Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Sunday, 7 February 2016

BANBANCI TSAKANIN TAUHIDI DA SHIRKA


A LOKACIN DA WASU SUKE CEWA; "YA ALIY MADAD", KO "YA BARHAMA" KO WANI DABAN DAGA CIKIN TALIKAI, MU KUMA SAI MU CE: "YA ALLAH MADAD".

ALLAH YA CE:
{إِذْ تَقُولُ لِلْمُؤْمِنِينَ أَلَنْ يَكْفِيَكُمْ أَنْ يُمِدَّكُمْ رَبُّكُمْ بِثَلَاثَةِ آلَافٍ مِنَ الْمَلَائِكَةِ مُنْزَلِينَ (124) بَلَى إِنْ تَصْبِرُوا وَتَتَّقُوا وَيَأْتُوكُمْ مِنْ فَوْرِهِمْ هَذَا يُمْدِدْكُمْ رَبُّكُمْ بِخَمْسَةِ آلَافٍ مِنَ الْمَلَائِكَةِ مُسَوِّمِينَ (125) } [آل عمران: 124 - 126]

"KA TUNA LOKACIN DA KAKE CE WA MUMINAI; SHIN BAI ISHEKU BA, UBANGIJINKU YA YI MUKU K'ARI DA MALA'IKU 3000, SUNA MASU SAUK'A DAGA SAMA? EH, IN KUN YI HAKURI, KUKA JI TSORON ALLAH, KUMA KAFIRAI SU ZO MUKU A CIKIN WANNAN TSANANIN FUSHIN NASU, TO ALLAH ZAI YI MUKU K'ARI DA MALA'IKU 5000 SUNA MASU ALAMA (A BADAR AN GA MALA'IKU DA FARAREN RAWANI)".

AL- WAHIDIY (R) YA CE:
وقوله: يمددكم ربكم أصل المد والإمداد في اللغة: الزيادة، يقال: مد النهر، ومد الماء، إذا زاد ومده نهر آخر.

"FA'DIN ALLAH "UBANGIJINKU ZAI YI MUKU K'ARI", ASALIN KALMAR "AL- MADDU" DA "AL- IMDADU" A LUGAR LARABCI SHI NE: K'ARI. A KAN CE; "RAFIN YA K'ARU", "RUWAN YA K'ARU", IDAN YA K'ARU, WANI RAFIN YA ZO YA YI MASA K'ARI".
التفسير الوسيط للواحدي (1/ 488)

KUMA DU YA CE:
وأكثر ما يستعمل الإمداد في الخير

"MAFI YAWAN INDA AKE AMFANI DA "IMDAD" SHI NE; A KAN ABIN ALHERI".
التفسير الوسيط للواحدي (1/ 488)

KUMA ALLAH YA CE:
{إِذْ تَسْتَغِيثُونَ رَبَّكُمْ فَاسْتَجَابَ لَكُمْ أَنِّي مُمِدُّكُمْ بِأَلْفٍ مِنَ الْمَلَائِكَةِ مُرْدِفِينَ (9) } [الأنفال: 9، 10]

"KA TUNA LOKACIN DA KUKE NEMAN AGAJIN GAGGAWA A WAJEN UBANGIJINKU, SAI YA AMSA MUKU CEWA; LALLAI NI MAI YI MUKU K'ARI NE DA MALA'IKU 1000 SAHENSU YANA BIYE DA SASHE".

* A WANNAR AYAR TA "SURATUL ANFALI", TANA BAYANIN HALIN MANZON ALLAH (SAW) DA SAHABBANSA NE A LOKACIN YAKIN BADAR, INDA SUKE ROK'ON ALLAH, SUKE NEMAN AGAJI DA TAIMAKONSA.
IBNU JARIR AL- 'DABARIY (R) YA RUWAITO DAGA:
سماك الحنفي قال: سمعت ابن عباس، يقول: ثني عمر بن الخطاب رضي الله عنه قال: " لما كان يوم بدر ونظر رسول الله صلى الله عليه وسلم إلى المشركين وعدتهم، ونظر إلى أصحابه نيفا على ثلاثمائة، فاستقبل القبلة، فجعل يدعو ويقول: «اللهم أنجز لي ما وعدتني، اللهم إن تهلك هذه العصابة من أهل الإسلام، لا تعبد في الأرض،» فلم يزل كذلك حتى سقط رداؤه، وأخذه أبو بكر الصديق رضي الله عنه، فوضع رداءه عليه، ثم التزمه من ورائه، ثم قال: كفاك يا نبي الله بأبي وأمي مناشدتك ربك، فإنه سينجز لك ما وعدك، فأنزل الله: {إذ تستغيثون ربكم فاستجاب لكم أني ممدكم بألف من الملائكة مردفين} [الأنفال: 9] "

