Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Thursday, 25 February 2016

YAYE SHUBUHOHI A KAN SULHUN HASSAN (RA) (1)

@GALADIMA NASIRU AMINU:

(1) NASIRU AMINU YA CE:
AMSA : KOSHAKKA BABU AWAJENKANE LAMARIN YAKEDA MATUKAR DAURE KAI, KOSHIN BAKASAN ANNABI YACE :
إن ابني هذا سيد وسيصلح الله به بين فئتين عظيمتين من المسلمين

WANNAN HADISINE WANDA ANNABI YAKE BADA LABARI DA ABINDA YAKE BABU MAKAWA FARUWARSA WATO YIN SULHU DA DANSA IMAM HASAN(A) ZAIYI DA MU'AWIYA, WATO WANNAN WANI ABUNE WANDA YAKE MUKADDARI WANDA BABU MAKAWA SAI YAFARU.
• AMMAR:
TO A NAN DAI KU 'YAN SHI'A KUNA KAFA HUJJA DA K'ADDARA KENAN WAJEN 'BATA WILAYAR IMAMIN DA IMAMANCINSA WAJIBI NE, INKARINSA KUMA KAFIRCI NE??!
SHE'DAN DA MUSHRIKAI NE SUKE KAFA HUJJA DA K'ADDARA:
قال رب بمآ أغويتني لأزينن لهم في الأرض ولأغوينهم أجمعين

GA MUSHRIKAI KUMA:
سيقول الذين أشركوا لو شاء الله ما أشركنا ولا آباؤنا ولا حرمنا من شيء كذلك كذب الذين من قبلهم حتى ذاقوا بأسنا

SHIN KUNA KAFA HUJJA DA K'ADDARA KENAN, WAJEN WARWARE IMAMANCI NA WAJIBI??!
SABODA K'IN AIKATA WAJIBI – ALHALI AKWAI IKON AIKATAWA – SA'BO NE, KAFA HUJJA DA K'ADDARA A KAN AIKATA SA'BO KUWA AIKIN SHE'DAN NE DA MUSHRIKAI. DON HAKA SHIN SHAI'DAN ABIN KOYINKU A NAN KENAN??!

(2) NASIRU YA CE:
SABODA HAKA MATSAWAR IDAN MUTUM YASANDA SHI WANNAN HADISIN SANNAN KUMA YAKE TUHUMTAR IMAM HASAN DACEWA YA AIKATA BADAI-DAIBA , TO YAKWANADA SANIN CEWA IRIN WADAN NAN ZANTUTTUKA DAYAKE FADA SUNYI KAMA DANA WAWAYE. DALILI KUWA SHINE TAYAYA ANNABI ZAICE ABU KAZA ZAIFARU SANNAN KUMA ACE SHI ANNABIN BAI NUNA KUSKUREN AIKATA YIN HAKA GASHI IMAM HASAN DINBA,

• AMMAR:
ZA KA FA'DI HAKA NE GA 'DAN SHI'A, WANDA YA YARDA DA WAJABCIN IMAMANCIN HASSAN (RA). SABODA DUK 'DAN SHI'A YANA DA WANNAR MATSALAR A CIKIN RANSA, SAI DAI YA YI TAQIYYA YA K'I BAYYANAWA. SABODA ABUBUWA GUDA BIYU SUN HA'DU MASA, 'DAYA YANA WARWARE 'DAYA, SUN YI MASA KARO A CIKIN AQIDARSA;
(1) ABU NA FARKO SHI NE: WAJABCIN IMAMA GA HASAN (RA).
(2) NA BIYU: JANYE WANNAN HANK'K'I NA WAJIBI DA SARAYAR DA SHI, TARE DA MIK'A SHI GA MUTUMIN DA BA YA CIKIN IMAMAI 12, WA'DANDA IMAMANCINSU YA WAJABA.
AMMA SHI AHLUS SUNNA BABU WANI ISHKALI (ABU MAI RIKITARWA) GARE SHI. SABODA BA YA 'DAUKE DA AQIDAR WAJABCIN IMAMANCIN HASAN (RA) A ZUCIYARSA. ALHAMDU LILLAHI, MU ZUKATARMU A TSARKAKE TAKE DAGA WANNAR AQIDA TAKU. AMMA DUK WANDA YA HA'DA WA'DANNAN ABUBUWA GUDA 2 TO DOLE YA SHIGA CIKIN RU'DU.
DON HAKA, MU AHLUS SUNNA DA KUKE SO MU FAHIMCI AQIDARKU, TA YAYA ZA KU IYA GAMSAR DA MU CEWA; BABU RIKITARWA A WANNAN HA'DIN GAMBIZAN DA KUKA YI??!

