Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Saturday, 6 February 2016

RAFIDHA ('YAN SHI'A) YAHUDAWA SUKA BI A AQIDARSU TA CANZA QUR'ANI

RAFIDA 'YAN SHI'A SUN YI KAMA DA YAHUDAWA TA WAJEN CANZA LITTAFIN ALLAH. A LOKACIN DA YAHUDAWA SUKA CANZA ATTAURA DA SAURAN LITTATAFANSU, RAFIDA 'YAN SHI'A MA SUN CANZA AL- QUR'ANI, DA NUFIN CANZA ADDININ DA MANZON ALLAH (SAW) YA ZO DA SHI.

RAFIDA sun yi kama da YAHUDAWA a cikin AQIDAR CANZA LITTAFIN ALLAH, TA FISKOKI KAMAR HAKA:
1 - ALLAH YA ZARGI YAHUDAWA DA CANZA MAGANAR ALLAH, KUMA YANA DAGA CIKIN CANZA MAGANAR ALLAH FASSARATA DA SABANIN ABIN DA AKA SAUKAR DA AYAR AKANSA.
KAMAR HAKA 
RAFIDA 'YAN SHI'A MA SUKA YI WA AYOYIN QUR'ANI.
ALI BIN IBRAHIMUL QUMMIY YA CE:
وقرأ أبو عبد الله عليه السلام " هذه جهنم التي كنتما بها تكذبان تصليانها ولا تموتان فيها ولا تحييان " يعني زريقا وحبتر
MA'ANA; ABU ABDILLAHI (AS) YA KARANTA AYAR DA HAKA, WAI YANA NUFIN AYAR TANA MAGANA NE AKAN ZURAIQU DA HABTAR.
DUBA TAFSIRIN AL- QUMMIY 2/ 345.
KULAINIY YA RUWAITO DAGA ABU ABDILLAHI YA CE:
عن أبي عبد الله عليه السلام في قول الله عزوجل: " إنا عرضنا الامانة على السماوات والارض والجبال فأبين أن يحملنها وأشفقن منها وحملها الانسان إنه كان ظلوما جهولا " قال: هي ولاية أمير المؤمنين عليه السلام.
MA'ANA; AMANAR DA ALLAH YA DORA WA MUTANE, ITA CE; SHUGABANCIN ALIYU (RA).
DUBA AL- KAFIY 1/ 413.
KULAINIY YA RUWAITO DAGA BABAN HAMZA:
قال: سألت أبا جعفر عليه السلام عن قول الله تعالى: " قل إنما أعظكم بواحدة" فقال: إنما أعظكم بولاية علي عليه السلام هي الواحدة التي قال الله تبارك وتعالى " إنما أعظكم بواحدة ".
MA'ANA; WAI ''WAHIDAH'' DA ALLAH YA AMBATA A CIKIN AYAR, ITA CE WILAYAR ALIYU (RA).
DUBA ALKAFIY 1/ 420.
KULAINIY YA RUWAITO DAGA MUSA DAN JA'AFAR YA CE:
في قوله تعالى: " وبئر معطلة وقصر مشيد " قال: البئر المعطلة الامام الصامت والقصر المشيد الامام الناطق.
WAI MA'ANAR AYAR, SHI NE; IMAMI MARAS MAGANA DA IMAMI MAI MAGANA.
DUBA AL- KAFIY 1/ 427.

2 - ALLAH YA ZARGI YAHUDAWA AKAN CANZA LAFAZIN LITTATAFANSU. KAMAR HAKA RAFIDA 'YAN SHI'A SUKA CANZA LAFAZIN AL- QUR'NI, GA MISALAI KAMAR HAKA:
ALI BIN IBRAHIMUL QUMMIY YA CE:
وقوله " ولقد نصركم الله ببدر وانتم أذلة " قال أبو عبد الله عليه السلام ما كانوا اذلة وفيهم رسول الله صلى الله عليه وآله وإنما نزل " لقد نصركم ببدر وانتم ضعفاء ".
MA'ANA; A CIKIN AYAR ALLAH YA CE: ''AZILLAH'', SU KUMA SUN CE; BA HAKA BA NE, WAI YADDA TA SAUKA; ''DU'AFA'U'' NE.
DUBA TAFSIRIN AL- QUMMIY 1/ 122.
AL- QUMMIY YA CE:
عن ابي عبد الله عليه السلام في قوله (يا ايها النبي جاهد الكفار والمنافقين) قال هكذا نزلت فجاهد رسول الله صلى الله عليه وآله الكفار وجاهد علي عليه السلام المنافقين فجاهد على عليه السلام جهاد رسول الله صلى الله عليه وآله.
KA DUBA YADDA YA CANZA AYAR!!
DUBA TAFSIRUL QUMMIY 2/ 377.
KULAINIY YA RUWAITO DAGA BABAN JA'AFAR:
قال: نزل جبرئيل عليه السلام بهذه الآية هكذا: " إن الذين ظلموا (آل محمد حقهم) لم يكن الله ليغفر لهم ولا ليهديهم طريقا إلا طريق جهنم خالدين فيها ابدا وكان ذلك على الله يسيرا.
ثم قال: " يا أيها الناس قد جاء كم الرسول بالحق من ربكم (في ولاية علي) فآمنوا خيرا لكم وإن تكفروا (بولاية علي) فإن لله ما في السماوات وما في الارض ".
KUMA YA RUWAITO DAGA BABAN JA'AFAR:
قال هكذا نزلت هذه الآية " ولو أنهم فعلوا ما يوعظون به (في علي) لكان خيرا لهم".
KUMA DU YA RUWAITO DAGA BABA JA'AFAR:
قال:نزل جبرئيل بهذه الآية هكذا: " فأبى أكثر الناس (بولاية علي) إلا كفورا" قال: ونزل جبرئيل عليه السلام بهذه الآية هكذا: " وقل الحق من ربكم (في ولاية علي) فمن شاء فليؤمن ومن شاء فليكفر إنا أعتدنا للظالمين (آل محمد) نارا".
DUBA AL- KAFIY NA KULAINIY 1/ 424 - 425.
JAMA'A KU DUBA IRIN WANNAN WASA DA AL- QUR'ANIN DA RAFIDA 'YAN SHI'A SUKE YI??????!!!!!!
AMMA WALLAHI SUN MAKARA, ALLAH YA CE:
'' إنا نحن نزلنا الذكر وإنا له لحافظون''
KUMA AI KIFI YANA GANINKA MAI JAR KOMA!!!!!!!
ALLAH YA SHIRYI RAFIDA 'YAN SHI'A, SU FAHIMCI CEWA ANA JAN SU NE ZUWA GA YAHUDANCI!!


