Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Monday, 8 February 2016

SHUBUHOHIN RAFIDHA 'YAN SHI'A A GAME DA KASHE HUSSAINI (RA) (1)

DA FARKO MUNA MARABA WA MALAM NASIRU AMINU, WANDA YA CANZA SUNANSA ZUWA Dodon Wahabiyawa Kano, DA YI MASA BARKA DA DAWOWA DAGA DOGON HUTU DA YA DAUKA, LALLAI MUN YI KEWARSA.

JAWABAI A KAN TAMBAYOYI DA MULAHAZA DA MALAM NASIRU YA KAWO A KAN RUBUTUN DA MUKA YI A KAN MATSAYIN YAZIDU A GAME DA KASHE HUSSAINI (RA).

DA FARKO: YA KAMATA JAMA'A SU SANI, BA MA HA'DA YAZIDU DA HUSSAINI (RA) WAJEN FALALA DA MATSAYI A WAJEN ALLAH, SABODA HUSSAINI (RA) SAHABIN ANNABI (SAW) NE, KUMA YANA CIKIN AHLUL BAITI, AMMA SHI KUMA YAZIDU BA SHI DA KO 'DAYA DAGA CIKIN WA'DANNAN FALALOLI GUDA BIYU MASU GIRMA DA DARAJA.

NA BIYU: YAZIDU SARKI NE DA YA YI KHALIFANCI, WANDA A ZAMANINSA AN YI 'BARNA DA YAWA, ALLAH NE KAWAI YA SAN YADDA ZAI YI DA SHI.

NA UKU: MU BA MA SON YAZIDU KUMA BA MA TSINE MASA, SABODA SHI MUSULMI NE, SABODA A AQIDAR AHLUS SUNNA BA A TSINE WA MUTUM SANANNE, A KAMA SUNANSA A TSINE MASA, KAMAR YADDA 'YAN SHI'A SUKE YI.

NA HU'DU: MUNA YIN IRIN WA'DANNAN RUBUCE - RUBUCE NE DON K'OK'ARIN YIN ADALCI DA KUMA BAYYANA GASKIYAR ABIN DA YA FARU A WANCAN LOKACI, A SAKAMAKON K'ARERAYI MASU YAWA DA RAFIDHA 'YAN SHI'A SUKA K'IRK'IRA SUKA JINGINA MA RIGINGIMUN WANCAN LOKACI DON SU RU'DI MUTANE SU RINJAYESU ZUWA GA AQIDAR SHI'ANCI, AQIDAR DA ASALINTA BAYAHUDE ABDULLAHI 'DAN SABA'I NE YA SHIGO DA ITA WA AL'UMMAR MUSULMI.

SABODA HAKA, LALLAI MUNA JIN ZAFIN KASHE HUSSAINI (RA), AMMA KUMA BA MU YARDA DA A WUCE GONA DA IRI WAJEN HAKAITO ABIN DA YA FARU BA, KUMA BA MU YARDA DA A WUCE IYAKA WAJEN NUNA BAK'IN CIKIN BA, SABODA AN KASHE WA'DANDA SUKA FISHI FALALA AMMA KUMA MUSULMAI BA SU YI MAKOKI KAMAR YADDA 'YAN SHI'A SUKE YI WA HUSSAINI (RA) BA, AN KASHE SAYYIDINA UMAR (RA), AN KASHE USMANU (RA), AN KASHE ALIYU (RA), AMMA BA A YI MUSU MAKOKI IRIN WANDA 'YAN SHI'A SUKE YI WA HUSSAINI (RA) BA.

KAI, HAKA SU 'YAN SHI'AR, SUN SANI AN KASHE BABANSA ALIYU (RA) AMMA BA SU DAMU DA KISAN BA. WANNAN SHI YAKE NUNA MAKA CEWA; ABIN DA 'YAN SHI'A SUKE YI NA MAKOKIN KASHE HUSSAINI (RA) SUNA YI NE SABODA WATA MANUFA, WATO ITA CE MANUFAR KARE AQIDAR IMAMA, DA KUMA YA'DATA A TSAKANIN AL'UMMAR MUSULMAI, SABODA SHI KASHE HUSSAINI (RA) YANA DA ALAKA DA MASU MULKI NA DAULAR BANU UMAYYA, WANNAN SHI YAKE NUNA MAKA CEWA; SUNA YIN WANNAN NE KAWAI SABODA AQIDAR IMAMA DA KUMA NEMAN MULKI, SHI YA SA BA SA YIN MAKOKI WA ALIYU (RA) IRIN WANDA SUKE YI WA HUSSAINI (RA), ALHALI SHI YA KAMATA AYI MASA IRIN WANNAN MAKOKIN KOMA FIYE DA HAKA IN FALALA DA DARAJA SUKE SA AYI, AMMA SABODA BA SHI NE MANUFARSU BA, SHI YA SA BA SA YI MASA HAKAN.

