Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Saturday, 6 February 2016

TATTAUNAWA TSAKANIN 'DAN SHI'A DA 'BARAWO A KAN KHALIFANCIN ALIYU (RA) DA FIFITA SHI A KAN SAURAN SAHABBAI (1)


AKWAI WANI ALKALI 'DAN SHI'A MAI SUNA MUHAMMAD BN HUSSAIN, YA KASANCE YANA FITA SHAK'ATAWA ZUWA LAMBUNSA DA ASUBA, WATA RANA YA FITA KAWAI SAI WANI 'BARAWO YA DIRO MASA, YA BUGI K'IRJINSA YA SHAK'E SHI, YA 'DORA MASA SHAR'BE'BIYAR WUK'A A WUYANSA SAI YA CE MASA:
"TU'BE MINI DUKKAN KAYAN JIKINKA".

BAYAN DOGUWAR TATTAUNAWA DA TA GUDANA A TSAKANINSU, SAI YA FARA TU'BE KAYAN NASA, TO YA TU'BE WANDONSA YANA MIK'A MASA KAWAI SAI YA GA ZOBE A HANUNSA NA DAMA, SAI 'BARAWON YA CE: "CIRO ZOBEN KA KAWO SHI".

BAYAN SUN TATTAUNA A KAN ZOBEN, SAI 'BARAWON YA CE MASA:
"DON ME YA SA KA SA ZOBE A HANUN DAMA, ALHALI HAKAN ALAMA CE TA WA'DANDA SUKA SA'BA MANA A RA'AYI".

ALKALI YA CE:
SHIN BA HALAL BA NE?

'BARAWO YA CE:
EH HALAL NE, AMMA SAI DAI SA ZOBE A HANUN DAMA YA ZAMA ALAMA TA WA'DANDA SUKA SA'BA, SAI YA KASANCE DA SHI AKE BANBANCE TSAKANIN MUTANENMU DA WA'DANDA SUKA SA'BA MANA.

ALKALI YA CE:
IN KANA NUFIN SA'BANIN MAZHABA NE, TO SA ZOBE A DAMA BABU LAIFI A WAJEN SHUGABAN MAZHABARMU (SHAFI'IY).

'BARAWO YA CE:
A'A, INA NUFIN SA'BANIN RA'AYI TSAKANIN AHLUS SUNNA DA RAFIDHA 'YAN SHI'A.

ALKALI YA CE:
NI NA YI IMANI DA WILAYAR AMIRUL MUMININA ALIYU BN ABI 'DALIB (AS), KUMA INA FIFITA SHI A KAN SAURAN MUSULMAI, AMMA BA TARE DA SUKA DA AIBANTA MAGABATA SHIRYAYYU BA, KUMA BA TARE DA BARIN SUNNONI DA BIN ADDINI BA. WANNAN SHI NE TUSHEN AQIDATA, A HUKUNCI KUMA INA BIN MAZHABAR SHAFI'IY NE, KUMA A KANTA SAURAN MUTANEN GARINMU SUKE.

'BARAWO YA CE:
MADALLA DA MAZHABAR DA KAKE BI.
TO AMMA, IDAN WANI YA YI MAKA JAYAYYA, YA CE MAKA: DA WANE ABU ALIYU (RA) YA CANCANCI A FIFITA SHI A KAN SAURAN MUSULMAI, HAR YA ZAMA YA FI KOWA FALALA A BAYAN MANZON ALLAH (SAW), ME ZA KA CE?

ALKALI YA CE:
AMSA A KAN HAKA ITA CE; ALIYU (AS) SHI YA CANCANCI A FIFITA SHI A KAN KOWA CIKIN SAHABBAI DA AHLUL BAITI, SABODA YA FI KUSACIN DANGANTAKA DA ANNABI (SAW), KUMA SHI SURUKINSA NE, KUMA SHI DA MANZON ALLAH (SAW) RASSA NE GUDA BIYU DAGA BISHIYA GUDA.

'BARAWO YA CE:
WANNAN SHI NE ABIN DA YA SA YA ZAMA YA FI KOWA A CIKIN ALMUHAJIRUNA?

ALKALI YA CE:
EH WANNAN NE.

'BARAWO YA CE:
TO AI IN HAKA NE ABBAS (RA) YA FI SHI FALALA, SABODA YA FI ALIYU (RA) KUSACIN DANGANTAKA DA ANNABI (SAW), SABODA ALLAH YA CE:
{وأولوا الأرحام بعضهم أولى ببعض في كتاب الله}

"MA'ABOTA DANGANTAKA SASHENSU YA FI CANCANTA DA SASHE A LITTAFIN ALLAH".
KUMA MUSULMAI SUN YI IJMA'I A KAN CEWA; DA MUTUM ZAI MUTU YA BAR BAFFANSA DA 'DAN BAFFANSA, DA BAFFAN NASA NE ZAI GAJI DUKIYARSA BA 'DAN BAFFAN BA, BA TARE DA WANI SA'BANI BA.

