Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Saturday, 6 February 2016

RAFIDHA ('YAN SHI'A) YAHUDAWA SUKE BI WAJEN NAQASA ALLAH DA AIBANTA SHI


RAFIDA ('Yan Shi'a) sun bi safun Iyayensu YAHUDAWA wajen NAQASA Allah (SWT) da AIBANTA shi, ta hanyar jingina masa BADA'I, wanda hakikaninsa shi ne; Siffanta shi da JAHILCI. Kamar haka YAHUDAWA suka siffanta shi da NADAMA, da MANTUWA. Don haka RAFIDA da YAHUDAWA sun yi tarayya a cikin SIFFANTA Allah da JAHILCI, (SUBHANALLAH). Aqidar RAFIDA ta BADA'I asalinta BAYAHUDIYAR AQIDA ce.

RAFIDA sun yi kama da YAHUDAWA a cikin AQIDAR SIFFANTA ALLAH DA JAHILCI (Subhanallah), ta fiskoki kamar haka:
1 - RAFIDA suna siffanta Allah da BADA'I, YAHUDAWA kuma suna siffanta shi da NADAMA, MANTUWA da BAKIN CIKI. Duka wadannan Siffofi karshensu sh
i ne, JAHILTAR LAMARI tun FARKO.
2 - Kamanni tsakanin Nassoshin da ke cikin littatafan RAFIDA da YAHUDAWA game da wannar muguwar AQIDA, abin da yake tabbatar da cewa, AQIDAR RAFIDA ta BADA'I sun daukota ne kai - tsaye daga littatafan YAHUDAWA. Ga MISALAI kamar haka:
* YAHUDAWA suka ce, - WAI - Allah yayi nufin halakar da BANI ISRA'ILA, har MALA'IKA zai halakasu sai Allah yayi NADAMA, sai ya umurci MALA'IKAN da ya bari. Kamar haka RAFIDA ma suka ce, - WAI - Allah yayi nufin halaka mutane a zamanin Manzon Allah (SAW), sai Allah yayi BADA'I (ma'ana, sai sabon RA'AYI ya bayyana masa) sai ya fasa halakasun.
* YAHUDAWA suka ce: - WAI - Annabi Musa (SAW) ya nemi Allah ya fasa halaka BANI ISRA'ILA, sai ya fasan. Kamar haka RAFIDA suka ce, - WAI - Ja'afarus Sadiq ya nemi Allah ya fasa mutuwar dansa Isma'il, sai ya jinkirta masa har sau 2.
* YAHUDAWA suna fadin WAI, Allah ya ba da mulkin BANI ISRA'ILA ma SHA'UL, sa'annan sai yayi NADAMA YA JI HAUSHI. Kamar haka RAFIDA ma suke fadi, - WAI - Allah ya nada Isma'il dan Ja'afar da Muh'd dan Aliyu (Baban Ja'afar) a matsayin Imamai, sai sabanin hakan ya bayyana ma Allah sai ya canzasu.
* YAHUDAWA suna fadin, - WAI - Siffar NADAMA ba za ta rabu da Allah ba, har abada zai yana nadama akan abu na sharri. Kamar haka RAFIDA suka ce, - WAI - Allah ya SHARDANTA ma kansa BADA'I, zai gabatar da abin da yake so ya jinkirta abin da ya so.
* YAHUDAWA suna ganin siffanta Allah da NADAMA yabo ne gare shi, da kuma girmama shi. Kamar haka RAFIDA ma suka dauki BADA'I, - WAI HAKAN - Girmama Allah ne, da yabonsa.
3 - Karshen ma'anar BADA'IN RAFIDA, da BAKIN CIKI da NADAMAN na wajen YAHUDAWA, shi ne SIFFANTA ALLAH DA JAHILCI, da rashi sanin abin da yafi zamowa maslaha kafin faruwan abu..
سبحان الله وتعالى عما يقول الظالمون علوا كبيرا




