Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Thursday, 25 February 2016

YAYE SHUBUHA A KAN ABUBAKAR (RA) (1)


(1) Shiatu Ali YA CE:
KUMA ALLAH (SWT) BAI TABA AIKO DA SAUKONSA BA FACE TA HANNUN WANI MA’ASUMI WANDA ZAI BADA CIKAKKIYAR FASSARA DA MISALIN YADDA ZA’A DABBAQA UMARNIN ALLAH (SWT).

AMMAR:
WA KAKE NUFI DA "MA'ASUMI" A CIKIN WANNAR MAGANA TAKA??
IN ANNABI MANZO KAKE NUFI, TO LALLAI MAGANARKA HAKA TAKE. ALLAH NE YA CE:
وما أرسلنا من رسول إلا بلسان قومه ليبين

"BA MU AIKO WANI MANZO BA FACE DA YAREN (LUGA) MUTANENSA DON YA YI MUSU BAYANI (NA SAK'ON ALLAH).
IN KUMA IMAMIN SHI'A KAKE NUFI SHI NE MA'ASUMI, TO SAI MU CE MAKA: KA KAWO MANA DALILI, NASSI A FILI INDA AKA FA'DI HAKAN??!

(2) SHI'ATU YA CE:
KUMA ALLAH (SWT) BAI TABA BAIWA WATA AL’UMMA ZABI BA AKAN KANTA WAJEN ZABAWA KANTA WANDA ZAI JAGORANCETA WAJEN ISAR DA SAKON ALLAH (SWT). DOMIN KUWA ALLAH YAFI SANIN INDA YA KAMATA YA AJIYE SAKONSA

AMMAR:
ME KAKE NUFI DA "JAGORA"??
IN MANZO KAKE NUFI TO LALLAI HAKA NE. KAMAR YADDA KA KAWO AYA, ALLAH YA CE:
الله أعلم حيث يجعل رسالته

AMMA IN KHALIFA KAKE NUFI, TO SAI MU CE MAKA:
INA DALILI A KAN CEWA; BA A TA'BA BAI WA AL'UMMA ZA'BIN KHALIFA BA??!
SABODA ITA WANNAR AYAR DA KA KAWO:
الله أعلم حيث يجعل رسالته

BA DALILI BA CE A KAN MAGANARKA, ITA A KAN MANZANCI TAKE MAGANA BA A KAN KHALIFANCI BA.
AMMA ITA KUMA AYA TA 2 DA KA KAWO:
وقال لهم نبيهم إن الله قد بعث لكم طالوت ملكا قالوا أنى يكون له الملك علينا ونحن أحق بالملك منه ولم يؤت سعة من المال قال إن الله اصطفاه عليكم وزاده بسطة في العلم والجسم والله يؤتي ملكه من يشاء والله واسع عليم

TANA MAGANA NE A KAN SHUGABAN DA ALLAH YA ZA'BA, AMMA SAI MUTANEN SUKA YI JAYAYYA BAYAN ALLAH NE YA ZA'BA MUSU SHI:
قالوا أنى يكون له الملك علينا ونحن أحق بالملك منه ولم يؤت سعة من المال

DON HAKA, AYAR BA TA NUNA WAJABCIN SAMUWAR NASSI A KAN SHUGABANCI, IN KUMA KA CE BA HAKA BA NE, TO SAI MU CE MAKA:
INA NASSI (K'ARARA) A KAN KHALIFAN DA ALLAH YA ZA'BA A BAYAN MANZON ALLAH (SAW)??!

(3) SHI'ATU YA CE:
ALLAH (SWT) NE TA HANNUN MANZANNINSA YAKE ZABAN JAGORORI KO DA KUWA ZABINSA YA SABAWA ABINDA MAFIYAWAN JAMA’A KE SO.

