Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Sunday, 7 February 2016

KYAUTA GA MASU HANKALI DAGA CIKIN 'YAN SHI'A

LIMAMIN 'YAN SHI'A NA FARKO; SAYYIDINA ALIYU BN ABI 'DALIB (RA) YA WARWARE AQIDAR IMAMA DA WILAYA TA 'YAN SHI'A!!!

YA ZO A CIKIN BABBAN LITTAFIN 'YAN SHI'A MAI SUNA; "NAHJUL BALAGA":

6 - ( ومن كتاب له عليه السلام إلى معاوية )
إنه بايعني القوم الذين بايعوا أبا بكر وعمر وعثمان، على ما
بايعوهم عليه، فلم يكن للشاهد أن يختار ولا للغائب أن يرد، وإنما
الشورى للمهاجرين والانصار، فإن اجتمعوا على رجل وسموه إماما
كان ذلك لله رضى، فإن خرج من أمرهم خارج بطعن أو بدعة ردوه إلى
ما خرج منه، فإن أبى قاتلوه على اتباعه غير سبيل المؤمنين وولاه
الله ما تولى.
ولعمري يا معاوية لئن نظرت بعقلك دون هواك لتجدني أبرأ
الناس من دم عثمان، ولتعلمن أني كنت في عزلة عنه إلا ان تتجنى فتجن ما بدا لك. والسلام.

FASSARA:
6 - ( YANA DAGA CIKIN WASIK'UN DA ALIYU (RA) YA AIKA WA MU'AWIYA (RA):

"LALLAI MUTANEN DA SUKA YI MUBAYA'A WA ABUBAKAR DA UMAR DA USMAN SU NE SUKA YI MINI MUBAYA'A. KUMA SUN YI MINI MUBAYA'A NE A KAN IRIN ABIN DA SUKA YI MUSU MUBAYA'A. DON HAKA, WANDA YAKE NAN, BA SHI DA WANI ZA'BI. HAKA WANDA BA YA NAN, SHI MA BAI ISA YA YI K'I MIK'A WUYA BA. SABODA SHURA (ZA'BEN SHUGABA) YANA HANUN MUHAJIRUNA DA ANSAR NE. IN SUN YI ITTIFAQI A KAN MUTUM GUDA, SUKA ZA'BE SHI, SUKA KIRA SHI A MATSAYIN IMAMI (SHUGABA), HAKAN YA ZAMA ABIN YARDA A WAJEN ALLAH. SA'ANNAN, IDAN WANI YA YI TAWAYE GA LAMARINSU, YA SOKI ABIN DA SUKA ZARTAR, KO YA ZO DA WATA BIDI'A, SUKAN MAYAR DA SHI YA KOMA KAN ABIN DA YA YI TAWAYEN (ABIN DA SUKA ZARTAR). IN KUMA YA K'I, ZA SU YAK'E SHI, SABODA YA BI TAFARKI SA'BANIN TAFARKIN MUMINAI, KUMA ALLAH ZAI JI'BINTAR DA SHI ABIN DA YA JI'BINTA.
YA KAI MU'AWIYA, INA TABBATAR MAKA, IN KA YI TUNANI DA HANKALINKA, BA DA SON RANKA BA, ZA KA GA CEWA; NA FI KOWA BARRANTA DAGA JININ USMAN. KUMA LALLAI ZA KA SAN CEWA; LALLAI NA NISANCI WANNAN AIKA -AIKAN. SAI DAI IN ZA KA K'IN YIN AIKI DA HANKALINKA, TO SAI KA YI HAUKA IYA YADDA KAKE SO.
WASSALAM".

* AKWAI DARUSA MASU TARIN YAWA A CIKIN WANNAR WASIK'A TA LIMAMIN SHI'A, GA KA'DAN DAGA CIKI KAMAR HAKA:

(1) LIMAMIN SHI'A ALIYU (RA) YA YARDA DA KHALIFANCIN ABUBAKAR DA UMAR DA USMAN, KHALIFANCINSU KHALIFANCI NE NA SHARI'A KUMA INGANTACCE WANDA ALLAH YA YARDA DA SHI.

(2) SHURA (ZA'BEN SHUGABA) DA MUHAJIRUNA DA ANSAR SUKA YI, SHI NE HANYA MAFI INGANCI A SHARI'A WAJEN ZAMOWA IMAMI (SHUGABA, KHALIFA). KUMA ZA'BINSU SHI NE ZA'BIN ALLAH, SABODA ALLAH YA YARDA DA ZA'BINSU.

(3) SAYYIDINA ALIYU (RA) YA NUNA CEWA; YA ZAMA IMAMI NE DA ZA'BIN MUHAJIRUNA DA ANSAR BA DA NASSI BA.

(4) WANNAN - A FILI - YA RUSA AQIDAR "NASSI" A KAN IMAMANCI, WANDA 'YAN SHI'A SUKE RAYAWA, SUKE TA KUMFAR BAKI A KANSA.

(5) WANDA YA YI TAWAYE GA ZA'BIN MUHAJIRUNA DA ANSAR YA FITA DAGA HANYAR MUMINAI.

(6) SAYYIDINA ALIYU (RA) YA YARDA DA MATSAYIN SAHABBAI, YA SAN DARAJARSU. SU MUMINAI NE, - BA KAFIRAI BA, KAMAR YADDA 'YAN SHI'A SUKA YI IMANI - DUK WANDA YA K'I BIN TAFARKINSU, YA BI TAFARKI SA'BANIN TAFARKIN MUMINAI, A K'ARSHE ZAI ZAMA 'DAN WUTA.

(7) ALIYU (RA) YA K'ARYATA 'YAN SHI'A, MASU RAYA CEWA; AN YI MASA K'WACEN KHALIFANCI. SABODA ALIYU (RA) YA NUNA CEWA; ALLAH YA YARDA DA ZA'BIN DA SAHABBAI SUKA YI WA ABUBAKAR DA UMAR DA USMAN.

(8) ALIYU (RA) YA BAYYANA DALILIN DA YA SA MU'AWIYA (RA) YAKE YAK'I DA SHI, WATO SHI NE; NEMAN A 'DAUKI FANSA A KAN JININ KHALIFAN USMANU (RA). DON HAKA BA TSANTSAR SON KHALIFANCI BA NE YA SA HAKA YA FARU, KAMAR YADDA 'YAN SHI'A SUKE ZATO.

** WA'DANNAN SU NE KA'DAN DAGA DARUSSA DA WANNAR WASIK'A TA ALIYU (RA) TA K'UNSA.

KAI MA, IN KA K'ARA LURA DA KYAU, ZA KA IYA FITAR DA WASU DARUSAN, TA YIWU MA SU FI WA'DANDA NA FITAR, SU FI SU YAWA, SU FI SU K'ARFIN HUJJA WAJEN WANCAKALAR DA AQIDAR IMAMA DA WILAYA TA 'YAN SHI'A.

*** 'YAN SHI'A, INA HANKULANKU SUKE NE??!

*** IN KA KARANTA WANNAN, AMMA BA KA FITA DAGA SHI'A BA, TO KA TUHUMI HANKALINKA!!!

*** GARGA'DI:
DA MASU HANKALI KAWAI NAKE MAGANA BA DA....!!

No comments:

Post a Comment