Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Saturday, 6 February 2016

RAFIDHA ('YAN SHI'A) YAHUDAWA SUKA BI A AQIDARSU TA RAJA'A


RAFIDA ('Yan Shi'a) sun yi IMANI da RAJA'AH, ma'ana; dawowar wasu matattu zuwa rayuwar Duniya kafin tashin Qiyama. Lallai wannar Aqida sun gajeta ne a wajen YAHUDAWA, ta hanyar Bayahuden nan Abdullahi Dan Saba'i. Don haka AQIDAR RAFIDA ta RAJA'AH (dawowar matattu duniya) asalinta AQIDAR YAHUDAWA ce.

Bayahude Abdullahi Dan Saba'i, shi ne farkon wanda ya kawo ma RAFIDA AQIDAR RAJA'AH. Ga abin da yake fadi game da dawowar Aliyu (RA) bayan an kashe shi:
قال النوبختي: "ولما بلغ عبد الله بن سبأ نعي علي بالمدائن قال للذي نعاه: كذبت لو جئتنا بدماغه في سبع
ين صرة وأقمت على قتله سبعين عدلا لعلمنا أنه لم يمت ولم يقتل ولا يموت حتى يملك الأرض"
Ma'ana: AL- NAUBAKHTIY (malamin RAFIDA ne) ya ce: ''A lokacin da sanarwar mutuwan Aliyu ya iso ga Abdullahi dan Saba'i a garin Madaa'in, sai ya ce ma wanda ya sanar da shi labarin mutuwar: Karya kake yi, da zaka zo mana da kwakwalwarsa a cikin mazubi 70, kuma ka kawo mana shaidu 70, to mun san cewa lallai bai mutu ba, kuma ba a kashe shi ba, kai ba zai mutu ba har sai ya mulki duniya''
Duba FIRAQUSH SHI'A shafi na 23.


RAFIDA sun yi kama da YAHUDAWA a cikin Aqidar RAJA'AH, ta fiskoki kamar haka:
1 - RAFIDA sun yi ITTIFAQI da YAHUDAWA akan lokacin BABBAR RAJA'AH, in da RAFIDA suke cewa; zai kasance ne a lokacin fitowar MAHDINSU da suke JIRA. Kamar haka YAHUDAWA ma suk
a ce; tayar da mamatan zai kasance ne a lokacin fitowar ALMASIIHUNSU da suke JIRA.
2 - RAFIDA sun yi ITTIFAQI da YAHUDAWA akan manufar wannar RAJA'AR, in da manufarta a wajen RAFIDA ita ce; ta da matattu daga cikin RAFIDA su hadu da sojojin MAHDINSU, don taimakonsa akan makiyansa. Haka YAHUDAWA ma, manufar ita ce; ta da YAHUDAWA daga kabarurrukansu don taimakon ALMASIIHUN da suke JIRA.
3 - Dukkan bangaren RAFIDA da YAHUDAWA - a cikin wannar Aqida ta RAJA'AH - sun yi Imani da cewa; mutum MAKHLUUQI yana da IKON RAYAR da MATACCE.
SUBHANALLAH!!!


Wasu RAFIDA suka ce: Wannar AQIDAR RAJA'A ta RAFIDA, - WAI - akwai ta a AL- QUR'ANI. To ga maganganun malamansu akan wannar AQIDA, sai mu ga a wane QUR'ANIN a ka fadeta??
Ibrahim Al- Musawiy ya ce:
"الرجعة عبارة عن حشر قوم عند قيام القائم الحجة بن الح
سن عليه السلام ممن تقدم موتهم من أوليائه وشيعته ليفوزوا بثواب نصرته ومعونته ويبتهجوا بظهور دولته، وقوم من أعدائه ينتقم منهم وينالون بعض ما يستحقونه من العذاب والقتل على أيدي شيعته، وليبتلوا بالذل والخزي بما يشاهدونه من علو كلمته، وهي عندنا الإمامية الاثنا عشرية تختص بمن محض الإيمان ومحض الكفر والباقون سكوت عنهم"
Duba AQA'IDUL IMAMIYYATIL ITHNAI ASHARIYYAH, 2/228, na IBRAHIM AL- MUSAWIY.

Muh'd Rida Al- Muzaffar ya ce:
"عقيدتنا في الرجعة, أن الله تعالى يعيد قوما من الأموات إلى الدنيا في صورهم التي كانوا عليها فيعز فريقا ويذل فريقا آخر، ويديل المحقين من المبطلين والمظلومين منهم من الظالمين، وذلك عند قيام مهدي آل محمد عليه وعليهم أفضل الصلاة والسلام، ولا يرجع إلا من علت درجته في الإيمان، أو من بلغ الغاية من الفساد، ثم يصيرون بعد ذلك إلى الموت"
Duba AQA'IDUL IMAMIYYAH, 118 na AL- MUZAFFAR.

RAFIDA ('Yan Shi'a) ku gaya mana a wane QUR'ANIN aka fadi irin wannar AQIDA?????????!!!!!!!
ALLAH YA MANA TSARI DA BATA!!!


No comments:

Post a Comment