BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
AN TAMBAYI IBNU TAIMIYYA (R) GAME DA FA'DIN AL- SHEIKH IBNU ABI ZAID, A K'ARSHEN AK'IDARSA:
وأن خير القرون القرن الذين رأوا رسول الله صلى الله عليه وسلم وآمنوا به ثم الذين يلونهم ثم الذين يلونهم . وأفضل " الصحابة " الخلفاء الراشدون المهديون أبو بكر وعمر وعثمان وعلي
MAFIFICIN K'ARNI SU NE K'ARNIN DA SUKA GA MANZON ALLAH (SAW), KUMA SUKA YI IMANI DA SHI. SAI WA'DANDA SUKE BIYE DA SU, SAI WA'DANDA SUKE BIYE DA SU. KUMA MAFIFICIN SAHABBAI KUWA SU NE KHULAFA'UR RASHIDUNA SHIRYAYYU; ABUBAKAR DA UMAR DA USMAN DA ALIYU.
TO, MENENE DALILI A KAN FIFITA ABUBAKAR A KAN UMAR, DA FIFITA UMAR A KAN USMAN, DA FIFITA USMAN A KAN ALIYU??
IDAN HAKAN YA BAYYANA, SHIN YA WAJABA A YI HORO GA WANDA YA FIFITA WANI WANDA AKA FI SHI A KAN MAFIFICI, KO KUMA A'A??KA YI MANA BAYANIN HAKAN, BAYANI MAI FA'DI, INSHA ALLAHU ZA KA SAMU LADA.
SAI IBNU TAIMIYYA (R) YA BA DA AMSA KAMAR HAKA:
GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN HALITTU.
AMMA FIFITA ABUBAKAR, SA'ANNAN UMAR A KAN USMANU DA ALIYU, WANNAN ABU NE DA AKA YI ITTIFAQI A KANSA A WAJEN MALAMAN MUSULMAI, WA'DANDA SUKA SHAHARA DA SHUGABANCI A ILMI DA ADDINI; A CIKIN SAHABBAI DA TABI'AI DA MABIYANSU. KUMA WANNAN SHI NE MAZHABAR IMAMU MALIK DA MUTANEN MADINA, DA LAITH 'DAN SA'AD, DA MUTANEN MISRA, DA AUZA'IY DA MUTANEN SHAAM, DA SUFYANU AL- THAURIY DA ABU HANIFA, DA HAMMAD 'DAN ZAID, DA HAMMAD 'DAN SALAMA, DA MAKAMANTANSU NA MUTANEN IRAQI. KUMA SHI NE MAZHABAR SHAFI'IY DA AHMAD, DA ISHAQ, DA ABU UBAID, DA WASUN WA'DANNAN CIKIN IMAMAN MUSLUNCI, WA'DANDA SUKE DA KYAKKYAWAN AMBATO A CIKIN AL'UMMA.
KUMA MALIK YA YI HIKAYAN IJAMA'IN MUTANEN MADINA A KAN HAKAN. YA CE:
ما أدركت أحدا ممن أقتدي به يشك في تقديم أبي بكر وعمر .
BABU WANI DA NA RISKA, DAGA CIKIN WA'DANDA NAKE KOYI DA SHI, WANDA YAKE SHAKKA WAJEN GABATAR DA ABUBAKAR DA UMAR.
WANNAN KUWA YA ZO TA HANYOYI MASU YAWA DAGA AMIRUL MUMININA ALIYU 'DAN ABI 'DALIB (RA). YA ZO A CIKIN SAHIHUL BUKHARI:
عن محمد بن الحنفية أنه قال لأبيه علي بن أبي طالب : يا أبت من خير الناس بعد رسول الله صلى الله عليه وسلم قال يا بني أوما تعرف قلت : لا . قال : أبو بكر . قلت : ثم من ؟ قال : عمر .
DAGA MUHAMMAD BIN HANAFIYYA, YA CE MA BABANSA ALIYU 'DAN ABI 'DALIB (RA): YA BABA, WANENE FIYAYYEN MUTANE BAYAN MANZON ALLAH (SAW)?
