Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Saturday, 6 February 2016

KIYAYYAR RAFIDHA GA BANU UMAYYA

TSINE MA BANU UMAYYA DA RAFIDA SUKE YI HANYA CE TA TSINE MA SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW). WANDA HAKAN ZINDIK'ANCI NE!!!

JAMA'A GA MAGANGANUN MALAMAN TAFSIRI AKAN TAFSIRIN DA RAFIDA SUKA RIK'E NA AYAR ISRA'I. SUN RIK'E WANNAN TAFSIRIN NE DON SU RINK'A TSINE MA SAHABBAI. ALLAH YA CE:
وما جعلنا الرؤيا التي أريناك إلا فتنة للناس والشجرة الملعونة في القرآن ونخوفهم فما يزيدهم إلا طغيانا كبيرا.
WAI MA'ANAR FA'DIN ALLAH:
والشجرة الملعونة.
WAI BANI UMAYYA NE.
TO WANNAN TAFSIRIN BA DADAI BA NE, BA MAI YARDA DA SHI SAI JAHILI KO MAI MUNGUN NUFI, MAI TSINE MA SAHABBAI.

تفسير القرطبي:
وقال ابن عباس: هذه الشجرة بنو أمية، وأن النبي صلى الله عليه وسلم نفى الحكم. وهذا قول ضعيف محدث والسورة مكية، فيبعد هذا التأويل، إلا أن تكون هذه الآية مدنية ولم يثبت ذلك.
ALK'UR'DUBIY YA CE: IBNU ABBAS (RA) YA CE: WANNAN BISHIYA ITA CE: BANU UMAYYA, KUMA ANNABI (SAW) YA KORI ALHAKAM. WANNAN MAGANA CE MAI RAUNI K'IRK'IRARRIYA, DON SURAR A MAKKA TA SAUKA. WANNAN TAFSIRIN YAYI NISA DA AYAR, SAI DAI IN AYAR A MADINA TA SAUKA, HAKAN KUWA BAI TABBATA BA!!!!!

DON HAKA DUK WANDA YA CE BANU UMAYYA TSINANNU NE TO SHI YA FI CANCANTAR TSINUWA. BA MAI FA'DIN HAKAN KUWA SAI RAFIDA!!!


التحرير والتنوير:
IBNU ASHUUR YA CE:
ويوجد في بعض التفاسير أن ابن عباس قال: في الشجرة الملعونة بنو أمية. وهذا من الأخبار المختلفة عن ابن عباس، ولا أخالها إلا مما وضعه الوضاعون في زمن الدعوة العباسية لإكثار المنفرات من بني أمية، وأن وصف الشجرة... بأنها 
الملعونة في القرآن صريح في وجود آيات في القرآن ذكرت فيها شجرة ملعونة وهي شجرة الزقوم كما علمت. ومثل هذا الاختلاق خروج عن وصايا القرآن في قوله: ولا تلمزوا أنفسكم ولا تنابزوا بالألقاب بئس الاسم الفسوق بعد الإيمان [الحجرات: 11].
YA CE: ANA SAMU A WASU LITTATAFAN TAFSIRAI, IBNU ABBAS (RA) YA CE: TSINANNIYAR BISHIYA ITA CE BANU UMAYYA. TO WANNAN YANA DAGA CIKIN RUWAYOYI DA AKA K'IRK'IRA WA IBNU ABBAS (RA), BA NA ZATONSU SAI DAGA IRIN ABIN DA MAK'ARYATA SUKA K'IRK'IRA A LOKACIN DA'AWAR KAFA GOMNATIN ABBASIYYA., DON YAWAITA ABUBUWAN DA ZA SU SA A K'I BANU UMAYYA. KUMA LALLAI SIFFANTA BISHIYA DA LA'ANANNIYA A BAYYANE YAKE A CIKIN K'UR'ANI, AKWAI AYOYI DA AKA AMBACI BISHIYA TSINANNIYA A CIKINSU, KUMA ITA CE BISHIYAR ZAK'K'UUM KAMAR YADDA KA SANI. IRIN WANNAN K'IRK'IRAN SUNAN SA'BA WASIYYAR ALK'UR'ANI NE. SAI YA AMBACI AYAR HUJRAT!

KA GA WANNAN YANA TABBATAR DA JAHILCIN RAFIDA DA IRIN MUNGUN NUFINSU!!!


