Shiatu Ali,
(1) ABIN DA YA KAMATA SHI'ATU ALI YA YI MANA BAYANI, SHI NE DALILIN DA YA SA SAYYIDINA HASAN (RA) YA YI SULHU ALHALI YANA DA K'ARFIN SOJA. SHIN BA SHI BA NE IMAMI WANDA YA WAJABA YA ZAMA SHUGABA BA, KO KUMA A'A, BABU WANI WAJABCI NE GA SHUGABANCIN NASA??!
IN KUMA WAJIBI NE YA ZAMA SHUGABA, AMMA SAI YA YI BAI'A GA SHUGABA KAFIRI (KAMAR YADDA 'YAN SHI'A SUKE RAYAWA), TO MENENE HUKUNCIN ABIN DA YA AIKATA??
• SA'ANNAN MISALAI DA KA KAWO NA YAK'IN BADAR DA SULHUL HUDAIBIYYA BA ZA SU DACE DA WANNAN BA. SABODA A LOKACIN DA ANNABI (SAW) YA YI YAK'IN BADR MUSULMAI SUNA DA K'ARFIN DA IZZAN DA ZA SU IYA FA'DA DA KAFIRAN DA SUKA YI YAK'I DA SU. SABODA ALLAH YA CE:
يا أيها النبي حرض المؤمنين على القتال إن يكن منكم عشرون صابرون يغلبوا مئتين وإن يكن منكم مئة يغلبوا ألفا من الذين كفروا بأنهم قوم لا يفقهون
MUTUM 20 SUNA DADAI DA MUTUM 200, MUTUM 100 SUNA DADAI DA MUTUM 1000.
TO A YAK'IN BADR KUWA, MUSULMAI 313, KAFIRAI KUMA 1000. TO KA GA SUN NINKASU KENAN. DON HAKA AN YI YAK'I BADAR NE A LOKACIN DA MUSULMAI SUNA DA K'ARFIN YIN YAK'I.
AMMA SULHUL HUDAIBIYYA ANNABI (SAW) BAI FITA DA SHIRIN YAK'I BA, A'A YA FITA NE DON ZUWA UMRA. SHI YA SA ANNABI (SAW) YA NUNA MUSU CEWA; SHI BA YAK'I YA ZO YI BA. TO SABODA ANNABI (SAW) YA TAUSAYA WA QURAISHAWA SABODA YAWAN YAK'UK'UWAN DA SUKE YI, SA'ANNAN KUMA YANA FATAN SHIRIYAR MUTANENSA, SAI SUKA AIKO WAKILANSU DON AYI SULHU, SUKA AIKO SUHAILU BN AMRU, SAI ANNABI (SAW) YA CE:
قد أراد القوم الصلح حين بعثوا هذا الرجل
LALLAI QURAISHAWA SUN NEMI SULHU TUN DA SUKA AIKO WANNAN MUTUMIN.
KUMA DA MA SU QURAISHAWAN SU SUKA NEMI YIN SULHUN, BA –WAI- SHI ANNABI (SAW) NE YA NEMA BA. SUKA CE MA SHI SUHAIL BN AMRU:
إيت محمدا فصالحه ولا يكون في صلحه إلا أن يرجع عنا عامه هذا فوالله لا تحدث العرب أنه دخلها علينا عنوة أبدا
TAFI WAJEN MUHAMMADU KA YI SULHU DA SHI, AMMA BA ABIN DA ZAI KASANCE A SULHUN SAI YA YARDA YA KOMA MADINA A WANNAN SHEKARAN, MA'ANA; BA ZAI YI UMRA BA….
SAI SUKA YI SULHU A KAN SU TSAYAR DA YAK'I A TSAKANINSU TSAWON SHEKARA 10.
DON HAKA BA –WAI- ANNABI (SAW) YA JANYE DAGA MATSAYINSA NA YA DENA MUSLUNCI YA ZO YA HA'DU DA SU BA.
DA WANNAN ZA KA FAHIMCI BABU ALAK'A A TSAKANIN SULHUL HUDAIBIYYA DA SULHUN DA AHSAN (RA) YA YI DA MU'AWIYA (RA), SABODA SHI HASAN (RA) JANYEWA YA YI DAGA MATSAYINSA GABA 'DAYA YA YI MUBAYA'A WA MU'AWIYA (RA).
HAKA KUMA BABU ALAK'A TSAKANIN YAK'IN BADR DA FITAN HUSAINI (RA), SABODA MUSULMAI A YAK'IN BADR SUNA DA K'ARFI, SA'BANIN FITAN HUSAINI (RA) DA MUTANENSA.
• DA WANNAN BAYANI ZA MU FAHIMCI RASHIN AMFANIN TAMBAYOYIN DA KA YI. SABODA KA GINASU NE A KAN KANA DA HUJJA A CIKIN SULHUL HUDAIBIYYA DA YAK'IN BADR, ALHALI BA KA DA HUJJA A CIKINSU KO KA'DAN, SABODA YANAYINSU BA 'DAYA BA NE. DON HAKA BABU BUK'ATAR AMSA TAMBAYOYINKA.
*** DA WANNAN ZA MU FAHIMCI CEWA; BA KA AMSA MANA TAMBAYARMU BA, SABODA SULHUL HUDAIBIYYA BA TA YI DADAI DA SULHUN HASAN (RA) WA MU'AWIYA (RA) BA. HAKA YAK'IN BADR MA BAI YI DAIDAI DA FITAN HUSAINI (RA) BA. DON HAKA TSUGUNE BA TA K'ARE BA.
*** HAKA SAURAN BAYANAN DA KA YI, DUKA KA GINASU A KAN WA'DANNAN ABUBUWA GUDA 2, ALHALI BA KA DA HUJJA A CIKINSU. DON HAKA KAWAI SHACI – FA'DI KA YI.
MUNA JIRAN GAMSASSHIYAR AMSA...
No comments:
Post a Comment