Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Saturday, 6 February 2016

TATTAUNAWA TSAKANIN 'DAN SHI'A DA 'BARAWO A KAN KHALIFANCIN ALIYU (RA) DA FIFITA SHI A KAN SAURAN SAHABBAI (2)


CIGABA DA TATTAUNAWAR KAMAR HAKA:

ALKALI YA CE:
TA YAYA ZA ACE; ABUBAKAR (RA) YA RIGA ALIYU (AS) YIN IMANI ALHALI SHI DA KANSA YANA FA'DAN CEWA; YANA DA WANI SHE'DANI DA YAKE BIJIRO MASA?

'BARAWO YA CE:
YA FA'DI HAKA, AMMA KUMA AI YA FA'DA NE A CIKIN TARON ALMUHAJIRUNA DA ANSAR, AMMA SAI DAI HAR YAU A DORON K'ASA BA A TA'BA SAMUN WANI MAI HANKALI DA YA CE WA ABUBAKAR (RA) MAHAUKACI BA, DA KUWA YA KASANCE A BISA HALIN SHAFAN ALJANI DA LAMARINSA BAI 'BUYA WA SAHABBAI DA AHLUL BAITI BA, DA BA SU BAR SHI YA YI KHALIFANCI BA, DA SUN KAFA HUJJA DA CEWA; SHI MAHAUKACI NE, YANA BUK'ATAR A KAI SHI WAJEN MAGANI, A MAIMAKON A BAR SHI YA YI SHUGABANCIN AL'UMMA DA KHALIFANCIN ANNABI (SAW). DON HAKA WANNAN WAUTA NE DA JAHILCI GA DUK WANDA YA FA'DI HAKA, SABODA YA MAYAR DA ALIYU (RA) DA SU AHLUL BAITIN MAHAUKATA, SABODA SUN ZURA IDO WA MAHAUKACI YA SHUGABANCESU, SAI DUKA SU ZAMA MAHAUKATA KENAN!
ALLAH YA TSARESU DA HAKA GABA 'DAYANSU.
KAWAI SHI DAI YA FA'DI HAKA NE SABODA ANNABI (SAW) YA CE:

«ما منكم من أحد إلا وله شيطان»، قالوا: ولك يا رسول الله؟ قال: «ولي، إلا أن الله أعانني عليه فأسلم».
صحيح ابن حبان (14/ 326)
"BABU WANI DAGA CIKINKU FACE YANA DA SHE'DANI", SAI SUKA CE: KAI MA KANA DA SHI YA MANZON ALLAH?
SAI YA CE: "NI MA INA DA SHI, SAI DAI ALLAH YA TAIMAKENI A KANSA SAI YA MUSULUNTA".

SHIN BA KA GA ANNABI (SAW) YA BA DA LABARIN YANA DA SHE'DANI BA?! ALLAH YA KIYAYE ACE; YANA DA HAUKA.
TO KAWAI ABUBAKAR (RA) YA FA'DI HAKA NE DON MUTANE SU NISANCI YIN AIKI DA ABIN DA YA YI KUSKURE A CIKINSA.

ALKALI YA CE:
SHIN MUTUMIN NAKU BAI CE:
«وليتكم ولست بخيركم؟».
"NA SHUGABANCEKU, AMMA BA NI NE MAFIFICINKU BA"?

'BARAWO YA CE:
WANNAR MAGANA TANA DA MA'ANONI, DAGA CIKI:
1- YA FA'DI HAKA NE YANA KAFA HUJJA WA ANSAR, SABODA YA CE: NA JAGORANCEKU A SALLAH, ALHALI MANZON ALLAH (SAW) YANA NAN.
NA RANTSE DA ALLAH BA ZAI YIWU ABUBAKAR (RA) YA ZAMA MAFIFICIN MUTANEN DA AKWAI MANZON ALLAH (SAW) A CIKINSU BA, DON HAKA KAMAR CEWA YA YI:
"TA YAYA BA ZAN JAGORANCEKU BA A LOKACIN DA MANZON ALLAH (SAW) BA YA NAN, ALHALI NA JAGORANCEKU A HALIN MANZON ALLAH (SAW) YANA NAN?!".

