو الله عند رجل واحد فترك علي الخطبة.
BUKHARI DA MUSLIM.
DON HAKA ALIYU (RA) NE YA FARA 'BATA MA FATIMA (RA) RAI, DON HAKA SHI BA MA'ASUMI BA NE. DON DA SHI MA'ASUMI NE DA BABU YADDA ZA AYI YA SO NEMAN AUREN WATA MATA, ABIN DA ZAI 'BATA MA FATIMA (RA) TSOKAR ANNABI (SAW) RAI.
SA'ANNAN KUMA A CIKIN WANNAN HADISI BABU ABIN DA YAKE NUNA FATIMA (RA) MA'ASUMA CE, DON IN YA ZAMA HAKA, TO DOLE DUKKAN 'YA'YANSA SU ZAMA MA'ASUMAI, SU ZAINAB (RA), RUK'AYYA (RA), UMMU KULTHUM (RA).
DON HAKA, IN FATIMA (RA) MA'ASUMIYA CE, TO SAURAN 'YA'YAN ANNABI (SAW) MA'ASUMAI NE.
(15) SHI'ATU YA CE:
SHI’ATU: TUN DA JAGORANCIN SALLA NA NUNA CANCANTAR KHALIFANCI NE A WAJEN WAHABIYYAWA, TO MAI MUCE IBNU UMMI MAKTUM (RA) YAFI UTHMAN BIN AFFAN CAN-CANTA KENAN DOMIN LOKACIN DA IBNU UMMI MAKTUM (RA) YAYI JAGORANCIN NASA AI UTHMAN NA NAN A GARIN MADINA DOMIN BAI SAMU HALARTAR BADAR BA.
AMMAR:
AI IN KA SAN DALILIN DA YA SA USMAN (RA) BAI JE BADAR BA, BA ZA KA YI WANNAR MAGANAR BA!!
DALILIN DA YA SA BAI JE BADAR BA, SHI NE DALILIN DA YA SA BA A BA SHI LIMANCI A MADINA BA.
USMANU (RA) BAI HALARCI BADAR BA, SABODA RASHIN LAFIYAR MATARSA RUQAYYA (RA) 'YAR ANNABI (SAW), YA ZAUNA A GIDA YANA JINYARTA, WANNAN SHI NE DALILIN DA YASA AKA 'DAUKE MASA ZUWA YAK'IN BADAR, KUMA SHI YA SA ANNABI (SAW) BAI 'DORA MASA NAUYIN LIMANCI BA, DON YA SAMU DAMAR KULA DA MATARSA 'YAR ANNABI (SAW) MARAS LAFIYA.
No comments:
Post a Comment