IDAN ALIYU (RA) YA KASANCE YANA SANE DA CEWA; SHI NE KHALIFA, WANDA AKA NASSANTA SHI TUN DAGA WAJEN ALLAH (T), TO DON ME YA SA ALIYUN (RA) YA YI MUBAYA'A WA ABUBAKAR (RA) DA UMAR (RA) DA USMANU (RA)??!
IN 'YAN SHI'A SUN CE: GAZAWA YA YI SABODA AN FI K'ARFINSA.
TO AI SHUGABANCI BAI KAMACI KASASSHE BA, SABODA SHUGABANCI YANA KASANCEWA NE GA MAI K'ARFI DA IKO.
IN KUMA SUN CE: YANA DA IKO, AMMA SAI DAI SHI NE KAWAI YA K'YALESU BAI K'WATA BA.
TO LALLAI WANNAN HA'INCI NE, MAHA'INCI KUWA BAI CANCANCI SHUGABANCI BA. BA ZA A BA SHI AMANAR TALAKAWA BA.
KUMA HAKAN YA NUNA CEWA; SHI BA MA'ASUMI BA NE, DON K'IN KARBAN KHALIFANCIN DA YA YI ALHALI AKWAI NASSI A KANSA DAGA WAJEN ALLAH, KUMA YANA DA IKO, TO HAKAN SA'BA MA ALLAH NE.
*** WANNAR TAMBAYA FA BA MATSALA BA CE GA AHLUS SUNNA, SABODA SU BA SU YI IMANI DA CEWA: ALLAH YA NASSANTA ALIYU (RA) A MATSAYIN KHALIFA BA. DON HAKA MUBAYA'AR DA ALIYU (RA) YA YI MA ABUBAKAR (RA) DA UMAR (RA) DA USMAN (RA), BAI SA YA ZAMA KASASSHE KO MAHA'INCI KO MAI SA'BO BA.
AMMA SU 'YAN SHI'A DA SUKA YI IMANIN AKWAI NASSI A KAN ALIYU (RA), MENENE JAWABINSU A KAN ABABEN DA MUBAYA'AR TASA GA KHALIFOFI 3 TAKE LAZIMTAWA, NA KASHI, KO HA'INCI, DA SA'BA MA ALLAH??!
*** TO 'YAN SHI'A GAREKU...
MUN BARKU DA MASU HANKALI SU YI ALKALANCI.
No comments:
Post a Comment