RAFIDA ('Yan Shi'a) suna jiran bayyanar Imaminsu na 12, sun ce, - wai - shi ne MAHDI, zai bayyana a karshen zamani don ya taimakesu, kuma zai dauko musu fansa daga makiyansu. Kamar haka Yahudawa ma suna jiran bayyanar wani mutum daga zuriyyar Dawuda, zai mulki duniya, zai dawo ma Yahudawa matsayinsu, kuma zai mai da sauran mutane bayi masu yi musu hidima. Don haka Aqidar Mahdin RAFIDA ta yi kama da Aqidar Yahudawa.
RAFIDA sun yi kama da Yahudawa a cikin Aqidar Mahdinsu, ta fiskoki kamar haka:
1 - Idan Mahdin RAFIDA ya bayyana dukkan RAFIDA ('Yan Shi'a) za su hadu a gari mafi tsarki a wajensu, wato KUUFA. Kamar haka Yahudawa ma idan Almasiihun da suke jira ya bayyana, dukkan Yahudawa zasu taru a gari mafi tsarki a wajensu, wato QUDUS.
2 - Idan Mahdin RAFIDA ya bayyana zai rayar da RAFIDAN da suka mutu don su shiga cikin rundunarsa. Kamar haka Yahudawa ma suka ce Almasiihunsu idan ya bayyana zai rayar da Yahudawan da suka mutu don su shiga cikin sojojinsa.
3 - RAFIDA suka ce idan Mahdinsu ya bayyana zai fitar da Sahabban Manzon Allah (SAW) daga kabarurrukansu don ya yi musu azaba. Kamar haka Yahudawa ma suka fada, Almasiihunsu zai fitar da gawarwakin masu sabo don Yahudawa su ga azabtar dasu.
4 - Mahdin RAFIDA zai yi hukunta duk wanda ya zalumcesu, kuma ya rama musu. Kamar haka Yahudawa ma suka ce, Almasiihunsu zai hukunta duk wanda ya zalumcesu ya kuma rama musu.
5 - Mahdin RAFIDA zai kashe 2 bisa 3 na mutanen duniya. Yahudawa ma haka suka ce Almasiihunsu zai yi.
6 - Idan Mahdin RAFIDA ya bayyana halittansu zai sanja, mutum 1 zai zama yana da karfin mutum 40, zai rinka taka mutane da kafarsa, kuma - wai - Allah zai tsawaita musu jinsu da ganinsu. Yahudawa kuma suka ce, in Almasiihunsu ya bayyana jikinsu zai canja, tsayin daya daga cikinsu zai kai zira'i 200, kuma za a tsawaita musu rayuwarsu.
7 - A zamanin Mahdin RAFIDA alkhairai zasu yi yawa, har za a samu rafuka guda 2, za su bubbugo daga KUUFA, daya na ruwa, daya kuma na nono, RAFIDA ne kawai zasu sha daga garesu. Kamar haka Yahudawa ma suka ce, a zamanin Almasiihunsu arziki zai yawaita, duwatsu za suna bubbugar da nono da zuma, kasa kuma za tana fitar da fanke da riguna na SUUFI.
8 - Mahdin RAFIDA babu shi, (babu hakikaninsa). haka ma Almasiihun Yawudawa babu shi.
Ina masu hankali, ku LURA!!
Ga wasu dalilai da suke nuna cewa, Mahdin RAFIDA ('Yan Shi'a) yana da alaqa da Yahudawa, kamar yadda ya zo a cikin littatafansu, suka
ce:
1 - Idan Mahdinsu ya bayyana zai kira ALLAh da sunansa na IBRANIYYANCI (yare ne na Yahudawa)
2 - Zai nemi cin nasarar kama garuruwa da Akwatin Yahudawa, kuma zai fitar da sandar Annabi Musa (AS), da sa'i 10 na ALMANNU, da kadan daga tsuntsayen SALWA. Kamar yadda zai fitar da dutsen Musa (AS) wanda ya bubbugar da idanuwar ruwa guda 12.
3 - Kuma zai yi hukunci ne da hukuncin zuriyyar Dawuda (AS).
Jama'a, Ina masu hankali daga cikin 'Yan Shi'a?? Ya kamata kuyi nazarin abin da muke kawowa da idon basira, ku karanta littatafan malamanku, zaku ga irin Yahudancin da Abdullahi dan Saba'i ya shuka a cikin RAFIDANCI, har RAFIDANCIN ya zama Photo Copy ne na Yahudanci.
No comments:
Post a Comment