Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Thursday, 25 February 2016

INA NEMAN GAMSASSHIYAR AMSA NA (9)

DUKKAN MUSULMAI; AHLUS SUNNA DA 'YAN SHI'A SUN YI ITTIFAQI A KAN KASANCEWAR SAYYIDINA ALIYU (RA) GWARZO NE KUMA JARUMI NE, BA YA SHAKKAR KOWA A KAN FA'DAR GASKIYA, KUMA BA YA TSORON ZARGIN MAI ZARGI. KUMA ITA WANNAR JARUMTAKA TASA, SAYYIDI ALI (RA) BAI TA'BA RABUWA DA ITA A RAYUWARSA BA, HAR ZUWA LOKACIN DA WANI MARAS ALBARKA IBNU MULJIM YA KASHE SHI.
KUMA KOWA YA SANI CEWA; 'YAN SHI'A SUNA YA'DA CEWAR; SAYYIDI ALI (RA) SHI NE WASIYYIN ANNABI (SAW), WATO WANDA ANNABI (SAW) YA YI MASA WASIYYAR KHALIFANCI A BAYAN RASUWARSA KAI TSAYE, BA TARE DA MARABA BA.

TO ABIN TAMBAYA A NAN SHI NE:
SHIN JARUMTAKAR SAYYIDI ALIN (RA) TA DENA AIKI NE A LOKACIN DA YA YI BAI'A MA KHALIFAN ANNABI (SWA) ABUBAKAR (RA)??!
SA'ANNAN BAYAN ABUBAKAR (RA), YA YI BAI'A MA KHALIFA UMAR (RA)??!
SA'ANNAN BAYANSA YA YI BAI'A WA USMANU (RA)??!

SHIN YAYA AKA YI SAYYIDI ALI (RA) YA KASA HAWA MINBARIN MANZON ALLAH (SAW) A ZAMANIN KHALIFANCI KHALIFOFI GUDA 3, YA SHELANTA MA DUNIYA CEWAR; LALLAI WANNAN KHALIFANCIN HAK'K'INSA NE, FASHI DA K'WACE AKA YI MASA, SHI NE YA FI CANCANTA, SABODA SHI NE WANDA ANNABI (SAW) YA YI MASA WASIYYAR KHALIFANCIN??!

DON ME YA SA SAYYIDI ALI (RA) BAI YI HAKA BA, ALHALI SHI JARUMI NE, WANDA BA YA TSORON FA'DAR GASKIYA MA KOWA??!
DON ME YA SA SAYYIDI ALI (RA) YA YI SHIRU A KAN WANNAN HAK'K'I NASA, ALHALI "WILAYA" 'DAYA CE DAGA CIKIN RUKUNIN ADDINI A WAJEN 'YAN SHI'A, KUMA DUK DA KASANCEWAR YANA DA MAGOYA BAYA??!

* GAREKU 'YAN SHI'A...

* DON ALLAH AMSA KAWAI MUKE BUK'ATA, TARE DA TATTAUNAWA TA ILMI, CIKIN NITSUWA DA GIRMAMAWA. BAN DA HAYANIYA KO ZAGE - ZAGE.

TO 'YAN SHI'A BISMILLAH ....

No comments:

Post a Comment