Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Sunday, 7 February 2016

DUK WANI MA'ASUMI A BAYAN ANNABI (SAW) MA'ASUMIN K'ARYA NE


A DUK DUNIYA BABU WANI MUTUM MA'ASUMI A BAYAN ANNABI (SAW) KAMAR YADDA BABU WANI ANNABI A BAYANSA. DUK WANI MA'ASUMI A BAYANSA MA'ASUMIN K'ARYA NE, KAMAR YADDA DUK WANI ANNABI A BAYANSA ANNABIN K'ARYA NE.

QA'IDA CE A KAN CEWA; BA A YIN IMANI DA MA'ASUMANCIN WANI MUTUM A BAYAN ANNABI (SAW), HAR KHALIFOFINSA GUDA HU'DU; ABUBAKAR (RA) DA UMAR (RA), DA USMAN (RA), DA ALIYU (RA), DUK CIKINSU BABU WANI MA'ASUMI, KAMAR YADDA BABU ANNABI A CIKINSU. WANNAN YA SA ZA SU IYA AIKATA KUSKURE DA AIKIN ZUNUBI, AMMA KUMA TA YIWU SU TUBA, ALLAH YA YAFE MUSU, KO KUMA A KANKARE MUSU SHI DA MANYAN AIYUKANSU NA ALHERI MASU YAWA DA SUKE DA SHI, KO KUMA A JARABESU DA WATA MASIFA A JIKINSU, KAMAR TA RASHIN LAFIYA KO A CIKIN IYALANSU, KO A DUKIYARSU, SAI ALLAH YA KANKARE MUSU ZUNABAN NASU A DALILINTA, KO KUMA DA WANI ABUN NA DABAN.

No comments:

Post a Comment