KOWA YA SANI, A LOKACIN DA ANNABI (SAW) YA ZO FITA HIJIRA ZUWA GARIN MADINA, YA TAFI NE TARE DA SAYYIDINA ABUBAKAR AL- SIDDIQ (RA).
ALLAH YA CE:
إلا تنصروه فقد نصره الله إذ أخرجه الذين كفروا ثاني اثنين إذ هما في الغار إذ يقول لصاحبه لا تحزن إن الله معنا فأنزل الله سكينته عليه
"IN BA ZA KU TAIMAKE SHI BA, TO HAKIKA ALLAH YA TAIMAKE SHI A LOKACIN DA KAFIRAI SUKA FIDDA SHI (DAGA MAKKA), NA BIYUN MUTUM 2, A LOKACIN SUNA CIKIN KOGO, YAKE CE MA ABOKINSA: KADA KA YI BAKIN CIKI, LALLAI ALLAH YANA TARE DA MU. SAI ALLAH YA SAUKAR DA NITSUWARSA GARE SHI ..."
KUMA A WANNAN LOKACIN ANNABI (SAW) YA BAR SAYYIDINA ALIYU (RA) BAI FITA TARE DA SHI BA, KUMA YA UMURCE SHI YA KWANTA A KAN GADONSA, DON IN MUSHRIKAI SUN ZO SU YI ZATON CEWA; ANNABI (SAW) NE YAKE KWANCE A KAN GADON, DON HAKA YANA NAN BAI FITA BA, DON KAR SU FAHIMCI YA FITA DON YIN HIJIRA.
TO, A WANNAN HALI, ALAL HAK'IK'A SAYYIDINA ALIYU (RA) YANA FISKANTAR HA'DARIN KISA. DON IN MUSHRIKAN NAN SUKA SHIGO SUKA GA MUTUM YANA KWANCE A GADON ANNABI (SAW), KO SHAKKA BABU ZA SU ZATON CEWA; ANNABI (SAW) NE YAKE KWANCE, DON HAKA BABU WATA - WATA ZA SU KAI SARA DA TAKUBA NE DON SU KASHE SHI.
ABIN TAMBATAYA A NAN SHI NE:
IN SAYYIDINA ALIYU (RA) YA KASANCE IMAMI BISA NASSI, KUMA SHI NE WANDA AKA YI MASA WASIYYAR KHALIFANCI, TA YAYA ZA A JEFA SHI CIKIN WANNAN DANGER MAI GIRMAN GASKE??!
IN AN KASHE SHI TO YAYA ZA AYI DA KASANCEWARSA SHI NE IMAMI WASIYYI NA'DA'D'DEN KHALIFA BISA NASSI??!
A LOKACIN DA KUMA AKA BAR SAYYIDINA ABUBAKAR (RA) TARE DA ANNABI (SAW), ZA SU TSIRA SU CIGABA DA RAYUWA TARE!!
DA KAMATA YA YI A BAR SAYYIDINA ABUBAKAR (RA) A KAN GADON ANNABI (SAW) SABODA KO DA AN KASHE SHI, BABU WATA MATSALA, SABODA BA SHI NE IMAMI BISA NASSI BA, KUMA BA NA'DA'D'DEN KHALIFA BA!
AMMA DA AN KASHE SAYYIDINA ALIYU (RA) TO DA AN TUN'BUKE BISHIYAR IMAMA DA KHALIFANCI (BISA NASSI) TUN DAGA K'ASA HAR SAMA.
DON HAKA, IN SAYYIDINA ALIYU (RA) NE IMAMI BISA NASSI, KUMA WASIYYI, KUMA KHALIFAN DA AKA NA'DA, SAYYIDINA ABUBAKAR (RA) KUMA BA SHI NE KHALIFA BA, TO A CIKINSU WANENE YA FI KAMATA A BARI A KAN GADON ANNABI (SAW), WANDA KO DA AN KASHE SHI BABU WATA MATSALA GA IMAMA DA KHALIFANCI??!
WANENE KUMA WANDA YA KAMATA A TAFI HIJIRA DA SHI, WANDA BA A SO YA TA'BU, SABODA SHI ZAI ZAMA IMAMI DA KHALIFA A BAYAN ANNABI (SAW)??!
GAREKU 'YAN SHI'A...
* DON ALLAH AMSA KAWAI MUKE BUK'ATA, TARE DA TATTAUNAWA TA ILMI, CIKIN NITSUWA DA GIRMAMAWA. BAN DA HAYANIYA KO ZAGE - ZAGE.
TO 'YAN SHI'A BISMILLAH .....
No comments:
Post a Comment