Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Sunday, 7 February 2016

SABODA FALALAR ALLAH DA ZA'BINSA GA SAHABBAI YA SA YAKE BA SU LADA A KAN AIYUKANSU NINKIN ABIN DA YAKE BAYAR MA SAURAN MUTANE!!!


KAMAR YADDA MUKA GABATAR DA CEWA; MATSAYIN SAHIBTAR MANZON ALLAH (SAW) MATSAYI NE DA ALLAH YAKE BAI MA WANDA YA ZA'BA DAGA CIKIN BAYINSA, YA YI MUSU FALALA YA BA SU WANNAN MATSAYI SABODA SANINSA GA CANCANTARSU GA WANNAN MATSAYIN.

YANA DAGA CIKIN ABIN DA YAKE TABBATAR DA WANNAN MATSAYI KASANCEWAR SU ALLAH YANA BA SU LADA DA SAKAMAKO A KAN AIYUKANSU NE NINKIN ABIN DA YAKE BA MA SAURAN BAYI.

1- ALLAH YA CE A GAME DA MATAN ANNABI (SAW):
ومن يقنت منكن لله ورسوله وتعمل صالحا نؤتها أجرها مرتين وأعتدنا لها رزقا كريما (31) يانساء النبي لستن كأحد من النساء إن اتقيتن

"DUK WACCE TA YI 'DA'A MA ALLAH DA MANZONSA DAGA CIKINKU, KUMA TA YI KYAKKYAWAN AIKI, TO ZA MU BA TA LADANTA SAU BIYU (NINKI BIYU NA LADAN SAURAN MATA), KUMA ZA MU TANADA MATA ARZIKI MAI GIRMA (A ALJANNA). YA KU MATAN ANNABI (SAW), IN KUN JI TSORON ALLAH, KU BA DADAI KUKE DA 'DAYA DAGA CIKIN SAURAN MATA BA".

IBNU ABI HATIM AL- RAZIY YA RUWAITO DAGA MUQATIL BN SULAIMAN YA CE:
نؤتها أجرها مرتين في الآخرة بكل صلاة أو صيام أو صدقة أو تكبيرة أو تسبيحة باللسان مكان كل حسنة تكتب عشرين حسنة

"ZA MU BATA LADANTA SAU BIYU A LAHIRA; A KAN KOWACE SALLAH DA AZUMI DA SADAKA, DA KABBARA KO TASBIHI DA HARSHE, A GURBIN KOWANE KYAKKYAWAN AIKI ZA A RUBUTA MATA (WA MATAR ANNABI (SAW) LADAN AIKI ISHIRIN (20)".
تفسير ابن أبي حاتم (9/ 3128)

* ALLAHU AKBAR!!
KAI LADA GOMA (10) ZA A BAKA A KAN KYAKKYAWAN AIKI, AMMA ITA MATAR ANNABI (SAW) LADA ISHIRIN (20) ZA A BATA!!!

ALLAHU AKBAR!!!
{ذَلِكَ فَضْلُ اللَّهِ يُؤْتِيهِ مَنْ يَشَاءُ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ}

SHI YA SA IBNU ABBAS (RA) YA FADA KAMAR YADDA AL- WAHIDIY YA HAKAITO:
قال ابن عباس: يريد ليس قدركن عندي مثل قدر غيركن من النساء الصالحات، أنتن أكرم علي وأنا بكن أرحم، وثوابكن أعظم.

"IBNU ABBAS (RA) YA CE: ALLAH YANA NUFIN CEWA; MATSAYINKU A WAJENA BA KAMAR MATSAYIN WATA DABAN DAGA CIKIN SAURAN MATA SALIHAI BA NE, KU KUN FI GIRMA DA MATSAYI A WAJENA, KUMA NA FI YI MUKU RAHAMA DA JIN TAUSAYI, KUMA LADANKU DA SAKAMAKON AIYUKANKU YA FI GIRMA A KAN NA SAURAN".
التفسير الوسيط للواحدي (3/ 469)

IBNU RAJAB AL- HANBALIY (R) YA CE:
فدل على أن من عظمت منزلته ودرجته عند الله فإن عمله يضاعف له أجره.

"WANNAN SAI YA YI NUNI A KAN CEWA; WANDA MATSAYINSA DA DARAJARSA TA GIRMAMA A WAJEN ALLAH, TO LALLAI AIKINSA ZA A NINKA MASA LADANSA".
فتح الباري لابن رجب (1/ 162)

2- HAKA GAME DA SAURAN SAHABBAI, ANNABI (SAW) YA CE:
«لا تسبوا أصحابي، فلو أن أحدكم أنفق مثل أحد ذهبا ما بلغ مد أحدهم، ولا نصيفه»

"KADA KU ZAGI SAHABBAINA, SABODA DA 'DAYANKU ZAI CIYAR DA ZINARI KAMAR DUTSEN UHUDU, BA ZAI KAI MUDU 'DAYA NA 'DAYANSU BA, KO RABINSA BA ZAI KAI BA".