"DAGA IBNU ABBAS (RA) YA CE: UMAR BN KHATTAB (RA) YA BA NI LABARI, YA CE:
"A RANAR BADAR, YAYIN DA MANZON ALLAH (SAW) YA KALLI MUSHRIKAI DA KAYAN YAK'INSU, KUMA YA DUBI SAHABBANSA SU 300 DA WANI ABU A KAI, SAI YA FISKANCI AL- QIBLA, SAI YA FARA ADDU'A YANA CEWA: "YA ALLAH KA ZARTAS MINI DA ABIN DA KA YI MINI ALKAWARI. YA ALLAH IN KA HALAKA WA'DANNAN 'YAN JAMA'A MA'ABOTA MUSLUNCI (WATO SAHABBAI KENAN, IN YA HALAKAR DA SU TA HANYAR BA DA NASARA WA MUSHRIKAI A KANSU, HAR SU KASHESU), BA ZA A SAMU MASU BAUTA MAKA A BAYAN KASA BA", MANZON ALLAH (SAW) BAI GUSHE BA A WANNAN HALI NA ADDU'A DA NEMAN TAIMAKO DA AGAJI A WAJEN ALLAH HAR SAI DA MAYAFINSA YA FA'DI, SAI ABUBAKAR (RA) YA 'DAUKA YA YAFA MASA, SA'ANNAN YA TSAYA TARE DA SHI A BAYANSA,.....
HAR ALLAH YA SAUKAR DA ITA WANNAR AYAR:
{إذ تستغيثون ربكم فاستجاب لكم أني ممدكم بألف من الملائكة مردفين} [الأنفال: 9] "
DUBA:
تفسير الطبري = جامع البيان (11/ 51)

* GA SHI NAN, MANZON ALLAH (SAW) DA SAHABBANSA ALLAH KAWAI SUKE ROK'O, SUKE NEMAN TAIMAKONSA A KAN YA YI MUSU "MADAD", WATO K'ARIN TAIMAKO.
* ABIN TAMBAYA A NAN: DON ME YA SA SAHABBAI BA SU NEMI "MADAD" A WAJEN ANNABI (SAW) BA, SU CE: "YA MANZON ALLAH MADAD"?!
DON ME YA SA SAHABBAI BA SU CE: "YA ALIY MADAD" BA?!
HAKA DON ME YA SA SHI ALIYU (RA) BAI CE: "YA MANZON ALLAH MADAD" BA?!

* AMSA: SABODA MANZON ALLAH (SAW) DA SAHABBANSA SU NE SHUGABANNIN MASU TAUHIDI DA KA'DAITA ALLAH, SHI YA SA BA ZA SU KIRA SUNAN KOWANE MAHLUKI BA, DON SU NEMI "MADAD" A WAJENSA. IN SUN YI HAKA SUN ZAMA 'DAYA DA KAFIRAN DA SUKE YAK'A KENAN, SABODA SU KAFIRAN SUNA NEMAN "MADAD" NE A WAJEN MAHLUKI WATO GUMAKANSU.
ALLAH YA KIYASHESU!

KUMA ALLAH YA CE:
{ ثُمَّ رَدَدْنَا لَكُمُ الْكَرَّةَ عَلَيْهِمْ وَأَمْدَدْنَاكُمْ بِأَمْوَالٍ وَبَنِينَ وَجَعَلْنَاكُمْ أَكْثَرَ نَفِيرًا (6) } [الإسراء: 6، 7]

"SA'ANNAN SAI MUKA DAWO MUKU DA DAULA DA MULKI A KANSU, KUMA MUKA YI MUKU K'ARI NA DUKIYA DA 'YA'YA, MUKA SANYAKU KUKA ZAMA MAFI YAWAN MUTANE".