اضواء البيان:
وبهذا التحقيق الذي ذكرنا تعلم أن قول من قال : إن الرؤيا التي أراه الله إياها هي رؤياه في المنام بني أمية على منبره ، وإن المراد بالشجرة الملعونة في القرآن بنو أمية - لا يعول عليه ; إذ لا أساس له من الصحة ، والحديث الوارد بذلك ض...عيف لا ت
قوم به حجة.
ASHSHANK'I'DIY BAYAN YA AMBACI INGANTACCEN TAFSIRIN AYAR TARE DA HUJJOJI SAI YA CE:
WANNAN TANTANCEWAR DA MUKA AMBATA DA SHI NE ZAKA SAN LALLAI FA'DIN WANDA YA CE: MAFARKIN DA ALLAH YA NUNA WA ANNABI (SAW) ITA CE MAFARKINSA DA YA YI A CIKIN BACCI NA BANI UMAYYA AKAN MINBARINSA, WAI BISHIYA TSINANNIYA A CIKIN ALK'UR'ANI ANA NUFIN BANU UMAYYA NE, BA MAGANA CE DA ZA A DOGARA DA ITA BA, DON BA TA DA TUSHEN GASKIYA DA INGANCI, HADISIN DA YA ZO DA WANNAN MAGANA MAI RAUNI NE BA A KAFA HUJJA DA SHI.

AMMA SABODA TSABAR JAHILCI WANNAN MAGANAR NURUDDEEN YA GUTSURO YA KAFA HUJJA DA ITA, SABODA BAI SAN FASSARAR BA, ALHALI HUJJA CE AKANSA.
BAI SAN FASSARAN:
لا يعول عليه.
BA. ALLAH YA RABA MU DA JAHILCI MURAKKABI. JAHILIN DA BAI SAN SHI JAHILI BA NE!!


المحرر الوجيز:
IBNU A'DIYYA BAYAN YA AMBACI TAFSIRIN SAI YA CE:
وفي هذا التأويل نظر.

AKWAI ABIN DUBAWA A WANNAN TAFSIRIN!!
MA'ANA BAI TABBATA BA SAI AN YI BINCIKE!!!!!
...TO INA NURUDDEEN KA BINCIKA MANA INGANCIN HADISIN TUKUNA KAFIN KA CIGABA DA MAGANA!!!!!

تفسير ابن كثير:
وقد قيل: المراد بالشجرة الملعونة: بنو أمية. وهو غريب ضعيف.
قال ابن جرير: حدثت عن محمد بن الحسن بن زبالة، حدثنا عبد المهيمن بن عباس بن سهل بن سعد، حدثني أبي عن جدي قال: رأى رسول الله صلى الله عليه وسلم بني فلان ينزون على منبره نزو القرود فساءه ذلك، فما استجمع ضاحكا حتى مات. قال: وأنزل الله في ذلك: { وما جعلنا الرؤيا التي أريناك إلا فتنة للناس } الآية.
وهذا السند ضعيف جدا؛ فإن "محمد بن الحسن بن زبالة" متروك، وشيخه أيضا ضعيف بالكلية. ولهذا اختار ابن جرير: أن المراد بذلك ليلة الإسراء، وأن الشجرة الملعونة هي شجرة الزقوم، قال: لإجماع الحجة من أهل التأويل على ذلك، أي: في الرؤيا والشجرة.
IBNU KASEER YA CE: WAI AN CE; ABIN NUFI DA TSINANNIYAR BISHIYA SHI NE BANU UMAYYA. WANNAN ABU NE BAK'O MAI RAUNI.
SAI YA KAWO HADISIN DA IBNU JARIR YA RUWAITO DAGA FARKO HAR ZUWA SAHAL BIN SA'AD (RA).....
SAI YA CE: WANNAN ISNADIN MAI MATUK'AR RAUNI NE, SABODA MUH'D BIN HASSAN BIN ZABALA MATRUKI NE, (WATO BA A KAR'BAN HADISINSA SABODA RASHIN GASKIYA), MALAMINSA KUMA GABA 'DAYA MAI RAUNI NE. DON HAKA NE MA IBNU JARIR 'DIN YA ZA'BI CEWA ABIN NUFI; SHI NE ABIN DA YA FARU DA MANZON ALLAH A DAREN ISRA'INSA, KUMA TSINANNIYAR BISHIYA ITA CE BISHIYAR ZAK'K'UUM, KUMA YA CE: SABODA HA'DUWAR HUJJA DAGA MASANA TAFSIRI AKAN HAKA...!