(3) NASIRU YA CE:
SAIMA YABONSA DA ANNABI YAYI DACEWA HASAN SHINE DAI SHUGABA…

• AMMAR:
TO AI WANNAN NE YA SA MU AHLUS SUNNA BA MU YI IMANI DA WAJABCIN IMAMANCIN HASSAN (RA) BA, SULHUN DA YA YI YA NUNA CEWA; DA MA IMAMANCINSA BA WAJIBI BA NE. KUMA DA IMAMANCIN WAJIBI HASAN (RA) YA BARI TO ZARGI NE ZAI ZO A KANSA, BA YABO BA. AMMA YABON DA YA ZO A DALILIN WANNAN SULHU SHI YAKE K'ARA NUNA CEWA; DA MA IMAMANCIN NASA BA NA WAJIBI BA NE.
AMMA KU 'YAN SHI'A, YAYA ZA KUYI DA WANNAN HADISI:
إن ابني هذا سيد وسيصلح الله به بين فئتين عظيمتين من المسلمين

IMAMINKU HASAN (RA) ZAI YI SULHU YA MIK'A SHUGABANCI NA WAJIBI, AMMA KUMA SAI AKA YABE SHI, MAIMAKON A ZARGE SHI, DON WANDA YA YA BAR WAJIBI –ALAHLI YANA DA IKON AIKATA SHI-, TO SHI ABIN ZARGI NE.
DON HAKA, KO DAI IMAMANCIN NASA BA WAJIBI BA NE??!
IN KUMA WAJIBI NE, TO YAYA ZA A YABI WANDA YA BAR WAJIBI??!
IN MU'AWIYA (RA) BAI CANCANTA BA, TO DON ME YA SA ANNABI (SAW) ZAI YABI HASAN (RA) A KAN SULHUN DA YA YI, YA MIK'A SHUGABANCI DA BAI'ARSA GA MU'AWIYA (RA)??!
IN HASAN (RA) YA CE:
إن معاوية نازعني حقا هو لي دونه فنظرت إصلاح الأمة وقطع الفتنة

IN HAK'K'IN IMAMA NA WAJIBI YAKE NUFI, TO YAYA ZAI YI YA SARAYAR DA SHI, SABODA HAK'K'I NE NA ALLAH, YA WAJABTA MASA IMAMANCI??!
SHIN – A WAJEN 'YAN SHI'A - AKWAI FITINAR DA TA KAI TAWAYE WA IMAMIN DA IMAMANCINSA NA WAJIBI NE, WANDA BARINTA KAFIRCI NE, TUN DA ANNABI (SAW) BAI GUSHE BA YANA YAK'AR MUSHRIKAI HAR SAI DA YA KAWAR DA FITINAR SHIRKA, DON HAKA HASAN (RA) MA KAMATA YA CIGABA DA YAK'I HAR SAI YA KAWAR DA FITINAR TAWAYE GA IMAMI WANDA AKWAI NASSI A KAN IMAMANCINSA. SABODA DUK WANDA YA YI ADDINI BA A K'ARK'ASHIN IMAMI BA TO YA YI AIKIN BANZA NE.
KULAINIY YA CE:
باب فيمن دان الله عزوجل بغير امام من الله جل جلاله

SAI YA KAWO DOGON HADISI DAGA ABU ABDILLA (RA) A CIKI SAI YA CE:
قال: لا دين لمن دان الله بولاية إمام جائر ليس من الله، ولا عتب على من دان بولاية إمام عادل من الله، قلت: لا دين لاولئك ولا عتب على هؤلاء؟ ! قال: نعم لا دين لاولئك ولا عتب على هؤلاء،

TO YAYA KENAN??!
SA'ANNAN KULAINIY YA KAWO A BABIN:
باب فرض طاعة الائمة

YA CE:
عن أبي سلمة عن أبي عبدالله عليه السلام قال: سمعته يقول: نحن الذين فرض الله طاعتنا، لا يسع الناس إلا معرفتنا ولا يعذر الناس بجهالتنا، من عرفنا كان مؤمنا، ومن أنكرنا كان كافرا، ومن لم يعرفنا ولم ينكرنا كان ضالا حتى يرجع إلى الهدى الذي افترض الله عليه من طاعتنا الواجبة فإن يمت على ضلالته يفعل الله به ما يشاء.

YA CE: MU NE WA'DANDA ALLAH YA FARLANTA YI MANA 'DA'A, …. MUTANE BA SU DA WANI UZURI IDAN SUKA JAHILCEMU. WANDA YA SANMU SHI NE MUMINI, WANDA KUMA YA YI INKARINMU YA ZAMA KAFIRI….
TO YAYA KENAN, SHIN WANNAR IMAMA WANDA FARLARCINTA YAKE DA MATUK'AR MUHIMMANCI BA TA KAI A CIGABA DA YAK'I A KANTA BA, SABODA INKARINTA KAFIRCI NE??!
KUMA – A BISA GA WANNAR RUWAYAR – AI IN HASAN (RA) YA YAK'I MUTANEN MU'AWIYA (RA), YA KASHESU KAFIRAI YA KASHE. ALLAH KUWA YA YI UMURNI DA A YAK'I KAFIRAI, TO IN HASAN (RA) YA K'I YAK'ARSU, BAI SA'BA UMURNIN ALLAH BA, ALHALI YANA DA K'ARFIN SOJA NA YAK'ARSU??!

No comments:

Post a Comment