Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Thursday, 25 February 2016

YAYE SHUBUHA A KAN ABUBAKAR (RA) (3)

(8) SHI'ATU YA CE:
ALLAH (SWT) YA KARE AL-QUR’ANI DAGA GURBATA NE TA DUKKAN HANYOYIN BIYU. TA HANYAR FARKO YA TSARE AL-QUR’ANI, TA YADDA BA WANDA ZAI IYA QARA KO CIRE KOMAI A CIKINSA:
إنا نحن نزلنا الذكر وإنا له لحافظون

AMMAR:
IN DA GASKE KA YARDA DA WANNAN, TO MENENE MATSAYINKA GAME DA WANNAR RUWAYAR:
عن جابر قال: سمعت أبا جعفر عليه السلام يقول: ما ادعى أحد من الناس أنه جمع القرآن كله كما أنزل إلا كذاب، وما جمعه وحفظه كما نزله الله تعالى إلا علي بن أبي طالب عليه السلام والأئمة من بعده عليهم السلام.

A CIKIN ALKAFIY NA KULAINIY??
GA SHI YA NUNA CEWA; BABU WANDA YA TARA AL- QUR'ANI SAI IMAMAN SHI'A GUDA 12 KAWAI??!
KUMA DU YA RUWAITO:
عن هشام بن سالم، عن أبي عبد الله عليه السلام قال: إن القرآن الذي جاء به جبرائيل عليه السلام إلى محمد صلى الله عليه وآله سبعة عشر ألف آية.

GA SHI YA NUNA CEWA; AL- QUR'ANI NA ASALI AYA 17,000 NE, ALHALI QUR'ANI A YAU AYA 6236 NE??!

(9) SHI'ATU YA CE:
WANNAN NE YASA MANZO (S.A.W.A) NA GAMA QADDAMAR DA WANNAN OFISHI A GHADEER KHUM SAI ALLAH (SWT) YA SAUKAR MASA DA AYAR KAMALAN ADDINI KAMAR HAKA:
اليوم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دينا

AMMAR:
MENENE DALILI A KAN CEWA; WANNAR AYAR A GHADEER TA SAUK'A??!

(10) SHI'ATU YA CE:
YA ZA’AYI AL’UMMAR DA BA’A YARDE MATA BA DA TA ZABAWA KANTA KWAMANDAN YAKI KADAI

AMMAR:
MENENE DALILI A KAN WANNAR MAGANA TAKA, CEWA; BA A YARDA MA AL'UMMA TA ZA'BI KWAMANDA BA??!
A LOKACIN DA ANNABI (SAW) YANA NAN SHI NE SHUGABA NA GABA 'DAYA, SHI NE MAI ZA'BAN KWAMANDAR YAK'I BA WANI BA. AMMA KHALIFANCI A BAYANSA BAI NASSANTA KOWA BA, SAI DAI YA YI ISHARA ZUWA GA SAYYIDINA ABUBAKAR (RA), DAGA CIKIN ISHARORIN; YA NA'DA SHI LIMANCI A LOKACIN RASHIN LAFIYANSA NA AJALI, KUMA YA YI NIYYAR YA RUBUTA WASIYYA GARE SHI A RUBUCE, AMMA SAI YA GA HAKAN BA DOLE BA NE, SABODA ISHARORO DA YA YI ZUWA GA ABUBAKAR (RA) 'DIN SUN WADATAR, KUMA SABODA YAK'INI DA YAKE DA SHI A KAN CEWA; ABUBAKAR (RA) NE ZAI ZAMA KHALIFA A BAYANSA, HAR YAKE CEWA:
ويأبى الله والمؤمنون إلا أبا بكر

"ALLAH DA MUMINAI ZA SU K'I KOWA (A MATSAYIN KHALIFA) SAI ABUBAKAR"
BUKHARI DA MUSLIM.

DON HAKA, IN KA CE; LALLAI ANNABI (SAW) YA NASSANTA KHALIFA, TO SAI MU CE MAKA: KAWO MANA NASSIN MU YI NAZARINSA??!

(11) SHI'ATU YA CE:
SHI’ATU: SUNE DAI MAKIYAN ALI KAMAR YADDA HADISIN ANNABI YA TABBATAR “BA MAI SON ALI SAI MUMINI KUMA BA MAI KIN ALI SAI MUNAFUKI” KA KO SAN MASOYI BAI YAKAN MASOYINSA.

AMMAR:
KA NUNA CEWA; WA'DANDA SUKA YAK'I ALIYU (RA), IRINSU MATAR ANNABI (SAW) A'ISHA (RA), DA 'DALHATU (RA) DA ZUBAIR (RA), DA MU'AWIYA (RA) DA SAURANSU MUNAFUKAI NE. SABODA KA CE:

" AKE GANE MU’MINI KO MUNAFUKI DA SO KO KIN ALI (A.S)"

A INA AKA SAMU WANNAR MAGANA, KUMA MENENE INGANCINTA, KAFIN KA YI HUKUNCI WA MATAR ANNABI (SAW) DA SAURANSU DA MUNAFURCI??!

No comments:

Post a Comment