GA NASSIN MAGANAR IBNU JARIR 'DIN BAYAN YA AMBACI HADISIN:
وأولى الأقوال في ذلك بالصواب، قول من قال: عنى به رؤيا رسول الله صلى الله عليه وسلم ما رأى من الآيات والعبر في طريقه إلى بيت المقدس، وبيت المقدس ليلة أسري به، وقد ذكرنا بعض ذلك في أول هذه السورة.
وإنما قلنا ذلك أولى بالصواب، لإجماع الحجة من أهل التأويل على أن هذه الآية إنما نزلت في ذلك، وإياه عنى الله عز وجل بها.
IBNU JARIR YA CE: MAGANAR DA TA FI DACEWA DA DADAI, ITACE MAGANAR WANDA YA CE: ANA NUFIN KALLON DA MANZON ALLAH YA YI NE A KAN HANYARSA TA ZUWA BAITUL MAK'DIS, NA AYOYIN ALLAH DA ABABEN LURA DA WA'AZTUWA A DAREN DA AKA YI ISRA'I DA SHI. KUMA MUN AMBACI SASHEN WANNAN BAYANIN A FARKON SURAR.
ABIN DA YASA MUKA CE WANNAN FASSARA TAFI DACEWA DA DADAI, SABODA HA'DUWAR HUJJAR MASANA TAFSIRI AKAN CEWA; WANNAN AYAR TA SAUK'A NE A WANNAN BATUN, KUMA SHI ALLAH YAKE NUFI!!!!!!

TO KAI NURUDDEEN DON ME YASA BA KA ZA'BI ABIN DA IBNU JARIR YA ZA'BA BA, IN HAR ZAKA KAFA HUJJA DA ABIN DA YA RUWAITO, KAWAI SABODA MUNGUN NUFI GA SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW)????!!!!
TO ALLAH WADAI!!!


مفاتيح الغيب:
القول الثاني : قال ابن عباس رضي الله عنهما : الشجرة بنو أمية يعني الحكم بن أبي العاص قال ورأى رسول الله صلى الله عليه وسلم في المنام أن ولد مروان يتداولون منبره فقص رؤياه على أبي بكر وعمر وقد خلا في بيته معهما فلما تفرقوا سمع ر...سول الله
 صلى الله عليه وسلم الحكم يخبر برؤيا رسول الله صلى الله عليه وسلم فاشتد ذلك عليه ، واتهم عمر في إفشاء سره ، ثم ظهر أن الحكم كان يتسمع إليهم فنفاه رسول الله صلى الله عليه وسلم. قال الواحدي : هذه القصة كانت بالمدينة ، والسورة مكية فيبعد هذا التفسير إلا أن يقال : هذه الآية مدنية ولم يقل به أحد ، ومما يؤكد هذا التأويل قول عائشة لمروان لعن الله أباك وأنت في صلبه فأنت بعض من لعنه الله.
AL-RAZIY YA AMBACI MAGANAR IBNU ABBAS (RA) NA CEWA TSINANNIYAR BISHIYA ITA CE BANU UMAYYA, TARE DA AMBATAN HADISAN, SAI YA CE:
ALWAHIDIY YA CE: WANNAN K'ISSAR A MADINA TA KASANCE, SURA KUMA A MAKKA TA SAUK'A, DON HAKA WANNAN TAFSIRIN YA YI NISA DA AYAR (MA'ANA BABU ABIN DA YA HA'DA SU), SAI DAI IN ACE: AYARA A MADINA AKA SAUK'ETA, BABU KUMA WANDA YA FA'DI HAKAN.

HADISIN ALHAKAM BIN ABIL AASI KUWA, SAM BAI TABBATA DAGA MANZON ALLAH BA. GA MAGANAR IBNU HAJAR AKAN HADISIN:
قوله : ( والشجرة الملعونة في القرآن قال : شجرة الزقوم )
هذا هو الصحيح ، وذكره ابن أبي حاتم عن بضعة عشر نفسا من التابعين ، ثم روى من حديث عبد الله بن عمرو أن الشجرة الملعونة الحكم بن أبي العاص وولده وإسناده ضعيف.
MA'ANA: FA'DIN ALLAH: TSINANNIYAR BISHIYA TANA CIKIN ALK'URA'ANI, YA CE: BISHIYAR ZAK'K'UUM CE.
WANNAN SHI NE INGANTACCEN FASSARA, IBNU ABI HATIM YA AMBACE SHI DAGA MUTUM GOMA SHA DAGA CIKIN TABI'AI. SA'ANNAN SAI YA RUWAITO DAGA HADISIN ABDULLAHI 'DAN AMR (RA) CEWA; TSINANNIYAR BISHIYA ITA CE ALHAKAM BIN ABIL AASI SHI DA 'YA'YANSA. AMMA ISNADINSA MAI RAUNI NE.
DUBA FATHUL BARIY NA IBNU HAJAR A KITABUT TAFSIR, A TAFSIRIN AYAR ISRA'I!!!

