BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
HUSAINI (RA) YA ISO KARBALA:
HUSAINI (RA) SAI YA TSAYA A WANI WAJE, SAI YA TAMBAYA, INA NE NAN?
SAI AKA CE MASA: KARBALA.
SAI YA CE: KARBUN WA BALA'UN.
MA'ANA; BAK'IN CIKI DA BALA'I.
ANA HAKA SAI GA RUNDUNA DAGA IRAK'I A K'ARK'ASHIN JAGORANCIN UMAR BIN SA'AD BIN ABI WAK'K'ASS. TARE DA SHI AKWAI SOJOJI 4000.
SAI HUSAINI (RA) YA CE: MUTANEN GARINKU NE SUKA RUBUTA MINI WASIK'U; AKAN IN ZO, AMMA IN KUN K'I NI, ZAN JUYA IN KOMA.
SAI UMAR BIN SA'AD YA AIKA WA IBNU ZIYAD YANA NEMAN SHAWARARSA.
TO DAGA NAN SAI YA CE; SU BARSHI YA TAFI YA DUBA YA GA ME LAMARIN MUTANE ZAI NUNA. SAI SU KUMA SUKA BA SHI ZA'BI; KO YA YI MUBAYA'A MA YAZEEDU KO KUMA SU YAK'E SHI. SAI YA CE MUSU; YA ZA'BI YAK'I.
WASU MALAMAN SUNA CEWA; SHI YA BA SU ZA'BIN ABUBUWA GUDA 3;
1- SU BAR SHI YA KOMA INDA YA FITO.
2- SU BAR SHI YA TAFI JIHADIN KAFIRAI.
3- SU BAR SHI YA TAFI SHAM WAJEN YAZEEDU.
TO SAI SHI UMAR BIN SA'AD YA CE: KAI KA AIKA WAJEN YAZEEDU, NI KUMA IN AIKA WAJEN IBNU ZIYAD. TO SAI SHI UMAR YA AIKA WAJEN IBNU ZIYAD, AMMA SHI HUSAINI (RA) BAI AIKA WAJEN YAZEEDU BA.
TO SAI IBNU ZIYAD YA AIKO DA WANI ANA CE MASA; SHAMRU 'DAN ZUL JAUSHAN, AKAN KAWAI HUSAINI (RA) YA YARDA DA HUKUNCIN IBNU ZIYAD; KAWAI YA MIK'A WUYA YA YI MUBAYA'A WA YAZEED, KO KUMA A YAK'E SHI. KUMA SHI SHAMRU YA ZAMA SHI NE; JAGORAN YAK'IN.
KAWAI SAI HUSAINI (RA) YA CE:
« لا والله لا أنزل على حكم عبيد الله بن زياد أبدا ».
YA CE: NA RANTSE DA ALLAH; HAR ABADA BA ZAN BI HUKUNCIN IBNU ZIYAD BA.
HUSAINI (RA) YANA GARGA'DIN RUNDUNAR IRAK'I:
YAWAN WA'DANDA SUKE TARE DA HUSAINI (RA) MUTUM 72 NE KAWAI. SU KUMA SOJOJIN KUFA, MUTUM 5000 NE. A LOKACIN DA 'BANGARORIN 2 SUKA HA'DU, SAI HUSAINI (RA) YA CE MA SOJOJIN KUFAN:
KU TAMBAYI KAWUKANKU, KU YI MASU HISABI. SHIN YA KAMATA KU YAK'I MUTUM IRINA, ALHALI NI 'DAN 'YAR ANNABINKU NE? A YANZU BABU WANI 'DAN 'YAR ANNABIN NAKU DA YA SAURA A BAYAN K'ASA IN BA NI BA. ALHALI MANZON ALLAH (SAW) YA CE MANA; NI DA 'DAN UWANA:
« هذان سيدا شباب أهل الجنة »
MA'ANA; WA'DANNAN GUDA 2, SHUWAGABANNIN MATASAN ALJANNA NE.
HAKA YA CIGABA DA K'WA'DAITAR DA SU AKAN SU BAR BIYAYYA WA IBNU ZIYAD; GWAMNAN IRAK'I, KUMA SU DAWO SU HA'DE DA SHI. SAI MUTUM 30 SUKA DAWO WAJENSA. DAGA CIKINSU AKWAI HURRU BIN YAZEED AL- TAMIMIY WANDA A BAYA SHI NE SHUGABAN RUNDUNAR FARKO DA TA ZO; MAI MUTUM 1000.
SAI AKA CE MA SHI HURRU; KAI DA KA ZO TARE DA MU, AMMA ZAKA KOMA CIKIN JAMA'AR HUSAINI (RA)?
SAI YA CE: WALLAHI KAITONKU! NA BA DA ZA'BI WA RAINA NE, A TSAKANIN WUTA DA ALJANNA. WALLAHI BA ZAN ZA'BI WANI ABU AKAN ALJANNA BA, KO DA ZA A DADDATSANI A K'ONANI.
BAYAN HAKA HUSAINI (RA) YA YI WA 'BANGARORI 2 SALLAR AZAHAR DA LA'ASAR NA RANAR ALHAMIS. ALHALI YA CE MUSU:
KUNA DA LIMAMINKU, MUNA DA NAMU LIMAMIN.
