Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Saturday, 6 February 2016

RAFIDHA ('YAN SHI'A) YAHUDAWA SUKA BI A AQIDARSU TA TAKAITA IMAMANCI A ZURRIYAR HUSSAIN (RA)


RAFIDA ('Yan Shi'a) sun takaita Imamanci a cikin zuriyyar Husaini Dan Aliyu (RA) kawai, kamar yadda Yahudawa suka takaice Mulkinsu a cikin zuriyyar Annabi Dawuda (AS) kawai. Wannar Aqida ta RAFIDA asalinta Bayahudiyar Aqida ce.

RAFIDA sun yi kama da Yahudawa a cikin wannar Aqida ta TAQAITA Imama cikin zuriyya Husaini (RA) kawai, ta fiskoki kamar haka:
1 - RAFIDA sun taqaita Imamanci cikin zuriyyar Husaini (RA) kawai har zuwa tashin Qiyama, kamar haka Yahudawa ma suka taqaita 
mulki cikin zuriyyar Dawuda (AS) kawai har zuwa tashin Qiyama.
2 - Dalilin RAFIDA akan taqaita imama a zuriyyar Husaini (RA) kawai ban da zuriyyar Hassan (RA), duk da cewa Hassan yafi daraja, shi ne koyi da Yahudawa, don sun taqaita jagororin Addini a zuriyyar Haruna (AS) kawai ban da Musa (AS), duk da cewa Musan yafi daraja.
3 - Yahudawa suna shardanta daukar Akwatin alkawarin Ubangiji ga sarakunansu. Kamar haka RAFIDA ma suka shardanta daukar Takobin Manzon Allah (SAW) ga ingancin Imamanci Imamansu, kuma suna kamanta takobin da wancan Akwatin.
4 - Abin mamaki, Imamancin da RAFIDA suka ce ba zai yanke ba a zuriyyar Husaini har zuwa tashin Qiyama, amma daga Husainin (RA) har zuriyyarsa babu wanda ya taba yin jagoranci. Kamar haka Yahudawa ma, mulkinsu da suka ce zai tabbata a zuriyya Dawuda (AS) ba inda yaje, don tuni ya yanke zamani mai tsawo. Wannan yana tabbatar da karyan RAFIDA da Yahudawa a wannar Aqida tasu.
5 -RAFIDA suna kafa dalili ma Aqidarsu ta taqaita adadin Imamansu zuwa 12 kawai, da kasancewar adadin ASBAADI Bani Isr'ila guda 12 ne.
Wadannan fiskoki suna tabbatar mana da cewa, lallai RAFIDANCI photo copy ne na Yahudanci. Ina masu hankali ku FARKA!!


Dalilin RAFIDA akan taqaita imama a zuriyyar Husaini (RA) kawai ban da zuriyyar Hassan (RA), duk da cewa Hassan yafi daraja, shi ne koyi da Yahudawa, don sun taqaita jagororin Addini a zuriyyar Haruna (AS) kawai ban da Musa (AS), duk da cewa Musan yafi daraja.
Almajlisiy ya ruwaito a cikin Biharul Anwar 25/ 249:
عن هشام بن سالم قال: قلت للصادق جعفر بن محمد عليه السلام الحسن أفضل أم الحسين ؟ فقال: الحسن أفضل من الحسين، قلت: فكيف صارت الامامة من بعد الحسين في عقبه دون ولد الحسن ؟ فقال: إن الله تبارك وتعالى أحب أن يجعل (3) سنة موسى وهارون جارية في الحسن والحسين، ألا ترى أنهما كانا شريكين في النبوة، كما كان الحسن والحسين شريكين في الامامة ؟ وإن الله عزوجل جعل النبوة في ولد هارون ولم يجعلها في ولد موسى وإن كان موسى أفضل من هارون.
Daga hisham dan Salim ya ce: Na ce ma Assadiq Ja'afar dan Muh'd (AS): hassan ne yafi falala ko hussaini? Sai yace: hassan ya fi hussaini falala. Sai nace: To yaya Imamanci ya zama a cikin zuriyyar hussaini bayansa, ba 'ya'yan hassan ba? Sai ya ce: Lallai Allah (TW) ya so ya sanya Sunnar Musa da haruna ta gudana ne game hassan da husaini, Shin ba ka ga sun yi tarayya a cikin Annabta ba ne, kamar yadda hassan da hussaini suka yi tarayya a cikin Imamanci? Lallai Allah ya sanya Annabta a cikin 'ya'yan haruna, amma bai sanyata a cikin 'ya'yan Musa ba, duk da kasancewar Musa ya fi haruna.

Yahudawa suna shardanta daukar Akwatin alkawarin Ubangiji ga sarakunansu. Kamar haka RAFIDA ma suka shardanta daukar Takobin Manzon Allah (SAW) ga ingancin Imamanci Imamansu, kuma suna kamanta takobin da wancan Akwatin.
Alkulainiy ya ruwaito a cikin Alkafiy 1/ 238:
عن سعيد السمان قال: سمعت أبا عبد الله عليه السلام يقول: إنما مثل السلاح فينا مثل التابوت في بني إسرائيل، كانت بنو إسرائيل أي أهل بيت وجد التابوت على بابهم اوتوا النبوة فمن صار إليه السلاح منا اوتي الامامة
Daga Sa'idu Assaman yace: Na ji Baban Abdullahi (AS) yana cewa: Misalin Makami (takobin Manzon Allah) a cikinmu, kamar Akwatin da yake wajen Banu Isra'ila ne. Banu Isra'ila sun kasance duk gidan suka samu akwatin a kofar gidansu, to za a basu Annabta. Kamar haka duk wanda takobin ya koma wajensa daga cikinmu to za a ba shi Imamanci.

To jama'a kun ga dai yadda RAFIDA suke ta kokkoyon Banu Isra'il cikin Aqidunsu.
Ina masu hankali ku farka!!
'Yan Shi'a ku koma ku karanta littatafan Malamanku, ku ga barnar da Bayahude Abdullahi dan saba'a ya dasa a cikinsu, da nufin gurbata Addini Muslunci. Amma ya makara, don Allah yayi Alkawarin kiyaye Addininsa daga hanun masu mungun nufi!


No comments:

Post a Comment