GA WASU MAGANGANUN MANYAN MALAM RAFIDA 'YAN SHI'A DAGA LITTATAFANSU, SUNA TABBATAR DA AQIDARSU TA CANZA AL- QUR'ANI, WANDA HAKAN KARYATA ALLAH NE (SUBHANALLAH):

1 - ALMUFEED YA CE:

إن الاخبار جاءت مستفيضة عن ائمة الهدى من آل محمد صلى الله عليه وآله وسلم باختلاف القرآن وما احدثه بعض الظالمين فيه من الحذف والنقصان.

WAI RUWAYOYI MASU YAWA SUN ZO DAGA IMAMANSU DA TABBACIN SABANI A CIKIN QUR'ANI, DA ABIN DA WASU AZZALUMAI SUKA YI A CIKINSA NA SHAFE WASU AYOYI DA RAGE WASU .
DUBA AWA'ILUL MAQALAAT pg 91.

* JAMA'A WALLAHI KARYA SUKE YI WA IYALEN MANZON ALLAH (SAW), SU SUNA KAN HANYA MADAIDAICIYA NE, SABANIN WADANNAN RAFIDA 'YAN SHI'AN.

2 - HASHIMUL BAHARANIY A MUGADDIMAN TAFSIRINSA YA CE:
اعلم ان الحق الذي لا محيص عنه حسب الاخبار المتواترة وغيرها, ان هذا القرآن الذي في ايدينا قد وقع فيه بعد رسول الله شيء من التغيرات, واسقط الذين جمعوه بعده كثيرا من الكلمات والآيات.

YA CE: LALLAI GASKIYAR DA BA MAKAWA GARETA, A GWARGWADON RUWAYOYI MUTAWATIRAI DA SAURANSU, SHI NE LALLAI WANNAN QUR'ANIN DA YAKE HANUNMU WANI ABU NA CANZAWA YA FARU A CIKINSA, BAYAN MANZON ALLAH (SAW). WADANDA SUKA TARA SHI A BAYANSA SUN ZUBAR DA KALMOMI DA AYOYI MASU YAWA.
DUBA TAFSIRUL BURHAN NA AL- BAHARANIY pg 32.

* DON ALLAH JAMA'A KU DUBA YADDA WANNAN MUJRIMIN YAKE TUHUMAR FIYAYYUN SAHABBAN MANZON ALLAH (RA) DA DA CANZA QUR'ANI.

3 - KUMA DU YA CE:
وعندي في وضوح صحة هذا القول (تحريف القرآن) بعد تتبع الاخبار وتفحص الآثار, بحيث يمكن الحكم بكونه من ضرورات مذهب التشيع, وانه من اكبر مقاصد غصب الخلافة.

YA CE: A RA'AYINA, INGANCIN WANNAN MAGANA ( NA CANZA QUR'ANI) A FILI YAKE. BAYAN BIBIYAN HADISAI DA BINCIKEN RUWAYOYI, TA YADDA ZAI YIWU A YI HUKUNCIN DA CEWA, HAKAN YANA DAGA CIKIN AQIDUN MAZHABAR SHI'A, KUMA YANA DAGA CIKIN MAFI GIRMAN MANUFOFIN K'WACEN KHALIFANCI (WATON WANDA AKA YI MA aLIYU (RA).
DUBA TAFSIRUL BURHAN, pg 49.

* JAMA'A DA MA ABIN DA SU RAFIDA 'YAN SHI'A SUKE FADI, SHI NE WAI SAHABBAI SUN ZUBAR DA AYOYIN KHALIFANCIN ALIYU (RA) DAGA AL- QUR'ANI. MA'ANA, ABINDA YA SA SUKA CANZA QUR'ANIN SHI NE SABODA K'WACEN KHALIFANCIN DA SUKA YI WA ALIYU (RA).



No comments:

Post a Comment