2- KO KUMA NI BA MAFIFICINKU BA NE A K'ABILA, SABODA BANU HASHIM SUN FI SHI 'DAUKAKA A DANGANTAKA.
SAI YA NUNA MUSU CEWA; ASHE SHUGABANCI A ADDINI BA ANA CANCANTARSA BA NE SABODA 'DAUKAKAR DANGI KO K'ABILA, SABODA HAKA BAI TAK'AITA A CIKIN BANU HASHIM KAWAI BA, BAN DA WANINSU DAGA CIKIN K'URAISHAWA, SABODA ANNABI (SAW) YA CE:
«الأئمة من قريش».
"SHUGABANNI DAGA CIKIN K'URAISHAWA SUKE".

ALKALI YA CE:
TA YAYA YA CANCANCI SHUGABANCI ALHALI SHI DA KANSA YANA CEWA:
أقيلوني أقيلوني.
"KU TSIGENI DAGA SHUGABANCIN, KU TSIGENI".

'BARAWO YA CE:
YA FA'DI HAKA NE SABODA NAUYIN 'DAUKAR 'DAWAINIYAR SHUGABANCI, WANNAN KUWA SHI YAKE NUNA CIKAN HANKALINSA DA FALALARSA DA TSANTSENINSA DA TSORON ALLANSA, DON HAKA BAI KAMATA WA MAI FALALA YA NUNA KWA'DAYINSA GA SHUGABANCI BA IDAN AN BIJIRO MASA DA SHI, SABODA WANNAN ZAI SA A FARA TUHUMARSA DA MUNANA MASA ZATO.

ALKALI YA CE:
TA YAYA ZA KU BA SHI SHUGABANCI ALHALI UMAR (RA) YA FA'DA A KAN MINBARI, KOWA YA JI, YA CE:
إن بيعة أبي بكر كانت فلتة وقى الله شرها، فمن عاد إلى مثلها فاقتلوه.
"BAI'AR ABUBAKAR (RA) TA KASANCE BA - ZATA CE, ALLAH NE KAWAI YA KIYAYE SHARRINTA, DON HAKA DUK WANDA YA SAKE YIN IRINTA TO KU KASHE SHI".

'BARAWO YA CE:
KOMAI YADDA ZA MU YI SHAKKA A KAN ABU, MU DA KU DUKA BA ZA MU TA'BA YIN SHAKKA A KAN CEWA; UMAR (RA) YA KASANCE MUTUM NE MAI HANKALI BA MAHAUKACI BA, DON HAKA WANNAR MAGANA TASA IN AN 'DAUKETA A BISA YADDA KUKE ZATO, TO DOLE AYI HUKUNCI DA HAUKA MA DUK WANDA YA 'DAUKA A HAKA, SABODA UMAR (RA) YANA KAFA HUJJA NE A KAN KHALIFANCINSA DA INGANCIN KHALIFANCIN ABUBAKAR (RA), SABODA IDAN BAI'AR DA AKA YI WA ABUBAKAR (RA) BATACCIYA CE, TO DOLE BAI'AR UMAR (RA) ITA MA TA ZAMA 'BATACCIYA, TO DOLE SAI SAHABBAI DA SAURAN AHLUL BAITI SU CE: TO KAI MA IN HAKA NE DOLE A KASHEKA, KUMA BA DOLE NE AYI AMFANI DA NA'DIN 'YAN MAJALISAR SHURA DA KA YI BA, NA WA'DANDA ZA SU ZA'BI KHALIFA A BAYANKA.

MA'ANAR WANNAR MAGANA; LALLAI UMAR (RA) YA YI IMANIN CEWA; ABUBAKAR (RA) YA KASANCE SHI NE MAFI FALALA A CIKIN WANNAR AL'UMMA BAYAN ANNABI (SAW), KUMA SHI YA CANCANCI KHALIFANCI A BISA DALILAI DA KUMA NAZARI NA HANKALI, SABODA SHI NE KAWAI ZA A YI MASA BAI'A TA BA-ZATA KUMA - DA IZNIN ALLAH - A ZAUNA LAFIYA, AMMA BAYANSA BABU WANDA YAKE DA WANNAN MATSAYI.
AMMA KHALIFOFIN DA SUKA BIYO BAYANSA SUN SHA BANBAN A MATSAYI, AMMA SU BA SU CANCANCI KHALIFANCIN BA KAMAR YADDA ABUBAKAR (RA) YA CANCANTA BA".

KADA KU GAJI, KU BIYOMU A KASHI NA UKU DON JIN YADDA TA KAYA.

AMMA DAI NI A GANINA; DA 'DAN SHI'A GARA 'BARAWO.

No comments:

Post a Comment