MA'ANA BAI TABBATA DAGA ANNABI (SAW) BA!!


روح المعاني:
وهو كما ترى ولا يخفى أن تفسير الآية بما ذكر غير ظاهر الملاءمة للسياق والله تعالى أعلم بصحة الأحاديث.
AL'ALUUSIY BAYAN YA AMBACI TAFSIRIN, KUMA YAYI MAGANA MAI TSAWO, SAI YA CE: GA FA ABIN KAMAR YADDA KAKE GANI, LALLAI BA ABU NE '...BOYAYYE
 BA, FASSARA AYAR NAN DA ABIN DA AKA AMBATAN NAN, A FILI BA SU DACE DA ABIN DA AKE MAGANA AKAI BA, TO ALLAH NE YASAN INGANCIN HADISAN!!!!!

INA NURUDDEEN, SAI KA NEMO MANA INGANCIN HADISAN, IN BA HAKA BA KUMA KA TABBATA JAHILI MAI MUNGUN NUFI WA SAHABBAN ANNABI (SAW)!!!!
ALLAH YA SHIRYEKA!!!!

زاد المسير:
والثاني : أنه أري بني أمية على المنابر ، فساءه ذلك ، فقيل له : إنها الدنيا يعطونها ، فسري عنه . فالفتنة هاهنا : البلاء ، رواه علي بن زيد بن جدعان عن سعيد بن المسيب ، وإن كان مثل هذا لا يصح ، ولكن قد ذكره عامة المفسرين.
IBNUL JAUZIY YA CE: NA 2, WAI AN NUNA WA ANNABI (SAW) BANU UMAYYA A MAFARKI SUNA KAN MINBARINSA, SAI HAKAN YA BA SHI HAUSHI, SAI AKA CE MASA: AI DUNIYA CE AKA BASU, SAI YAYI FARIN CIKI.
FITINA A CIKIN AYAR ITA CE: BALA'I. ALIYU BIN ZAID BIN JUD'AN NE YA RUWAITO DAGA SA'IDU BINIL MUSAYYAB. KO DA YAKE IRIN WANNAN BA YA ZAMA INGANTACCE.

TO NURA KA JI, DUK MALAMAN DA KAKE CEWA SUN FA'DA A CIKIN TAFSIRANSU SUN CE MA BAI INGANTA BA, DON HAKA JINGINA SHI WA MANZON ALLAH KUWA JAHILCI NE!!!!!
TSINE MA SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW) KUWA ZINDIK'ANCI NE!!!!!!!
SAI KA YI HATTARA!!!!!

KA AMBACI ALKASHSHAF NA ZAMAKHSHARIY, TO LALLAI BAN SAMU MAGANAR BA A CIKIN LITTAFI!!!!!

DUK ABIN DA NA KAWON NAN, ZAKA SAME SHI A LITTATAFAN TAFSIRAN DA NA AMBATA, A WAJEN TAFSIRIN AYAR, A SURATUL ISRA'I!!!!

AL- RABE'I BIN NAFI'I AL-HALABIY YA YI GASKIYA DA YAKE CEWA:
معاوية ستر لأصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم، فإذا كشف الرجل الستر اجترأ على ما وراءه.
MA'ANA: MU'AWIYA (RA) LABULE NE NA SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW), DAGA MUTUM YA YAYE LABULEN KAW
AI ZAI FA'DA KAN ABIN DA KE BAYANSA NE!!!!!!!!!!

YAU GA SHI MUNA GANI A WALL 'DIN RAFIDI NURUDDEEN, YANA GAMA KAFIRTA MU'AWIYA (RA) SAI YA FA'DA KAN USMANU (RA) YA KAFIRTA SHI!!!



ALLAH YA SHIRYI MAI NEMAN GASKIYA!!!

No comments:

Post a Comment