Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Thursday, 25 February 2016

INA NEMAN GAMSASSHIYAR AMSA (3)

*** IDAN 'YAN SHI'A SUNA RAYA CEWA; DUBBAN SAHABBAN ANNABI (SAW) SUN HALARCI LOKACIN DA ANNABI (SAW) YA YI WASIYYAR KHALIFANCI GA ALIYU (RA) A GADEER KHUM, KUMA DUKKANSU SUN JI ANNABI (SAW) YA NA'DA ALIYU (RA) A MATSAYIN KHALIFANSA A BAYAN RASUWARSA KAI TSAYE, TO DON ME YA SA BA A SAMU KO DA SAHABI GUDA 'DAYA BA, - DUK DA CEWA; SAHABBAN DUBBAI NE -, KAI, BA A SAMU KO DA AMMAR BN YASIR (RA) BA, KO MIQDAD BN AMRU (RA), KO KUMA SALMANUL FARISIY (RA) DA YA ZO WAJEN ABUBAKAR (RA) YA CE MASA:
"DON ME YA SA ZA KA K'WACE WA ALIYU (RA) HAK'K'INSA NA KHALIFANCI, ALHALI KA SAN ANNABI (SAW) SHI YA NA'DA KHALIFANSA A GADEER KHUM BA KAI BA?"

** DON ALLAH ABOKAN TATTAUNAWA DAGA CIKIN 'YAN SHI'A, JAWABI MAI GAMSARWA KAWAI MUKE BUK'ATA, BA MU BUK'ATAR HAYANIYA DA KAME - KAME, KO ZAGE - ZAGE DA SAURAN ABUBUWAN DA BA SU DACE BA.
** YANA DA KYAU MU KOYI TATTAUNAWA MAI FA'IDA, WACCE ZA TA BA DA NATIJA.

** ALLAH YA SA MU DACE.

TO 'YAN SHI'A GAREKU....

No comments:

Post a Comment