BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
FITAN HUSAINI (RA) DAGA MAKKA ZUWA IRAK'I:
HUSAINI YA FITA DAGA MAKKA YA KAMA HANYA ZUWA GARIN KUFA, A RANAR LITININ 10 GA ZUL HIJJA. YA FITA TARE DA IYALANSA DA KUMA MUTUM 60 DAGA CIKIN MUTANEN KUFA.
IBNU UMAR (RA) YA CE:
غلبنا حسين بن على بالخروج ولعمرى لقد رأى فى أبيه واخيه عبرة فرأى من الفتنة وخذلان الناس لهما ما كان ينبغى له أن لا يتحرك ما عاش وأن يدخل فى صالح ما دخل فيه الناس فان الجماعة خير.
YA CE: HUSAINI (RA) YA RINJAYEMU AKAN SAI YA TAFI, NA TABBATA YA GA WA'AZI GAME DA BABANSA DA 'DAN UWANSA. YA GA FITINA DA YAUDARAR MUTANEN GARESU, ABIN DA YA KAI YA SA KAR YA TAFI MATUK'AR YANA RAYE, YA KAMATA YA SHIGA CIKIN KYAKKYAWAN ABIN DA MUTANE SUKA SHIGA. DOMIN HA'DIN KAI SHI NE ALHERI.
DUBA IBNU KASIR.
BANU UMAYYA SUNA GARGA'DI MA GWAMNAN IRAK'I UBAIDULLAHI BIN ZIYAD; AKAN YA KIYAYE AFKA MA HUSAINI (RA):
1- KHALIFA YAZIDU BIN MU'AWIYA:
YAZIDU YA RUBUTA TAKARDA WA IBNU ZIYAD:
قد بلغنى أن الحسين قد توجه إلى نحو العراق فضع المناظر والمسالح واحترس واحبس على الظنة وخذ على التهمة غير أن لا تقتل إلا من قاتلك واكتب إلى فى كل ما يحدث من خبر والسلام.
YA CE: LABARI YA SAME NI CEWA; HUSAINI (RA) YA FISKANCI IRAK'I, KA SA MAHANGAI, DA MASU MAKAMAI, KA SA TSARO, KUMA KA TSARE DUK WANDA AKE ZATO YANA DA HANU A CIKI, KA KAMA WANDA AKE TUHUMA. SAI DAI KAR KA KASHE KOWA SAI WANDA YA YAK'E KA. SA'ANNAN KA RUBUTO MIN LABARIN DUKKAN ABIN DA YA FARU. WASSALAM.
2- MARWAN BIN HAKAM.
MARWAN BIN HAKAM YA RUBUTA TAKARDA WA IBNU ZIYAD GWAMNAN IRAK'I:
أما بعد فان الحسين بن على قد توجه إليك وهو الحسين بن فاطمة وفاطمة بنت رسول الله ص وتالله ما احد يسلمه الله احب إلينا من الحسين فاياك أن تهيج على نفسك مالا يسده شىء ولا تنساه العامة ولا تدع ذكره آخر الدهر والسلام.
YA CE: BAYAN HAKA, LALLAI HUSAINI 'DAN ALIYU (RA) YA FISKANCI WAJENKA. SHI NE; HUSAINI 'DAN FATIMA, FATIMA 'YAR MANZON ALLAH (SAW). NA RANTSE DA ALLAH BABU WANI DA MUKA FI SON ALLAH YA KARE SHI KAMAR HUSAINI (RA). INA GARGA'DINKA, KAR KA TAYAR MA KANKA MASIFAR DA BABU ABIN DA ZAI IYA KARETA. KUMA ABIN DA MUTANE BA ZA SU MANTA DA SHI BA. KUMA ABIN DA K'ARSHEN ZAMANI BA ZAI DENA TUNA SHI BA. WASSALAM.
3- GWAMNAN MAKKA AMRU 'DAN SA'EED 'DAN ASS.
AMRU 'DAN SA'EED YA RUBUTA MA IBNU ZIYAD GWAMNAN IRAK'I TAKARDA:
أما بعد فقد توجه إليك الحسين وفى مثلها تعتق أو تكون عبدا تسترق كما يسترق العبيد.
YA CE: BAYAN HAKA, HAK'IK'A HUSAINI (RA) YA FISKANCE KA. A IRIN WANNAN NE ZA A 'YANTAKA KO KUMA KA ZAMA BAWA, ZA A BAUTAR DA KAI KAMAR YADDA AKE BAUTAR DA BAYI.
DUKKAN WA'DANNAN NASSOSHI SUNA CIKIN AL- BIDAYA NA IBNU KASIR.
HUSAINI (RA) YA ISA K'ADISIYYA:
HUSAINI (RA) YANA KAN HANYA SAI LABARIN KASHE MUSLIM BIN AK'EEL YA SAME SHI. SAI YA YI NIYYAR KOMOWA. TO SAI IYALAN AK'EEL DA SUKE TAR DA SHI SUKA CE:
لا والله لا نبرح حتى ندرك ثارنا او نذوق ما ذاق اخونا.
SUKA CE: BA ZAI YIWU BA, MUN RANTSE DA ALLAH BA ZA MU GUSHE BA, HAR SAI MUN 'DAUKO FANSANMU, KO KUMA MU MA MU 'DAN'DANA ABIN DA 'DAN UWANMU YA 'DAN'DANA.
SAI HUSAINI (RA) YA CE:
لا خير في العيش بعد هؤلاء.
YA CE: RAYUWA BA TA DA AMFANI A BAYAN WA'DANNAN.
LALLAI HUSAINI (RA) BAI GUSHE BA YANA GANIN MUTANEN KUFA ZA SU TAIMAKE SHI, AMMA KUMA BA ZAI IYA ISA KUFAN BA, SABODA GWAMNA IBNU ZIYAD YA SA MATA TSARO A KOWACE HANYA TA SHIGA KUFAN, BA SHIGA BA FITA.
TO DA LABARI YA ISA GA IBNU ZIYAD CEWA; HUSAINI (RA) YANA HANYA SAI YA TURA RUNDUNA TA MAYAK'A 1000, A K'ARK'ASHIN JAGORANCI AL- HURRU 'DAN YAZEED AL- TAMIMIY. SAI YA SAME SHI KUSA DA K'ADISIYYA.
SAI HURRU YA CE MASA; INA ZUWA YA 'DAN 'YAR ANNABI (SAW)?
SAI YA CE: IRAK'I.
SAI YA CE: INA UMURTANKA DA KA KOMA, KAR ALLAH YA JARABENI DA KAI. KA KOMA TA INDA KA FITO, KO KUMA KA TAFI SHAM WAJEN YAZEEDU, KAR KA JE KUFA!
AMMA HUSAINI (RA) SAI YA K'I, YA CIGABA DA TAFIYA KUFA.
AMMA SAI HURR YA K'YALE SHI, SABODA YA ZA'BI SU RABU LAFIYA.
A BIYO MU A HANKALI, GASKIYA TA YI KUSA TA YI HALINTA. ZA A SHA MAMAKI; ANA TSAMMANIN WUTA A MAK'ERA SAI AKA SAMETA A MASAK'A.
No comments:
Post a Comment