Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Thursday, 25 February 2016

SHIN AKWAI HUJJA A KAN AQIDAR IMAMA A CIKIN HADISIN MANZILA?


ANNABI (SAW) YA CE MA ALIYU (RA):
"أنت مني بمنزلة هارون من موسى إلا أنه لا نبي بعدي"

"KAI MATSAYINKA GARENI A MATSAYIN HARUNA NE GA ANNABI MUSA, SAI DAI BABU ANNABI A BAYANA"

ABUBUWAN LURA A WANNAN HADISI SU NE KAMAR HAKA:

1. KOWA YA SAN CEWA; MATSAYIN ANNABI HARUNA (AS) GA ANNABI MUSA (AS) SHI NE KASANCEWARSA 'DAN UWA, KAMAR YADDA ALIYU (RA) YAKE 'DAN UWA GA ANNABI (SAW). SA'ANNAN KUMA ANNABI (SAW) YA WAKILTA ALIYU (RA) A MADINA A LOKACIN DA YA TAFI YAK'IN TABUKA, KAMAR YADDA ANNABI MUSA (AS) YA WAKILTA ANNABI HARUNA (AS) A CIKIN MUTANENSA A LOKACIN DA YA TAFI MUNAJATI DA ALLAH. WANNAN SHI NE MATSAYIN DA ANNABI (SAW) YAKE NUFI GA ALIYU GAME DA SHI, KAMAR YADDA MATSAYIN HARUNA YAKE GAME DA ANNABI MUSA (AS).
ABIN TAMBAYA A NAN SHI NE; TA YAYA WANNAN HADISI ZAI YI NUNI A KAN IMAMANCIN ALIYU (RA) BAYAN RASUWAR ANNABI (SAW) BAYAN KOWA YA SAN CEWA; HARUNA (AS) YA RASU NE KAFIN ANNABI MUSA (AS)??

2. SA'ANNAN KOWA YA SAN CEWA; HARUNA BAI ZAMA KHALIFAN ANNABI MUSA (AS) BA A BAYAN RASUWARSA, YUSHA'U NE YA ZAMA KHALIFA A BAYANSA.
SHIN DA ANNABI (SAW) KHALIFANCI YAKE NUFI DA WANNAN HADISI, ME YA HANA YA KAMANTA SHI DA YUSHA'U, SABODA SHI NE KHALIFA A BAYAN ANNABI MUSA (AS) BA HARUNA (AS) BA??

3. KOWA YA SAN CEWA; ANNABI (SAW) YA WAKILTA WASU DAGA CIKIN SAHABBANSA A MADINA A SAURAN YAK'UK'UWANSA, KAMAR SU IBNU UMMI MAKTUM (RA), DA MUHAMMAD BN MASLAMA (RA) DA KHAFAF BN EIMA'I AL- GHIFARIY, DA SAURANSU.
TO SHIN HAKAN BA YA NUNA CANCANTARSU GA KHALIFANCI A BAYAN ANNABI (SAW) KAMAR YADDA IN WANNAN HADISIN YA NUNA CANCANTAR ALI (RA) GA KHALIFANCI??

4. IN AN CE; TUN DA ANNABI (SAW) YA WAKILTA ALIYU (RA) A MADINA A YAK'IN TABUKA, DON HAKA SHI YA FI KOWA FALALA, DON HAKA SHI NE KHALIFA.
TO SHIN SAURAN SAHABBAI DA ANNABI (SAW) YA WAKILTASU A MADINA A SAURAN YAK'UK'UWANSA DA TAFIYE - TAFIYENSA BA ZA SU ZAMA SUN FI ALIYU (RA) FALALA BA A MAFI YAWAN LOKUTAN YAK'UK'UWANSA DA TAFIYE - TAFIYENSA, DON HAKA SAI SU ZAMA SUN FI SHI CANCANTAR KHALIFANCI??

5. SA'ANNAN SAURAN WAKILAN ANNABI (SAW) A MADINA SUNA WAKILTANSA NE A KAN MUMINAN MAZA DA MATA, AMMA SHI ALIYU (RA) YA WAKILCE SHI NE A KAN YARA DA MATA DA MASU UZURI DA MUTUM 3 DA AKA KAR'BI TUBANSU.
TO SHIN WANNAN BA ZAI NUNA CEWA; SAURAN WAKILAN ANNABI (SAW) SUN FI ALIYU (RA) FALALA BA, SABODA WA'DANDA AKA WAKILTASU A KANSU SUN FI WA'DANDA AKA WAKILTA ALIYU (RA) A KANSU??

*** SAHABBAN DA ANNABI (SAW) YA WAKILTASU A MADINA A LOKACIN TAFIYE - TAFIYENSA:
1. SA'AD BN UBADAH (RA).
2. SA'AD BN MU'AZ (RA).
3. ZAIDU BN HARITHA (RA).
4. ABU SALAMA BN ABDIL ASHHAL (RA).
5. IBNU UMMI MAKTUUM (RA) SAU 11.
6. ABU LUBABA (RA).
7. USMAN BN AFFAN (RA).
8. ABDULLAHI BN RAWAHA (RA).
9. SUBA'U BN ARFA'DA (RA).
10. ABU RAHM (RA).
11. MUHAMMAD BN MASLAMA (RA).
12. KHAFAF BN EIMA'I AL- GHIFARIY (RA).
13. ALIYU BN ABI 'DALIB (RA).

INA KIRA GA MASU HANKALI A CIKIN 'YAN SHI'A DA SU TAYA NI NAZARIN WANNAN HADISIN, DA FATAN ZA MU ISA ZUWA GA HAK'IK'ANIN LAMARIN.

ALLAH YA SA MU DACE.

No comments:

Post a Comment