GA NAN JAWABAN DA ZA MU YI A KAN WA'DANNAN MAGANGANU DA MALAM NASIRU YA KAWO, LA'ALLA ALLAH YA AMFANAR DA SHI, SHI DA MAKAMANTANSA, SABODA DA YAWA DAGA CIKIN 'YAN SHI'A K'ARANCIN TUNANI DA NUFIN ADALCI SHI YAKE SA SU SHIGA WANNAN ADDINI NA SHI'A.

(1) WASIYYAR MU'AWIYA (RA) GA 'DANSA YAZIDU:
(a) DA MUKA KAWO WANNAR WASIYYA, MUN KAWOTA NE CIKIN LAFAZIN LARABCI, KUMA MUN FA'DI MARJI'I (MADOGARA), DON HAKA ABIN DA YA KAMATA SHI NE, MALAM NASIRU YA KOMA CAN INDA NA 'DAUKO MAGANAR DON YA GANI, SHIN MAGANAR TANA DA ISNADI KO BABU?

(b) NASIRU YA CE:
"IDAN SHARRI NE YA SAMESU MEYASA MU'AWIYA YAKE FATAN SHARRI GA JIKAN ANNABI (S.A.W.)? DUK MAI HANKALI A NAN ZAI FAHIMCI IRIN KULLIN DAKE CIKIN ZUCIYAR MU'AWIYA DANGANE DA IMAM HUSAINI (A). SABODA HAKA A INA FATAN ALKHAIRI ANAN YAKE GA IMAM HUSAIN (A) ACIKIN WANNAN MAGANA TA MU'AWIYA?"

KA GA WANNAN RASHIN FAHIMTA CE DAGA MALAM NASIRU, SHI YA SA SUKA CE:
وكم من عائب قولا صحيحا … وآفته من الفهم السقيم

ABIN DA YAKE NUFI SHI NE; FATANSA ALLAH YA SA HUSSAINI (RA) YA SHAGALA DA NEMAN 'DAUKAR FANSAN JININ BABANSA DAGA WA'DANDA SUKA KASHE SHI, BA YA SHAGALA DA NEMAN MULKI BA, DON SU ZAUNA LAFIYA DA SHI.
BA –WAI- YANA NUFIN YANA SO A KASHE SHI BA.
WANNAR GURGUWAR FAHIMTA CE, WACCE TUSHENTA YAKE DAGA RASHIN ADALCI MA WA'DANNAN BAYIN ALLAH, DA KUMA KULLA MUSU GABA A CIKIN ZUCIYA.

(c) DUKKAN TAMBAYOYIN DA SUKA BIYO BAYA, BA SU DA MUHALLI, SABODA MALAM NASIRU YA GINASU NE A KAN GURGUWAR FAHIMTARSA GA MAGANAR MU'AWIYA (RA). SABODA HAKA MAGANAR MALAM NASIRU KAMAR HAKA:
" KAMAR MUTUM NE YACE KYALE WANE KADA KARAMA ABINDA YAYI MAKA ALLAH YA HADASHI DA GAMONSA KO KUMA INA FATAN ALLAH YA ISARMA. DUK MAI HANKALI YASAN BAKAR ADDU'A KAKEYI MASA BAWAI KANA CEWA YA YAFE MASA BANE BA, SABODA ITA YAFIYA BA'A NEMAN FANSA KO MUGUN FATA AKANTA.

TO KAMAR HAKA ZANCAN MU'AWIYA YAKE CEWA IDAN KASAMI DAMA AKANSA TO KAYI MASA AFUWA, ALHALI KUWA ABAYA GA ABINDA YAKE CEWA INA FATAN ALLAH YA ISAR MAKASHI DA ABINDA YASAMI MAHAIFINSA DA 'DAN UWANSA".

DUKA WANNAR MAGANA K'ARYA CE DA ZATO WANDA YA GINU A KAN RASHIN FAHIMTA, SA'ANNAN KUMA GA "TAHRIFI", WATO CANZA MAGANA SABODA RASHIN ADALCI.