SAI YA CE: YA 'DANA, SHIN BA KA SANI BA?!
SAI NA CE: A'A.
SAI YA CE: ABUBAKAR.
SAI NA CE: SAI WA?
SAI YA CE: UMAR.
KUMA AN RUWAITO HAKAN DAGA ALIYU (RA) TA HANYOYI KUSAN 80; KUMA YANA FA'DIN HAKAN A KAN MIMBARIN KUFA. KAI, YA CE:
لا أوتى بأحد يفضلني على أبي بكر وعمر إلا جلدته حد المفتري . فمن فضله على أبي بكر وعمر جلد بمقتضى قوله - رضي الله عنه - ثمانين سوطا .
BABU WANDA ZA A KAWO MINI SHI YANA FIFITANI A KAN ABUBAKAR DA UMAR, FACE NA YI MASA BULALAN K'AZAFI.
DON HAKA, DUK WANDA YA FIFITA SHI A KAN ABUBAKAR DA UMAR, ZA A DAKA SHI; BULALA 80, A BISA WANNAR MAGANA TASA.
SUFYANU YA KASANCE YAKAN CE:
من فضل عليا على أبي بكر فقد أزرى بالمهاجرين ؛ وما أرى أنه يصعد له إلى الله عمل - وهو مقيم على ذلك .
DUK WANDA YA FIFITA ALIYU A KAN ABUBAKAR, HAK'IK'A YA CI MUTUNCIN AL- MUHAJIRUN. BA NA GANIN WANI AIKINSA ZAI 'DAGU ZUWA GA ALLAH, ALHALI YANA KAN HAKAN.
TIRMIZIY DA WANINSA YA CE:
روي هذا التفضيل : عن النبي صلى الله عليه وسلم وأنه قال : " { يا علي هذان سيدا كهول أهل الجنة من الأولين والآخرين ؛ إلا النبيين والمرسلين }
AN RUWAITO WANNAN FIFIKON DAGA ANNABI (SAW) YA CE: YA KAI ALIYU, WA'DANNAN BIYUN SHUGABANNIN MAZAJEN 'YAN ALJANNA NE, TUN DAGA NA FARKO HAR NA K'ARSHE, SAI DAI ANNABAWA DA MANZANNI KAWAI.
YA ZO TA HANYOYI MASU YAWA A CIKIN SAHIHAINI DA WASUNSU DAGA ANNABI (SAW), TA FISKOKI DABAN - DABAN, A HADISIN ABU SA'EED, IBNU ABBAS, JUNDUB 'DAN ABDULLAH, DA 'DAN ZUBAIR DA WASUNSU:
أن النبي صلى الله عليه وسلم قال " { لو كنت متخذا من أهل الأرض خليلا لاتخذت أبا بكر خليلا ولكن صاحبكم خليل الله }
LALLAI ANNABI (SAW) YA CE: DA NA KASANCE ZAN RIK'I BADA'DE A CIKIN MUTANEN DUNIYA, DA NA RIK'I ABUBAKAR A MATSAYIN BADA'DENA. SAI DAI MUTUMIN NAKU BADA'DEN ALLAH NE.
YANA NUFIN SHI KANSA.
A CIKIN HADISI SAHIHI YA FA'DA A KAN MIMBARI:
{ إن أمن الناس علي في صحبته وذات يده . أبو بكر ؛ ولو كنت متخذا من أهل الأرض خليلا لاتخذت أبا بكر خليلا ولكن صاحبكم خليل الله . ألا لا يبقين في المسجد خوخة إلا سدت إلا خوخة
أبي بكر } .