SAI SUKA CE: A'A, ZAMU BI KA SALLAH. SAI SUKA BI SHI SALLAR. DA LOKACIN MAGARIBA YA YI KUSA SAI SUKA MATSO DA DAWAKINSU KUSA DA WAJEN HUSAINI (RA), DA YA GANSU, HAR YA 'DAN FARA BACCI, SAI YA CE MUSU; MEYE HAKA? SAI AKA CE; AI MATSOWA SUKA YI. SAI YA CE: KU JE KU CE MUSU ME SUKE NUFI??
SAI MUTUM 20 SUKA JE SUKA TAMBAYESU. SAI SUKA CE:
IMMA HUSAINI (RA) YA YARDA DA HUKUNCIN IBNU ZIYAD KO KUMA ZA A YAK'E SHI. SAI SUKA CE: TO KU BARI MU JE MU GAYA WA BABAN ABDULLAH (HUSAINI (RA). SAI SUKA KOMA SUKA GAYA MASA. SAI YA CE: KU CE MUSU; SU SAURARA MANA DAREN YAU DA GOBE, HAR IN SAMU IN YI SALLAH WA UBANGIJINA.
A WANNAN DAREN, SAI YA KWANA YANA TA SALLAH, YANA NEMAN GAFARA YANA ROK'ON ALLAH (T), YANA TA ADDU'O'I SHI DA SAURAN WA'DANDA SUKE TARE DA SHI.
MAI AUKUWA TA AUKU:
A RANAR JUMA'A DA SAFE YAK'I YA KAURE TSAKANIN 'BANGARORIN GUDA 2. SABODA HUSAINI (RA) YA K'I YA YARDA YA ZAMA KAMAMME ZUWA GA GWAMNAN IRAK'I UBAIDULLAHI BIN ZIYAD. AMMA SAI DAI K'ARFIN 'BANGARORIN YA BANBANTA MATUK'A. DON HAKA JAMA'AR HUSAINI (RA) BA SU DA WANI ABU DA ZA SU IYA YI WA RUNDUNAR IRAK'I. DON HAKA KAWAI BURINSU SHI NE; SU MUTU DON FANSAR HUSAINI (RA), HAKA AKA RINK'A KASHE SU 'DAYA BAYAN 'DAYA. SAI DA SUKA K'ARE GABA 'DAYA, SAURA HUSAINI (RA) SHI DA 'DANSA ALIYU ZAINUL ABIDINA (R). HAKA SUKA ZAUNA TSAWON WUNI, BABU WANDA ZAI ISO WAJENSA FACE YA KOMA DA BAYA, YANA TSORON KAR ALLAH YA JARABE SHI DA KASHE SHI.
ANA HAKA SAI GA SHAMRU 'DAN ZUL JAUSHAN YA ZO, SAI YA YI TSAWA WA MUTANE; KAITONKU, IYAYENKU SUN YI ASARAR HAIHUWARKU!!
KU KEWAYE SHI, KU KASHE SHI!!!
KAWAI SAI SUKA ZO SUKA KEWAYE SHI, AMMA HUSAINI (RA) YANA KARAWA DA SU DA TAKOBINSA, HAR YA KASHE WASU DAGA CIKINSU. SABODA YA KASANCE KAMAR ZAKI NE A CIKINSU. AMMA SAI DAI; SARKIN YAWA YA FI SARKIN K'ARFI.
SAI SHAMRU YA SAKE DAKA MUSU TSAWA; KAITONKU, ME KUKE JIRA??!!
KU AFKA MASA!!!
KAWAI SAI SUKA AFKA MASA, SAI SUKA KASHE SHI!!!
انا لله وانا إليه راجعون!!!
AN CE WANDA YA KASHE SHI DA HANNUNSA SHI NE SINAN BIN ANAS AL- NAKHA'IY, KUMA YA CIRE KANSA. WASU KUMA SUKA CE; SHAMRU NE.
ALLAH YA YI MUSU ABIN DA YA DACE DA SU!!!
BAYAN SUN KASHE SHI SAI SUKA 'DAUKI KANSA, SUKA TAFI DA SHI KUFA, WAJEN GWAMNA UBAIDULLAHI BIN ZIYAD. KAWAI SAI YA FARA TSOKALE MASA BAKI DA TSINKEN DAKE HANUNSA, YANA CEWA; YANA DA KYAKKYAWAN WUSHIRYA KUWA!!
SAI ANAS 'DAN MALIK (RA) YA CE: ALLAH WADAI DA WANNAN MUMMUNAN AIKI. WALLAHI NA GA MANZON ALLAH (SAW) YANA SUMBANTAR WAJEN DA KAKE SA WANNAN TSINKEN NAKA A BAKINSA.
DUBA FATHUL BARIY, A BABIN FALALAR HASAN DA HUSAINI (RA).
A BIYO MU A HANKALI, GASKIYA TA YI KUSA TA YI HALINTA. ZA A SHA MAMAKI; ANA TSAMMANIN WUTA A MAK'ERA SAI AKA SAMETA A MASAK'A.
No comments:
Post a Comment