AMMAR:
WANNAR MAGANA NA YI TAMBAYA A BAYA A KANTA KAMAR HAKA:
INA NASSI (SARIHI) A KAN KHALIFAN DA ALLAH YA ZA'BA A BAYAN MANZON ALLAH (SAW)??!

• MALAM SHI'ATU, KAR KAMANTA CEWA; DUK ABIN DA KA FA'DA WANDA YAKE BUK'ATAR DALILI K'ARARA, AMMA SAI MUKA RASA DALILIN, TO WANNAR MAGANA K'ARYA CE.

(4) SHI'ATU YA CE:
ALLAH (SWT) YA FADA MANA A CIKIN AL-QUR’ANI MAI TSARKI CEWA SHI (QUR’AN) LITTAFI NE TSARARRE WANDA BA MAI SHAFARSA SAI TSARKAKAKKU (WAQI’A: 77-79):
إِنَّهُ لَقُرْءَانٌ كَرِيمٌ * فِى كِتَـبٍ مَّكْنُونٍ * لاَّ يَمَسُّهُ إِلاَّ الْمُطَهَّرُونَ
ASHE WANNAN BAYA NUNAR DA CEWA TSARKAKAKKU SU SUKA FI KOWA FAHIMTAR MA’ANAR AL-QUR’ANI?

AMMAR:
MENENE MA'ANAR KALMAR:
المطهرون

A CIKIN AYAR DA KA KAWO?!
TSARKAKKUN DA AKE NUFI A CIKIN AYAR, MALA'IKU AKE NUFI BA MUTANE BA. MALA'IKU NE MASU TA'BA LITTAFIN DA YAKE SAMA, WANDA AL- QUR'ANI YAKE CIKINSA. WATO "LAUHUL MAHFUZ" KENAN.
YA KAMATA KA KULA DA MA'ANAR AYAR, BA TANA MAGANA BA NE A KAN AL- QUR'ANI, A'A, TANA MAGANA NE A KAN "KITABUN MAKNUN" WATO SHI NE "LAUHUL MAHFUZ", SHI NE WANDA BABU MAI SHAFARSA SAI TSARKAKAKKU.
AL- SHERAZIY A CIKIN TAFSIRINSA (TABYINUL QUR'AN) YA CE:
{ في كتاب } في اللوح المحفوظ { مكنون } مصون لا تمسه يد التغيير.
{ لا يمسه إلا المطهرون } من الملائكة، أو من تطهر عن الحدث من البشر.

ALMAJLISIY A CIKIN AL- BIHAR YA KAWO KAMAR HAKA:
" في كتاب مكنون " مصون وهو اللوح " لا يمسه إلا المطهرون " لا يطلع على اللوح إلا المطهرون من الكدورات الجسمانية وهم الملائكة، أو لا يمس القرآن إلا المطهرون من الأحداث.

DUKA SUN AMBACI TAFSIRI GUDA 2; NA FARKO YA NUNA CEWA; AYAR TANA MAGANA NE A KAN MALA'IKU. NA 2; YA NUNA CEWA; TANA MAGANA NE A KAN MUTANE. TO WANNE TAFISIRI NE YA FI DACEWA?
AMSA; SHI NE NA FARKO. SABODA ITA WANNAR AYAR:
لا يمسه إلا المطهرون

KOMAWAN LAMIRIN DA YAKE JIKIN:
يمسه

YA FI DACEWA DA YA KOMA ZUWA GA:
كتاب مكنون

SABODA SHI NE SUNA NA KUSA DA SHI. K'A'IDA A LARABCI KUWA ITA CE:
الضمير يعود إلى أقرب مذكور.
DA WANNAN YA TABBATA CEWA; AYAR TANA MAGANA CE A KAN MALA'IKU, SU NE TSARKAKAKKUN DA AKE NUFI A CIKIN AYAR, BA MUTANE BA. SABODA:
كتاب مكنون

SHI NE "LAUHUL MAHFUZ" WANDA YAKE CAN SAMA.

No comments:

Post a Comment