LALLAI MAI FALALA A KAINA DAGA CIKIN MUTANE A ABOKANTAKARSA DA NI DA KUMA ABIN HANUNSA (DUKIYARSA) SHI NE ABUBAKAR. DA ZAN RIK'I WANI A MATSAYIN BADA'DE (CIKAKKEN MASOYIN DA BA SHI DA ABOKIN TARAYYA) DAGA MUTANEN DUNIYA DA NA RIK'I ABUBAKAR A MATSAYIN BADA'DENA. SAI DAI MUTUMIN NAKU BADA'DEN ALLAH NE. KAR A BAR WATA K'OFA TA SAURA A MASALLACI FACE AN RUFETA, SAI DAI K'OFAR ABUBAKAR.
WANNAN A FILI YAKE CEWA; BA SHI DA WANDA YA CANCANCI MATSAYIN BADA'DE A CIKIN MUTANEN DUNIYA, DA HAKAN ZAI YIWU A CIKIN HALITTA, TO DA ABUBAKAR (RA) NE. TO SAI AKA SAN CEWA; BABU WANI MAFIFICI A WAJENSA, KUMA MAFI SOYUWA A WAJENSA KAMAR ABUBAKAR (RA).
HAKA YA ZO A SAHIHIN HADISI; YA CE:
{ قال عمرو بن العاص : أي الناس أحب إليك ؟ قال : عائشة . قال : فمن الرجال ؟ قال : أبوها } .
AMRU 'DAN AAS YA CE: WANE MUTUM NE YA FI SOYUWA A GAREKA?
SAI YA CE: A'ISHA.
YA CE: A MAZA FA?
SAI YA CE: BABANTA.
HAKA YA ZO A INGANTACCEN HADISI, YA CE MA A'ISHA (RA):
{ ادعي لي أباك وأخاك حتى أكتب لأبي بكر كتابا لا يختلف عليه الناس من بعدي ثم قال يأبى الله والمؤمنون إلا أبا بكر } .
KI KIRA MINI BABANKI DA 'DAN UWANKI DON IN RUBUTA MA ABUBAKAR TAKARDA, DON KAR MUTANE SU SA'BA MASA A BAYANA. SAI ANNABI (SAW) YA CE: ALLAH DA MUMINAI ZA SU K'I KOWA SAI ABUBAKAR.
YA ZO A SAHIHIN HADISI:
{ أن امرأة قالت يا رسول الله : أرأيت إن جئت فلم أجدك - كأنها تعني الموت - قال : فأتي أبا بكر }.
WATA MATA TA CE: YA MANZON ALLAH (SAW), ME KAKE GANI IN NA ZO BAN SAMEKA BA? - KAMAR MUTUWA TAKE NUFI -.
SAI YA CE: KI ZO WAJEN ABUBAKAR.
YA ZO A CIKIN SUNAN YA CE:
{ اقتدوا باللذين من بعدي أبي بكر وعمر }
KU YI KOYI DA MUTANE BIYU, WA'DANDA SUKE BAYANA; ABUBAKAR DA UMAR.
A CIKIN SAHIHIN HADISI, YANA HALIN TAFIYA, SAI YA CE:
{ إن يطع القوم أبا بكر وعمر يرشدوا } .
IN MUTANEN SUN YI BIYAYYA WA ABUBAKAR DA UMAR, TO ZA SU DACE.
YA ZO A SUNAN YA CE:
{ رأيت كأني وضعت في كفة والأمة في كفة فرجحت بالأمة ثم وضع أبو بكر في كفة والأمة في كفة فرجح أبو بكر ثم وضع عمر في كفة والأمة في كفة فرجح عمر } .
NA GA NI, (A MAFARKI) AN 'DORANI A HANUN SIKELI 'DAYA, AL'UMMATA AN 'DORASU A 'DAYA HANUN, SAI NA RINJAYI AL'UMMAR. SA'ANNAN SAI AKA 'DORA ABUBAKAR A HANU 'DAYA, AKA 'DORA AL'UMMA A HANU 'DAYAN, SAI ABUBAKAR YA RINJAYI AL'UMMA. SAI AKA 'DORA UMAR A HANU 'DAYA, AL'UMMA A 'DAYA HANUN SAI UMAR YA RINJAYA.