GA NAN MAGANAR MU'AWIYA (RA) KAMAR HAKA:
"INA FATAN ALLAH YA SA WA'DANDA SUKA KASHE BABANSA, KUMA SUKA K'I TAIMAKON 'DAN UWANSA SU ISHE SHI".

AMMA SHI MALAM NASIRU SAI YA CE:
"INA FATAN ALLAH YA ISAR MAKASHI DA ABINDA YASAMI MAHAIFINSA DA 'DAN UWANSA".

SUBHANALLAH!!
DON ALLAH KA DUBA TSANTSAR "TAHRIFI" A FILI, DA RASHIN ADALCI??!!!

ALHALI KUWA A FILI YAKE GA DUK MAI HANKALI, BALLE KUMA MAI ADALCI CEWA; ABIN DA YAKE NUFI SHI NE; SU ISHE SHI, MA'ANA YA TAK'AITA DA SU, BA TARE DA YA ZO YA NEMI MULKI BA.

NASIHA:
YA KAMATA MALAM NASIRU YA JI TSORON ALLAH, YA SAN CEWA; YIN ADALCI WA MAK'IYINKA ALAMA CE TA JIN TSORON ALLAH, RASHIN YI MASA ADALCI KUWA, ALAMA CE TA RASHIN TSORON ALLAH, ALLAH YA CE:
{وَلَا يَجْرِمَنَّكُمْ شَنَآنُ قَوْمٍ عَلَى أَلَّا تَعْدِلُوا اعْدِلُوا هُوَ أَقْرَبُ لِلتَّقْوَى وَاتَّقُوا اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ } [المائدة: 8]

DON HAKA BAI KAMATA K'IYAYYA TA SA KA YI K'ARYA WA MUTUM BA, KA CANZA MASA MAGANA KAWAI DON TSANANIN K'IYAYYA DA RASHIN TSORON ALLAH, YA KAMATA KA SAN CEWA; ALLAH YANA SANE DA DUKKAN ABIN DA KAKE AIKATAWA, KUMA ZAI TAMBAYEKA A KAI.

(2) WASIYYAR HASSAN (RA) GA 'DAN UWANSA HUSSAINI (RA:
(a) ISNADIN WANNAR MAGANA KA BINCIKA.
(b) MALAM NASIRU YA CE:
"TO MEYASA ALLAH BAZAI IYA HADAWA ALAYAN MUHAMMAD (S.A.W.) KHILAFA DA ANNABTA BA?".

AMSA: SABODA BA MU SAMU DALILI A KAN HAKA BA.

(3) WASIK'AR YAZIDU ZUWA GA IBNU ABBAS (RA):
MALAM NASIRU YA CE:
"AMS : SHIMA INA ISNADIN WANDA ZANCE YAKE?".

AI BINCIKAWA ZA KA YI, IN KA BINCIKA BA KA SAMU BA SAI KA ZO KA TAMBAYA KA CE; BA KA SAMU BA, SAI IN KAWO MAKA SHI.

• FA'DAKARWA:
DAGA YANZU, DUK ABIN DA KA TAMBAYI ISNADINSA BA ZAN YI MAGANA A KANSA BA, HAR SAI KA TABBATAR MINI DA CEWA; KA BINCIKA AMMA BA KA SAMU BA, TO SAI IN KAWO MAKA, SABODA WANNAN YANA NUNA RASHIN BINCIKE.

(4) WASIK'AR YAZID ZUWA GA GOMNANSA UBAIDULLAH:
LALLAI INA SANE DA WANNAR RIWAYA AKWAI "INQI'DA'I" A CIKIN SANADINTA, AMMA KUMA TANA DA SHAIDA DAGA 'DAN SHI'A ABU MIKHNAF, WANNAN YA SA NA YI LA'AKARI DA ITA, SABODA IN KA GA MAK'IYINKA YA FA'DI ALHERI A KANKA TO KO SHAKKA BABU 65 – 70% GASKIYA NE, ABU MIKHNAF YA CE:
فكتب إليه يزيد: أما بعد، فإنك لم تعد أن كنت كما أحب، عملت عمل الحازم، وصلت صولة الشجاع الرابط الجأش، فقد أغنيت وكفيت، وصدقت ظني بك، ورأيي فيك، وقد دعوت رسوليك فسألتهما، وناجيتهما فوجدتهما في رأيهما وفضلهما كما ذكرت، فاستوص بهما خيرا، وإنه قد بلغني أن الحسين بن علي قد توجه نحو العراق، فضع المناظر والمسالح، واحترس على الظن، وخذ على التهمه، غير الا تقتل إلا من قاتلك، واكتب إلي في كل ما يحدث من الخبر، والسلام عليك ورحمة الله.
تاريخ الطبري (5/ 380 - 381)

A CIKI SAI YA CE:
غير الا تقتل إلا من قاتلك

"SAI DAI KADA KA KASHE KOWA SAI WANDA YA YAK'EKA".

