Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Saturday, 6 February 2016

RAFIDHA ('YAN SHI'A) YAHUDAWA SUKA BI A AQIDARSU TA WASIYYA

Yahudawa sun yi nufin gurbata Addinin Muslunci, sai suka haifar da RAFIDANCI (Shi'anci) ta hanyar Abdullahi dan Saba'i, kamar yadda suka gurbata Kiristanci ta hanyar Bulus. Don haka RAFIDANCI Photo Copy ne na Yahudanci. A biyomu a hankali don samun tabbacin wannar magana.

RAFIDA ('Yan Shi'a) suna da Aqidar WASIYYA, ma'ana wai Aliyu (RA) ne WASIYYIN Manzon Allah (SAW). Wannar Aqida sun gajeta ne a wajen Yahudawa, inda suke cewa Yusha'u bin Nuuni shi ne WASIYYIN Musa (AS). Don haka Aqidar RAFIDA ta WASIYYA asalinta Bayahudiyar Aqida ce.

RAFIDA sun yi kama da Yahudawa a cikin wannar Aqida ta Wasiyya ta fiskoki kamar haka:
1 - RAFIDA sun yi laqabi ma Aliyu (RA) da WASIYYIN Manzon Allah (SAW), haka Yahudawa ma sun yi wannan laqabi ma Yusha'u bin Nuuni da WASIYYIN Musa (AS).
2 - RAFIDA su
n WAJABTA samun WASIYYI a bayan Annabi Muh'd (SAW). haka Yahudawa ma sun WAJABTA samun WASIYYI a bayan Annabi Musa (AS).
3 - RAFIDA da Yahudawa sun yi tarayya akan cewa: Allah shi yake nada wannan WASIYYI. A wajen RAFIDA Allah ne ya nada Aliyu (RA), a wajen Yahudawa kuma shi ne zabi Yusha'u bin Nuuni.
4 - RAFIDA da Yahudawa dukansu sun tarayya akan cewa, Allah yana magana da WASIYYI, kuma yana masa Wahayi.
5 - RAFIDA da Yahudawa dukansu suna ba ma WASIYYI matsayin da yake daidai da matsayin Annabi.
6 - RAFIDA sun ce: Allah ya dawo da rana ma Aliyu (RA) bayan ta fadi. Kamar haka Yahudawa ma suka ce: Allah ya tsayar da rana da wata ma Yusha'u bin Nuuni.


Malaman Shi'a da kansu sun tabbatar da cewa Aqidar WASIYYA wa Aliyu (RA), Bayahude Abdullahi dan Saba'i ne ya kirkireta. Kuma ya daukota ne daga Yahudanci.
Annaubakhtiy ya ce:
"وحكى جماعة من أهل العلم من أصحاب علي عليه السلام أن عبد الله بن سبأ كان يهو
دياً فأسلم ووالى علياً عليه السلام , وكان يقول وهو على يهوديته في يوشع بن نون بعد موسى عليه السلام بهذه المقالة فقال في إسلامه بعد وفاة النبي - صلى الله عليه وسلم - في علي عليه السلام بمثل ذلك, وهو اول من اشهر القول بفرض إمامة علي عليه السلام, واظهر البراءة من اعدائه, وكاشف مخالفيه, فمن هناك قال من خالف الشيعة: إن اصل الرفض ماخوذ من اليهودية"
Duba Firaqush Shi'a pg. 22
Ni'imatul lahi Aljaza'iriy ya ce:
قال عبد الله بن سبأ لعلي بن أبي طالب: أنت الإله حقاً فنفاه علي عليه السلام إلى المدائن وقيل إنه كان يهودياً فأسلم وكان في اليهودية يقول في يوشع بن نون وفي موسى مثل ما قال في علي, وقيل إنه اول من اظهر القول بوجوب إمامة علي, ومنه تشعبت اصناف الغلاة
Duba Al'anwarun Nu'umaniyya (2/ 234)
Ina masu hankali daga cikin 'Yan Shi'a ku farka!! Wallahi muna wannan aiki ne da nufin NASIhA, da so muku alheri. Allah ya shiryi masu neman gaskiya.


RAFIDA da Yahudawa dukansu sun tarayya akan cewa, Allah yana magana da WASIYYI, kuma yana masa Wahayi.
Almufeed ya ruwaito a cikin littafinsa Al- Ikhtisaas (327):
عن حمران بن أعين قال: قلت لأبي عبد الله عليه السلام: بلغني أن الرب تبارك وتعالى قد ناجى ع
ليا " عليه السلام، فقال: أجل قد كانت بينهما مناجاة بالطائف نزل بينهما جبرئيل
Daga himraan dan A'ayun yace: na ce wa Baban Abdullahi (AS): Labari ya sameni cewa, Ubangiji (TW) ya gana da Aliyu (AS), sai ya ce: Eh, hakika ganawa ta kasance a tsakaninsu a Da'ifa, Jibrilu ne ya sauka a tsakaninsu.
Assafaar ya ruwaito a cikin littafinsa Basaa'irud Darajaat (476):
عن سماعة بن مهران قال سمعت ابا عبد الله عليه السلام يقول ان الروح خلق اعظم من جبرئيل وميكائيل كان مع رسول الله صلى الله عليه وآله يسدده ويرشده وهو مع الائمة و الاوصياء من بعده.
Daga Samaa'a dan Mihraan ya ce: Ya ji Baban Abdullahi (AS) yana cewa: Lallai Alruuhu halitta ne yafi Jibrilu da Mika'ilu, ya kasance yana tare da Manzon Allah (SAW) yana dacar da shi kuma yana shiryar da shi, Kuma yana tare da Imamai da Wasiyyai bayansa (SAW).
To kun ji abin da RAFIDA suka ruwaito daga Imamansu, Wai ana musu Wahayi, kuma suna ganawa da Allah (T). Jama'a sai ku yi hukunci!


RAFIDA da Yahudawa dukansu suna ba ma WASIYYI matsayin da yake daidai da matsayin Annabi.
Kulaini ya ruwaito a cikin littafinsa Alkafiy 1/ 270:
عن محمد بن مسلم قال: سمعت أبا عبد الله عليه السلام يقول: الائمة بمنزلة رسول الله صلى الله عليه وآله إلا أنهم
ليسوا بأنبياء ولا يحل لهم من النساء ما يحل للنبي صلى الله عليه وآله فأما ما خلا ذلك فهم فيه بمنزلة رسول الله صلى الله عليه وآله.
Daga Muh'd dan Muslim yace: Na ji Baban Abdullahi (AS) yana cewa: Imamai suna da matsayin Manzon Allah (SAW), sai dai su ba Annabawa ba ne, kuma abin da ya halatta wa Annabi (SAW) na mata su bai halatta garesu ba, amma duk abin da ba wannan ba, to suna daidai da matsayin Manzon Allah (SAW) a cikinsa.
To Jama'a kun ga fa yadda littatafan RAFIDA ('Yan Shi'a) yake ciki da wulakanta matsayin Manzon Allah (SAW). Mu mun fadi gaskiya an ce ba ma son Annabi (SAW).
Ina masu hankali???
Ina masu Adalci??
Ina masu son sanin hakikanin Addinin RAFIDA ('Yan Shi'a)????!!!!!


No comments:

Post a Comment