A CIKIN HADISI SAHIHI:
{ كان بين أبي بكر وعمر كلام فطلب أبو بكر من عمر أن يستغفر له فلم يفعل . فجاء أبو بكر إلى النبي صلى الله عليه وسلم فذكر ذلك . فقال : اجلس يا أبا بكر يغفر الله لك وندم عمر فجاء إلى منزل أبي بكر فلم يجده فجاء إلى النبي صلى الله عليه وسلم فغضب النبي صلى الله عليه وسلم . وقال : أيها الناس إني جئت إليكم فقلت : إني رسول الله فقلتم : كذبت وقال أبو بكر صدقت . فهل أنتم تاركو لي صاحبي ؟ فهل أنتم تاركو لي صاحبي ؟ فهل أنتم تاركو لي
صاحبي ؟ فما أوذي بعدها }
SA'BANI YA SHIGA TSAKANIN ABUBAKAR DA UMAR, SAI ABUBAKAR YA NEMI UMAR DA YA YAFE MASA, SAI UMAR YA K'I. SAI ABUBAKAR YA ZO WAJEN ANNABI (SAW) SAI YA GAYA MASA. SAI YA CE: ABUBAKAR KA ZAUNA, ALLAH ZAI GAFARTA MAKA. SAI UMAR YA YI NADAMA, SAI YA ZO GIDAN ABUBAKAR, SAI BAI SAME SHI BA. SAI YA ZO WAJEN ANNABI (SAW) SAI ANNABI (SAW) YA YI FUSHI. SAI YA CE: YAKU MUTANE! NA ZO GAREKU, NA CE: NI MANZON ALLAH NE, SAI KUKA CE: K'ARYA KAKE YI, SAI ABUBAKAR YA CE: KA YI GASKIYA.
YANZU ZA KU BAR MINI ABOKINA??!!
YANZU ZA KU BAR MINI ABOKINA??!!
YANZU ZA KU BAR MINI ABOKINA??!!
BAYAN WANNAN BA A SAKE CUTAR DA SHI BA.
HADISI YA ZO MUTAWATIRI A CIKIN SAHIHI DA SUNAN; ANNABI (SAW) YA YI RASHIN LAFIYA, SAI YA CE:
{ مروا أبا بكر فليصل بالناس : مرتين أو ثلاثا حتى قال : إنكن لأنتن صواحب يوسف مروا أبا بكر أن يصلي بالناس } .
KU UMURCI ABUBAKAR YA YI SALLAH WA MUTANE. YA FA'DA SAU 2 KO SAU 3. HAR YA CE: LALLAI KU 'DIN NAN KAMAR MATAN ZAMANIN YUSUF NE, NA CE: KU UMURCI ABUBAKAR YA YI SALLAH WA MUTANE.
TO, WANNAN KE'BANCEWA DA KUMA MAIMAITAWAN, DA K'ARFAFAWAN; A GABATAR DA SHI A LIMANCI A KAN SAURAN SAHABBAI, DUK DA CEWA; UMAR YANA NAN, USMAN YANA NAN, ALIYU YANA NAN, DA SAURANSU, YANA BAYYANA WA AL'UMMA YADDA (ANNABI) YAKE GABATAR DA SHI A WAJENSA (SAW) A KAN WANINSA.
A CIKIN SAHIH:
{ أن جنازة عمر لما وضعت جاء علي بن أبي طالب يتخلل الصفوف ثم قال : لأرجو أن يجعلك الله مع صاحبيك فإني كثيرا ما كنت أسمع النبي صلى الله عليه وسلم يقول : دخلت أنا وأبو بكر وعمر وخرجت أنا وأبو بكر وعمر وذهبت أنا وأبو بكر وعمر } .
