** KOWA YA SANI, ANNABI (SAW) KAFIN YA RASU SAI DA YA YI RASHIN LAFIYAN CIWON AJALI, WANDA HAR TA KAI GA BA YA IYA FITOWA YA JA JAMA'A SALLAH A MASALLACINSA, WANDA HAKAN YA SA YA UMURCI SAYYIDINA ABUBAKAR (RA) DA YANA JAN MUTANE SALLAH, HAR ZUWA RANAR DA YA KOMA GA RAHAMAR UBANGIJINSA.
*** TO A NAN AKWAI ABUBUWAN TAMBAYA MASU YAWA, AMMA ZAMU TAK'AITA NE A KAN WASU DAGA CIKINSU KAWAI, GA SU KAMAR HAKA:
(1) IN YA TABBATA ALLAH YA SAUK'AR DA NASSI A KAN IMAMANCIN ALIYU (RA), KUMA ANNABI YA NA'DA SHI A MATSAYIN SHUGABA, KHALIFANSA A RANAR GHADEER KHUM, DON ME YA SA ANNABI (SAW) BAI BA WA ALIYU (RA) LIMANCIN SALLAH WA MUTANE A CIWONSA NA AJALI BA. DON YA KAMATA KHALIFANSA YA ZAMA NA'IBINSA A LIMANCI??
(2) IN ANNABI (SAW) YA SAN GAIBU, TO DOLE YA SAN CEWA; ABUBUAKAR (RA) ZAI YI RIDDA - KAMAR YADDA 'YAN SHI'A SUKE RAYAWA -, TO DON ME YA SA ANNABI (SAW) ZAI NA'DA WANDA ZAI YI MUMMUNAR K'ARSHE A MATSAYIN LIMAMI WA MUTANE, KUMA NA'IBINSA, ALHALI AKWAI WANDA YA FI SHI, WATO ALIYU (RA), SHUGABA NA ASALI, KUMA MA'ASUMI, KUMA MASANIN GAIBI??
**** INA KIRA ZUWA GA MASU HANKALI A CIKIN 'YAN SHI'A, IN KA GA IRIN WA'DANNAN TAMBAYOYIN, DON ALLAH AJIYE TA'ASSUBANCI A GEFE, KAR KA CE; AI BAWAHABIYE NE YA YI WANNAR TAMBAYAR, KA TSAYA KA YI TSAM A RANKA, KA AUNA DA HANKALINKA, YI K'OK'ARIN BA MA KANKA GAMSASSHIYAR AMSA MAI 'YANCI. SA'ANNAN NATIJAR DA KA SAMU SAI KA YI K'OK'ARIN GAMSAR DA MU DA ITA.
ALLAH YA SA MU DACE GABA 'DAYA.
TO 'YAN SHI'A GAREKU....
No comments:
Post a Comment