Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Thursday, 25 February 2016

YAYE SHUBUHAR SANIN GAIBIN IMAMAN SHI'A

WATA RIWAYA TANA NUNA CEWA; ALIYU (RA) BAI SAN WANDA ZAI KASHE SHI BA, KUMA BAI SAN LOKACIN DA ZA A KASHE SHI BA. KAI, HASALI MA YA YI ZATON A WANNAN DAREN HIJIRAN ZA A KASHE SHI.
. AN RUWAITO DAGA GARE SHI YANA BA DA LABARIN DAREN HIJIRAN ANNABI (SAW), YAKE CEWA:
وأمرني أن أضطجع في مضجعه وأقيه بنفسي، فأسرعت إلى ذلك مطيعاً له مسروراً لنفسي بأن أقتل دونه.

"ANNABI (SAW) YA UMURCE NI DA IN KWANTA A SHIMFI'DARSA, IN BA DA KAINA KARIYA GARE SHI. SAI NA YI GAGGAWA ZUWA GA HAKAN, INA MAI YI MASA 'DA'A, INA MAI FARIN CIKI MA KAINA A KASHE NI A KANSA".

DUBA AL- LIKHTISWASW (165), AL- KHISWAL (367), AL- BIHAR (38/ 169), AMAALIY NA 'DUSIY (460), NURU AL- THAQALAINIY (1/ 205).

A WATA RIWAYAR AKA CE:
فلما نامت العيون جاء أبو طالب ومعه أمير المؤمنين، فأقام رسولَ الله واضطجع أمير المؤمنين مكانه، فقال أمير المؤمنين: يا أبتاه، إني مقتول.

"A YAYIN DA AKA YI BACCI, SAI ABU 'DALIB YA ZO TARE DA AMIRUL MUMININA, SAI MANZON ALLAH (SAW) YA TASHI, AMIRUL MUMININA KUMA YA KWANTA A WAJANSA. SAI YA CE: YA BABA, LALLAI NI KAM ZA A KASHE NI"!!

DUBA: AL- FUSULUL MUKHTAARAH (33), AL- BIHAR (36/46).

* TO A NAN SHI ALIYU (RA) YA 'DAUKA ZA A KASHE SHI. DON HAKA ASHE BAI SAN CEWA; SHAK'IYYI NE ZAI KASHE SHI BA. KUMA YA NUNA BAI SAN CEWA; ZAI ZAMA IMAMI A BAYAN ANNABI (SAW) BA, DON DA YA SANI, DA BA ZAI TA'BA ZATON ZA A KASHE SHI BA. ALHALI KUMA AKWAI RUWAYAR DA TAKE NUNA CEWA; SHI ALIYUN (RA) YA SAN CEWA; SHI IMAMI NE.

DON HAKA BA KA DALILI A MAGANARKA, KUMA WANNAN YANA NUNA UBAN IMAMAI 11, ALIYU (RA) BAI SAN GAIBU BA, BARE 'YA'YANSA SAURAN IMAMAI 11, KUMA YA NUNA CEWA; BAI SAN ZAI ZAMA IMAMI BA. DON HAKA BAI SAN AKWAI NASSI A KAN ZAMOWARSA IMAMI BA.

No comments:

Post a Comment