* GIRMAN DUTSEN UHUDU KAMAR YADDA 'YAN MADINA SUKE BA DA LABARI (ALLAH NE MAFI SANI):
1. TSAYINSA KUSAN KILOMITA 8 NE.
2. FA'DINSA KUSAN KILOMITA 3 NE.

* ALLAHU AKBAR!!!
{ذَلِكَ فَضْلُ اللَّهِ يُؤْتِيهِ مَنْ يَشَاءُ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ}

ABU SULAIMAN AL- KHA'D'DABIY (R) YA CE:
والمعنى أن جهد المقل منهم واليسير من النفقة الذي أنفقوه في سبيل الله مع شدة العيش والضيق الذي كانوا فيه أوفى عند الله وأزكى من الكثير الذي ينفقه من بعدهم.

"MA'ANA; KOKARIN MAI 'DAN KA'DAN DAGA CIKIN SAHABBAI, DA 'DAN KA'DAN NA ABIN CIYARWAN DA SUKA CIYAR SABODA ALLAH, DUK DA TSANANIN RAYUWA DA K'UNCIN RAYUWA DA SUKA KASANCE A CIKI, 'DAN ABIN DA SUKA CIYAR YA FI CIKA A WAJEN ALLAH, KUMA YA FI TSARKAKUWA FIYE DA ABU MAI YAWAN DA NA BAYANSU ZA SU CIYAR".
معالم السنن (4/ 308)

SHARAFUD DEEN AL- 'DIBIY (R) YA CE:
والمعنى أنه لا ينال أحدكم بإنفاق مثل أحد ذهبا من الفضيلة والأجر ما ينال أحدهم بإنفاق مد طعام أو نصفه لما يقارنه من مزيد الإخلاص وصدق النية وكمال النفس.

"MA'ANA; LALLAI 'DAYANKU IN YA CIYAR DA ZINARI KAMAR DUTSEN UHUDU, BA ZAI SAMU FALALA DA LADA IRIN ABIN DA SAHABI ZAI SAMU BA IDAN YA CIYAR DA MUDUN ABINCI, KO RABIN MUDU, SABODA ABIN DA YA HA'DU DA HAKAN NA K'ARIN IKHLASI DA GASKIYAR NIYYA, DA KAMALAR RAI".
شرح المشكاة للطيبي الكاشف عن حقائق السنن (12/ 3841)

AMMA IBNU HAJAR (R) YA DANGANTA WANNAR MAGANA GA AL- BAIDHAWIY, DUBA:
فتح الباري لابن حجر (7/ 34)

* A CIKIN WANNAN HADISI SAI ANNABI (SAW) YA NUNA YADDA ALLAH YAKE NINKA AIYUKAN SAHABBAI, YA BASU LADA NINKI - NINKIN ABIN DA ZAI BAYAR WA SAURAN MUTANEN DA SUKA ZO A BAYANSU.
WANNAN TSANTSAR FALALAR ALLAH CE, DA YAKE BAYAR DA ITA GA WANDA YA ZA'BA DAGA CIKIN BAYINSA, SABODA SANINSA GA CANCANTARSU GA WANNAN MATSAYI.

IN BA TSANTSAR FALALAR ALLAH BA, TA YAYA MUTUM ZAI SAMU WANNAN MATSAYI?!
BABU MAI IYA SAMUN WANNAN MATSAYI KOMAI YAWAN TSORON ALLANSA DA YAWAN IBADARSA DA YAWAN AIYUKAN ALHERINSA SAI SU SAHABBAI DA ALLAH YA ZA'BA YA YI MUSU WANNAR FALALA. WANNAN SHI YAKE NUNA MANA MATSAYIN SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW) A WAJEN ALLAH YA WUCE WANI YA TSAYA YANA TUNANIN -WAI- SAHABBAI SUN YI LAIFI KAZA, DA KAZA, HAR KA TSAYA KANA YI MUSU ALKALANCI!!!

DA WANNAN ZA KA SAN CEWA; GIRMAN LADA DA ALLAH ZAI BAI WA SAHABBAI A KAN AIYUKANSU, SUN KAI SU SHIGA ALJANNA KAI TSAYE DA IZNIN ALLAH, ALHALI DA MA ALLAH YA YI MUSU ALKAWARIN GAFARA DA GIDAN ALJANNA TUN TUNI SABADA FALALAR DA YA YI MUSU.

SANIN WANNAN SHI ZAI SA KA TAUSAWA MA RAFIDHA 'YAN SHI'A, SABODA SUN JAHILCI MATSAYIN SAHABBAI A WAJEN ALLAH, TARE DA JAHILTAR FALALAR DA ALLAH (T) YA YI MUSU A DUNIYA DA LAHIRA.

No comments:

Post a Comment