Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Thursday, 25 February 2016

INA NEMAN GAMSASSHIYAR AMSA (1)


MAI LITTAFIN "NAHJUL BALAGA" - LITTAFI NE ABIN DOGORO A WAJEN 'YAN SHI'A - YA RUWAITO CEWA; ALIYU (RA) YA NEMI A YAFE MASA HAWA KHALIFANCI, YA CE:
"دعوني والتمسوا غيري"
"NI KAM KU K'YALE NI, KU NEMI WANI"

LALLAI WANNAN YANA NUNA RUSHEWAR MAZHABAR SHI'A. SABODA TA YAYA ALIYU (RA) ZAI NEMI A YAFE MASA HAWA KHALIFANCI, ALHALI A WAJEN 'YAN SHI'A, NA'DA SHI A MATSAYIN KHALIFA ABU NE DA YAKE FARILLA NA LAZIMI DAGA ALLAH, WANDA HAR 'YAN SHI'A SUNA RAYA CEWA; YA NEMI WANNAN MATSAYI NASA A WAJEN ABUBAKAR (RA)??!

*** NI FA ABUN YA 'DAURE MINI KAI, A TAIMAKA MINI DA GAMSASSHIYAR AMSA!!!

No comments:

Post a Comment