LOKACIN DA AKA AJIYE GAWAR UMAR, ALIYU 'DAN ABI 'DALIB YA ZO YANA RATSA SAFU. SA'ANNAN YA CE: INA FATAN ALLAH YA SANYAKA TARE DA ABOKANKA GUDA 2, SAU DA YAWA NAKAN JI ANNABI (SAW) YANA CEWA; NA SHIGA NI DA ABUBAKAR DA UMAR, NA FITA NI DA ABUBAKAR DA UMAR, NA TAFI NI DA ABUBAKAR DA UMAR.
WANNAN YANA NUNA LIZIMTARSU NE GA ANNABI (SAW) A WAJEN SHIGANSA DA FITANSA DA TAFIYANSA. SABODA HAKA NE IMAMU MALIK YA CE MA HARUNA RASHID, A LOKACIN DA YA CE MASA:
يا أبا عبد الله أخبرني عن منزلة أبي بكر وعمر : من النبي صلى الله عليه وسلم ؟ فقال : يا أمير المؤمنين منزلتهما منه في حياته كمنزلتهما منه بعد وفاته فقال شفيتني يا مالك
YA BABAN ABDULLAH, BA NI LABARIN MATSAYIN ABUBAKAR DA UMAR A WAJEN ANNABI (SAW)?
SAI YA CE: YA AMIRUL MUMININA, MATSAYINSU A WAJENSA A LOKACIN RAYUWARSA, KAMAR MATSAYINSU A WAJENSA BAYAN MUTUWARSA. (MA'ANA; SUNA KWANCE A WAJE 'DAYA. KABARINSU SU 3 A WAJE 'DAYA)
SAI YA CE: MALIK, KA WARKAR DA NI.
WANNAN YANA BAYYANA CEWA; ABIN DA YA KASANCE SUNA DA SHI NA KE'BANTUWANSU DA TARAYYA DA SHI, DA TAIMAKONSU GARE SHI A KAN LAMURANSA, DA ZAMOWANSU ABOKAN SIRRINSA, ABU NE DA DOLE YA SAN DA SHI, DUKKAN WANDA YA SAN HALIN ANNABI (SAW) DA MAGANGANUNSA DA AIYUKANSA DA TARIHINSA TARE DA SAHABBANSA. SABODA HAKA NE BABU WANI DA YA YI JAYAYYA A KAN HAKAN DAGA CIKIN MASU ILMIN TARIHINSA DA SUNNARSA DA HALAYENSA. KAWAI WANDA YAKE KORE WANNAN KO YAKE TARADDUDI A KANSA, SHI NE WANDA BA SHI DA ILMIN HAK'IK'ANIN AL'AMURAN ANNABI (SAW). KO DA KUWA YANA DA 'DAN KASO A ILMUL KALAM, KO ILMIN FIK'HU, KO ILMIN HISABI, KO WANIN HAKAN. KO KUMA WANDA YA JI HADISAN K'ARYA, WA'DANDA SUKE WARWARE ABUBUWAN DA SANANNU NE A BISA DOLE, A WAJEN KE'BANTATTUN MASU ILMI, AMMA SAI YA YI TARADDUDI A LAMARIN, KO KUMA YA RINJAYAR DA WANIN ABUBAKAR. WANNAN KUWA KAMAR SAURAN ABUBUWAN DA SUKE SANINSU NA DOLE NE A WAJEN MASU ILMIN SUNNAR MANZON ALLAH (SAW), DUK DA CEWA; WANINSU ZAI YI SHAKKA A CIKINSU KO YA KORESU....
DUBA MAJMU'UL FATAWA 4/ 421 - 425.
AKWAI CIGABA, SAI A BIYO MU A HANKALI.
A WANNAN BAYANIN, MAI KARATU YA FAHIMCI CEWA; ABUBAKAR (RA) DA UMAR (RA) SUN FI KOWA A CIKIN SAHABBAN ANNABI (SAW), AMMA ABUBAKAR (RA) YA FI UMAR (RA) FALALA. DON HAKA ABUBAKAR (RA) YA FI KOWA FALALA DA MATSAYI DA DARAJA A BAYAN MANZON ALLAH (SAW).
ALLAH YA SA MU DACE!!
No comments:
Post a Comment