SABODA HAKA WANNAR RIWAYA SHAIDA CE GA WACCAR, TANA NUNA CEWA; YAZIDU BAI YI UMURNI NA KAI TSAYE DA KASHE HUSSAINI (RA) BA, KAMAR YADDA RIWAYAR 'DAN SHI'A ABU MIKHNAF TA TABBATAR.

(5) JAWABIN YAZIDU BAYAN AN KAWO MASA LABARIN ABIN DA YA FARU A KARBALA:
MALAM NASIRU YA CE:
"NIDAI DANA DUBA ISNADIN WANNAN MAGANA SAI NAGA WANDA YA RAWAICI RIWAYAR SHINE " ABU MIKHNAF".

AI ABU MIKHNAF 'DAN SHI'A NE, IN KA YARDA MU JEFAR DA SHI A NAN, TO DOLE MU JEFAR DA DUKKAN RIWAYOYINSA GABA 'DAYA TARE DA SAURAN MARUWAITA 'YAN SHI'A A LABARUN DA SUKA RUWAITO NA KASHE HUSSAINI (RA).

MISALI: AL- 'DABARIY YANA DA RIWAYOYI (108) DAGA ABU MIKHNAF A KAN KASHE HUSSAINI (RA), DON HAKA DUKKANSU K'ARYA NE KENAN?!
KUMA ABU MIKHNAF BABBAN MADOGARA NE GA 'DABARIY A CIKIN LITTAFINSA NA TARIHI A LABARUN KASHE HUSSAINI (RA), DON HAKA IN KA YARDA, SAI MU ZO MU 'DAUKESU 'DAYA BAYAN 'DAYA MU K'ARYATASU SABODA ABU MIKHNAF, MU GA IN WANI ABU ZAI SAURA MA 'YAN SHI'A A LABARUN DA SUKE YA'DAWA NA KASHE HUSSAININ (RA)??

(6) MATSAYIN IBNU TAIMIYYA (R) A GAME DA KASHE HUSSAINI (RA):
MALAM NASIRU YA CE:
" GA ABINDA SHEHUNKU 'DANTAIMIYYA YAKAWO DANGANE DA WANDA YAKE SHINE SABABIN KASHE IMAM HUSAINI (A) ACIKIN LITTAFINSA MAI SUNA MAJ'MA'UL FATAAWA. 4/483. :

...ولم يولد إلا فى خلافة عثمان ولم يكن كافرا ولكن جرى بسببه ما جرى من مصرع الحسين..

LALLAI HAKA NE, AN KASHE HUSSAINI (RA) NE DON KARE MULKIN YAZIDU, AMMA KUMA HAKAN BA YA LAZIMTA YA ZAMA MAI LAIFI, SABODA ZA A IYA YIN ABU SABODA KAI, AMMA KAI KUMA BA KA MA SAN AN YI BA, KO KUMA IN KA SAN AN YI AMMA BA KA GOYI BAYA BA.

A TAK'AICE, YAZIDU MUSULMI NE, YA KOMA GA UBANGIJINSA, YA JE YA TARAD DA AIYUKANSA DA YA AIKATA NA SHARRI DA NA ALHERI, IN ALLAH YA GA DAMA ZAI AZABTAR DA SHI A KAN LAIFUKANSA, IN KUMA YA GA DAMA YA GAFARTA MASA, SABODA ALLAH MAI AFUWA NE, KUMA MAI GAFARA, KUMA IN AN KWATANTA GAFARAR ALLAH DA RAHAMARSA DA LAIFUKAN YAZIDU SAI MU GA LAIFUKANSA BA KOMAI BA NE A GABAN RAHAMAR ALLAH.
IN ALLAH YA GAFARTA MASA BABU WANDA YA ISA YA SA A AZABTAR DA SHI, KAMAR YADDA IN YA GA DAMAN AZABTAR DA SHI BABU WANDA YA ISA YA HANA.

ALLAH YA SAUWAK'E.


No comments:

Post a Comment