Ga irin ruwayoyin RAFIDA da suke dauke da Aibanta Allah (SWT), ana karya wa bayin Allah Ahlul Baiti:
An ruwaito daga Abu Ja'afar da Abu Abdillahi, sun ce:
"إن الناس لما كذبوا برسول الله - صلى الله عليه وسلم - هم الله تبارك وتعالى بهلاك أهل الأرض إلا عل
يا فما سواه بقوله: {فتول عنهم فما أنت بملوم} ، ثم بدا له فرحم المؤمنين ثم قال لنبيه: {وذكر فإن الذكرى تنفع المؤمنين}
DUBA ALKAFIY na KULAINIY, 8/ 103.

An ruwaito daga Ja'afarus Sadiq yace:
"ما بدا لله في شيء كما بدا له في إسماعيل ابني"
DUBA KAMALUD DEEN na AL- SADUQ pg 69, da AL'ANWARUN NU'UMANIYYA na AL- JAZA'IRIY, 1/ 359.

Assaduq yayi bayanin wannar ruwaya yace:
''أما قوله "ما بدا لله في شيء كما بدا له في إسماعيل ابني"، فإنه يقول: ما ظهر لله أمر كما ظهر له في إسماعيل ابني إذ اخترمه في حياتي''
DUBA KAMALUD DEEN na AL- SADUQ pg 69.

An ruwaito daga Ja'afar yana fadi game da mutuwar dansa Isma'il:
''كان القتل قد كتب على إسماعيل مرتين فسألت لله في دفعه فدفعه''
DUBA TASHIHUL I'ITIQADI na AL- MUFEED pg 51.

An ruwaito daga Abu Hashim Al- Ja'afariy yace:
''كنت عند أبي الحسن عليه السلام بعد ما مضى ابنه أبو جعفر وإني لأفكر في نفسي أريد أن أقول: كأنهما أعني أبا جعفر وأبا محمد في هذا الوقت كأبي الحسن موسى وإسماعيل ابني جعفر ابن محمد عليهم السلام وإن قصتهما كقصتهما، إذ كان أبو محمد المرجي بعد أبي جعفر عليه السلام فأقبل علي أبو الحسن قبل أن انطلق فقال: نعم يا أبا هاشم بدا لله في أبي محمد بعد أبي جعفر عليه السلام ما لم يكن يعرف له كما بدا له في موسى بعد مضي إسماعيل ما كشف به عن حاله، وهو كما حدثتك نفسك وإن كره المبطلون، وأبو محمد ابن الخلف من بعدي، عنده علم ما يحتاج إليه ومعه آلة الإمامة''
DUBA ALKAFIY na KULAINIY, 1/ 327.

Dusi ya ruwaito daga Usman Annawa yace:
''سمعت أبا عبد الله عليه السلام يقول: كان هذا الأمر في فأخره الله ويفعل بعد في ذريتي ما يشاء''.
DUBA AL- GAIBAH na DUSIY, pg 263, da BIHARUL ANWAAR 52/ 106.

Dusiy yayi ta'aliqi akan ruwayoyin yace:
"فالوجه في هذه الأخبار أن نقول - إن صحت - أنه لا يمتنع أن يكون الله تعالى قد وقت هذا الأمر في الأوقات التي ذكرت، واقتضت تأخيره إلى وقت آخر، وكذلك فيما بعد، ويكون الوقت الأول وكل وقت يجوز أن يؤخر مشروطا بأن لا يتجدد ما يقتضي المصلحة تأخيره، إلى أن يجيء الوقت الذي لا يغيره شيء فيكون محتوما''
DUBA AL- GAIBAH na DUSIY, pg 263
Jama'a kun ga yadda ake sharara karya wa Ahlul Baiti, ana Aibanta Allah (SWT).
سبحانك هذا بهتان عظيم!

No comments:

Post a Comment