ALKALI YA CE:
AI SHI ABBAS (RA) BAI YI HIJIRA BA, SHI KUMA ALIYU (RA) YA YI HIJIRA?

'BARAWO YA CE:
TO SHI KENAN FIFITA ALIYU (RA) SABODA DANGANTAKARSA DA ANNABI (SAW) TA RUSHE, YA ZAMA YA FISU NE SABODA HIJIRA BA SABODA DANGANTAKA BA KENAN?

ALKALI YA CE:
EH HAKA NE.

'BARAWO YA CE:
TO IN HAKA NE AI JA'AFAR BN ABI 'DALIB (RA) MA YA YI HIJIRA, KUMA SHI MA 'DAN BAFFAN ANNABI (SAW) NE, DON HAKA IN WANI YA YI MAKA JAYAYYA YA CE; JA'AFAR (RA) YA FI ALIYU (RA) FALALA WACCE AMSA ZA KA BA SHI?

ALKALI YA CE:
SHI ALIYU (RA) BAI TA'BA YIN SHIRKA MA ALLAH (T) BA, KO SAU 'DAYA, KUMA BA A TA'BA SAMUNSA DA K'ARYA KO KARYA ALKAWARI BA, KUMA YA RIGA SHI YIN IMANI SHI DA ABBAS (RA) DUKANSU.

'BARAWO YA CE:
TO IN HAKA NE ABUBAKAR (RA) YA RIGASU IMANI DUKKANSU.

ALKALI YA CE:
AI ABUBAKAR (RA) DAGA SHIRKA YA KOMA MUSLUNCI.

'BARAWO YA CE:
SHIN A WAJENKU WANDA BAI TA'BA SHIRKA BA YA FI MUSULMIN DA YA TA'BA YIN SHIRKA A BAYA FALALA?

ALKALI YA CE:
EH HAKA NE.

'BARAWO YA CE:
TO A WAJENKU WACECE TA FI FALALA; A'ISHA (RA) KO KHADIJA (RA), KO KUMA WASUNSU DAGA CIKIN MATAN ANNABI (SAW) WA'DANDA BA SU TA'BA YIN SHIRKA BA?

ALKALI YA CE:
KHADIJA (RA) TA FI FALALA.

'BARAWO YA CE:
TO IN HAKA NE HUJJAR FIFITA ALIYU (RA) SABODA YA RIGA IMANI TA RUSHE, SABODA A BISA K'A'IDARKU DOLE A'ISHA (RA) TA FI KHADIJA (RA) FALALA, DON A'ISHA (RA) BA TA TA'BA YIN SHIRKA BA, KHADIJA (RA) KUWA TA YI SHIRKA A BAYA.

ALKALI YA CE:
SAI DAI KUMA SHI ALIYU (AS) TARE DA RIGA IMANI DA YA YI, YANA DA HA'DUWAR DANGANTAKA DA ANNABI (SAW).

'BARAWO YA CE:
DON HAKA DUK WANDA YA FI KUSACI DA ANNABI (SAW) YA FI FALALA KENAN?

ALKALI YA CE:
EH HAKA NE.

'BARAWO YA CE:
TO IN HAKA NE FATIMA (RA) CE TA FI KUSACI ZUWA GA ANNABI (SAW) KO ALIYU (RA)?

ALKALI YA CE:
FATIMA (RA) TA FI KUSACI DA SHI.

'BARAWO YA CE:
TO IN HAKA NE HUJJAR FIFITA ALIYU (RA) DA FIN KUSACI DA ANNABI (SAW) TA RUSHE.

ALKALI YA CE:
AI ALIYU (AS) YA RIGA FATIMA (AS) YIN IMANI, KUMA YA YI JIHADI.

'BARAWO YA CE:
TO AI IN HAKA NE, ABUBAKAR (RA) YA RIGA ALIYU (RA) YIN IMANI, KUMA SHI MA YA YI JIHADIN, SABODA SHI NE FARKON WANDA YA YI IMANI DA ALLAH (T), KUMA YA YI JIHADI, KUMA YA RIGA KOWA GASKATA ANNABI (SAW), KUMA YA TAIMAKI ANNABI (SAW) A LOKACIN DA BABU WANI MAI TAIMAKONSA DAGA CIKIN IYALAN GIDANSA DA DANGINSA DA ABOKANSA, KUMA SHI NE FARKON WANDA YA RIGA KOWA AMSA KIRANSA, KUMA YA KIRA MUTANE ZUWA GA YI MASA MUBAYA'A, KUMA YA BA DA DUKIYARSA DON TAIMAKON ADDINI".

KU BIYOMU A KASHI NA BIYU DA IZNIN ALLAH TA'ALA.

No comments:

Post a Comment