Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Sunday, 7 February 2016

SIFFANTA MAGANAR ALLAH DA MANZONSA DA WAUTA KAFIRCI NE

IN WANNAR MAGANA TA SHAIKHUL ISLAMI IBNU TAIMIYYA (R) WAUTA CE DA SHIRME, TO BA SHI YA FARA FA'DA BA.
ANNABI (SAW) YA FARA CEWA; SHAIDAR MACE, - KO WACECE - RABIN SHAIDAR NAMIJI CE. BUKHARI YA RUWAITO:
عن أبي سعيد الخدري قال خرج رسول الله صلى الله عليه وسلم في أضحى ، أو فطر - إلى المصلى فمر على النساء فقال يا معشر النساء تصدقن فإني أريتكن أكثر أهل النار فقلن وبم يا رسول الله قال تكثرن اللعن وتكفرن العشير ما رأيت من ناقصات عقل ودين أذهب للب الرجل الحازم من إحداكن قلن وما نقصان ديننا وعقلنا يا رسول الله قال أليس شهادة المرأة مثل نصف شهادة الرجل قلن بلى قال فذلك من نقصان عقلها أليس إذا حاضت لم تصل ولم تصم قلن بلى قال فذلك من نقصان دينها.

SA'ANNAN, ALLAH NE YA FARA CEWA; DIYYAR MACE - KO WACECE - RABIN DIYYAR NAMIJI NE.
ALLAH YA CE:
يوصيكم الله في أولادكم للذكر مثل حظ الأنثيين

* DON HAKA IN Aminu Ashafa YA CE WANNAR MAGANA TA SHAIKHUL ISLAMI (R) WAUTA CE SABODA SHAIKHUL ISLAM IBNU TAIMIYYA CE YA FA'DETA TO ABIN DA SAUKI, SAI YA ZAMA SABODA KIYAYYA NE DA HASADA.
IN KUMA YA CE; WANNAR MAGANA WAUTA CE SABODA ITA MAGANAR KANTA, TO KENAN HUKUNCIN AMINU ASHAFA BAI TSAYA A KAN MAGANAR IBNU TAIMIYYA KAWAI BA, TA SHAFI DUK WANI DA YA FA'DI IRIN MAGANAR, DON HAKA TA SHAFI MAGANAR ALLAH DA MANZONSA. IN KUWA HAKA NE TO KO SHAKKA BABU SIFANTA MAGANAR ALLAH DA MANZONSA DA WAUTA KAFIRCI NE.

ALLAH YA YI MANA TSARI DA JAHILCI DA ZALUNCI. SON RAI YANA IYA KAI MUTUM GA KALMAR KAFIRCI ALHALI MUTUM BAI SANI BA.

JAMA'A BARKA DA JUMA'A.

No comments:

Post a Comment