Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Sunday, 7 February 2016

WUCE GONA - DA - IRI NA 'YAN SHI'A GWAGWARMAYA, DA GULUWWINSU A GIRMAMA JAGORANSU A NIGERIA

'YAN HARKA A NIGERIA SUNA K'OK'ARIN GUR'BATA SHI'ANCI, TA HANYAR K'IRK'IRE - K'IRK'IRE DA KUMA WUCE GONA DA IRI DA SUKE YI WAJEN GIRMAMA JAGORANSU ZAKZAKY MAZAUNIN GARIN ZARIA.

GA KA'DAN DAGA IRIN WANNAN SHISHSHIGI NASU KAMAR HAKA:

(1) GIRMAMA SHAKHSIYAR JAGORANSU ZAKZAKY ABIN DA BA ZA KA SAMU IRINSA A WAJEN MABIYA SAURAN KUNGIYOYIN GWAGWARMAYA NA DUNIYA BA.
(2) A TARURRUKAN NA MUNASABOBIN IMAMAN SHI'A MABIYA ZAKZAKY SUNA HA'DA SHI DA IMAMAI.
(3) KAMAR A NISFU SHA'ABAN SUNA AMBATON HAIFUWAR ZAKZAKY A TARE DA TA MAHDIN SHI'A, IN AN KARANTA TARIHIN MAHDI SAI A KARANTA NA ZAKZAKY.
(4) IN ANA INFAQI SUNA KAWO ASUSUN ANNABI (SAW), SAI A KAWO NA ALIYU (RA), SAI A KAWO NA FATIMA (RA), SAI KUMA A KAWO NA ZAKZAKY.
(5) A BIKIN ASHURA KUWA, SUNA CEWAR; HUSAINI (RA) DA SAHABBANSA SUN RIGA DA SUN SHU'DE, DON HAKA ZAKZAKY NE HUSAINI NA WANNAN ZAMANI.
(6) 'YAN HARKA SUNA YIN GORI MA IMAMAN SHI'A, SABODA SUNA RAYA CEWA; BABU WANDA YA KAI ZAKZAKY HIDIMA WA IMAMAI TUN FARKON DUNIYA HAR YAU.
(7) 'YAN SHI'AR HARKA SUN YI SHIRKA WA HUSAINI (RA), SABODA SUN K'IRK'IRI TATTAKI ZUWA ZARIA, ALHALI WANNAN ABU NE DA YA KE'BANTA DA HUSAINI (RA) KAWAI A TSARIN SHI'A.
(8) MABIYA ZAKZAKY SUN YI SHIRKA WA MA'ASUMAI IMAMAN SHI'A, SABODA A WAJENSU ZAKZAKY BA YA KUSKURE, YANA KAR'BAN UMURNI NE DAGA MAHDI.
(9) DUK CIKIN JAGORORIN SHI'A NA DUNIYA BABU WANDA AKE YI MASA IRIN WANNAN WUCE IYAKA KAMAR YADDA MABIYA ZAKZAKY SUKE YI MASA. BA AYI IRIN WANNAN GA KHOMAINY BA, BARE KUMA MAGAJINSA KHAMNA'I. HAKA KUMA BA AYI WA NASRULLATA BA.
(10) ABIN TSORON SHI NE; NAN GABA IN ZAKZAKY YA TUNKUYI K'ASA, KAR MABIYANSA SU BISNE SHI A CIKIN HUSAINIYYAR TASA, SU MAI DA WAJEN YA ZAMA WAJEN 'DAWAFI KAMAR YADDA AKE YI A KARBALA!!

KAI 'YAN SHI'A, INA HANKALUNKU SUKE NE??!

No comments:

Post a Comment