KUMA YA CE:
{أَيَحْسَبُونَ أَنَّمَا نُمِدُّهُمْ بِهِ مِنْ مَالٍ وَبَنِينَ (55) نُسَارِعُ لَهُمْ فِي الْخَيْرَاتِ بَلْ لَا يَشْعُرُونَ (56) } [المؤمنون: 55 - 57]

"SHIN SUNA ZATO ABIN DA MUKE YI MUSU K'ARI DA SHI NA DUKIYA DA 'YA'YA (SABODA SUNA DA WANI MATSAYI NE A WAJENMU, A'A), KAWAI MUNA GAGGAUTA MUSU ALHERAI NE TUN A NAN DUNIYA, ALHALI BA SU SANI BA".

KUMA DU YA CE:
{وَأَمْدَدْنَاهُمْ بِفَاكِهَةٍ وَلَحْمٍ مِمَّا يَشْتَهُونَ (22)} [الطور: 22]

"SAI MUKA YI MUSU K'ARI DA KAYAN MARMARI DA NAMA NA DAGA ABIN DA SUKE SHA'AWA".

KUMA YA CE:
{وَيُمْدِدْكُمْ بِأَمْوَالٍ وَبَنِينَ وَيَجْعَلْ لَكُمْ جَنَّاتٍ وَيَجْعَلْ لَكُمْ أَنْهَارًا (12) } [نوح: 12، 13]

"KUMA ZAI YI MUKU K'ARI NA DUKIYA DA 'YA'YA, KUMA ZAI SANYA MUKU LAMBUNA, KUMA ZAI SANYA MUKU RAFUKA".

TO JAMA'A, KUN GA GABA 'DAYA A CIKIN AYOYIN AL- QUR'ANI ALLAH YANA JINGINA "MADAD" NE GARE SHI, BAI JINGINA SHI GA WANI MAHLUKI BA, SABODA SHI "AL- MADAD AL - MU'DLAQ" (WATO MADAD A SAKE BA QAIDI), YANA DAGA CIKIN AIYUKAN ALLAH NE SHI KA'DAI, BABU WANI MAHLUKI DA YAKE DA IKO A KANSA.

DON HAKA ALLAH NE KAWAI YAKE YIN MADAD, WATO K'ARI NA TAIMAKO DA AGAJI KO K'ARIN ALHERI NA ARZIK'I DA 'YA'YA DA SAURAN ALHERAI GA BAYINSA, BABU WANI MAHLUKI DA YA ISA YA YI MAKA MADAD KAI TSAYE SAI ALLAH KAWAI.

SABODA HAKA BAI HALATTA WANI YA KIRA SUNAN WANI MAHLUKI (KOMAI MATSAYINSA) A KAN YA YI MASA MADAD BA SAI DAI ALLAH KAWAI.

DA WANNAN ZA MU GANE GIRMAN KUSKUREN WA'DANDA SUKE KIRAN WANIN ALLAH, SUNA MASU NEMAN MADAD A WAJENSA.

DON HAKA, IN KUNA MAGANA DA WANI, SAI YA CE: "YA ALIY MADAD", KO YA KIRA WANI MAHLUKI DABAN, KAI KUMA SAI KA CE: "YA ALLAH MADAD", LA'ALLA ZAI FAHIMCI GIRMAN BANBANCIN DA KE TSAKANIN NAKA DA NASA, SHI YA NEMI K'ARIN TAIMAKO A WAJEN MAHLUKI MABUK'ACI A WAJEN ALLAH, KAI KUMA KA NEMA A WAJEN MAHALICCI KUMA MAMALLAKIN KOWA DA KOMAI, KUMA MAI CIKAKKEN IKO A KAN KOMAI, SAI YA GA GIRMAN BANBANCIN DA KE TSAKANIN MAHALICCI DA MAHLUKI, SAI YA FAHIMCI KUSKURENSA YA TUBA YA KOMA KAN HANYA MADAIDAICIYA.

No comments:

Post a Comment