Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Sunday, 7 February 2016

SHIN AKWAI NASSI A KAN IMAMANCIN ALIYU (RA) (2)??!

BAYAN RAFIDHA SUN TAK'AITA IMAMANCI A CIKIN ZURRIYAR HUSAINI (RA) BAN DA ZURRIYAR HASSAN (RA) SABODA LAIFIN DA SHI IMAMIN NASU NA BIYU HASSAN (RA) YA YI MUSU NA YIN SULHU DA MU'AWIYA (RA) DA MIK'A MASA KHALIFANCI, ABIN DA YAKE NUNA K'ARYAN SAMUWAR NASSIN DA RAFIDHA 'YAN SHI'A SUKE IK'IRARI.

TO BAYAN RASUWAR ZAINUL ABIDINA ALIYU BUNUL HUSAINI IMAMINSU NA 4 SAI SHI'A ZAIDIYYA SUKA BAYYANA MASU RA'AYIN IMAMANCIN ZAIDU BIN ALIY, A SAKAMAKON RABA GARI DA SUKA YI DA RAFIDHA 'YAN SHI'A MASU RA'AYIN IMAMANCIN MUHAMMAD BN ALIY AL- BAQIR, BAYAN ZAIDU BN ALIY YA BAYYANA YARDARSA GA ABUBAKAR (RA) DA UMAR (RA), SAI SU RAFIDHA SUKA YI ALLAH WADAI DA SHI.

TO, IN HAR 'YAN SHI'A ZA SU RABU GIDA 2; ZAIDIYYA SU CE: ZAIDU BN ALIY SHI NE IMAMI, SU KUMA RAFIDHA 'YAN SHI'A ZA SU CE: AL- BAQIR SHI NE IMAMI, TO INA NASSIN DA AKE RAYAWA, CEWA; IMAMAI 12 NAN AKWAI NASSI DA YA AMBACESU?!
KO KUMA IN BABANSU ZAINUL ABIDINA YA YI WASIYYA, YA NASSANTA IMAMIN DA ZAI BIYO BAYANSA, TO DON ME YA SA AKA SAMU WANNAN DAREWA GIDA BIYU DA 'YAN SHI'A SUKA YI, ZUWA RAFIDHA MASU RA'AYIN IMAMANCIN AL- BAQIR DA KUMA ZAIDIYYA MASU RA'AYIN IMAMANCIN ZAIDU BN ALIY??!!
TUN DA DOLE MUTUM 'DAYA NE A CIKINSU AKA NASSANTA SHI A MATSAYIN IMAMI, IN AKWAI NASSIN!!

TO SAI RAFIDHA SUKA SAMO DABARA DON FITA DAGA WANNAN MATSATSI DA SUKA SHIGA, SAI SUKA CE: AI IMAMA TANA KASANCEWA NE GA BABBAN 'DA, DON HAKA AL- BAQIR NE IMAMI BA ZAIDU BN ALIY BA, KUMA IMAMA BA ZA TA KASANCE GA 'YAN UWA GUDA 2 BA, TUN DAGA KAN HASSAN (RA) DA HUSSAINI (RA).

SAI KULAINIY DA AL- SADUQ SUKA RUWAITO MUSU WATA RIWAYA:
عن ابن أبي نصر قال: قلت لابي الحسن الرضا عليه السلام: إذا مات الامام بم يعرف الذي بعده؟ فقال للامام علامات منها أن يكون أكبر ولد أبيه
الكافي الكليني - (1 / 284)، الخصال للصدوق (1/ 116)

"DAGA IBNU ABI NASR YA CE: NA CE MA BABAN HASSAN AL- RIDHA (AS) IDAN IMAMI YA MUTU DA WACE ALAMA ZA A GANE IMAMIN DA YAKE BAYANSA? SAI YA CE: IMAMI YANA DA WASU ALAMOMI, DAGA CIKINSU YA ZAMA SHI NE BABBAN 'DA A WAJEN UBANSA".

TO AMMA BAYAN RASUWAR ISMA'ILA BN JA'AFAR BABBAN 'DA GA JA'AFARUS SADIQ, KAFIN YA ZAMA IMAMI, SAI SUKA CE; IMAMI SHI NE MUSA BN JA'AFAR, ALHALI BA SHI BA NE BABBAN 'DA GA JA'AFARUS SADIQ BA, KUMA GA SHI SUN SA IMAMANCI GA 'YAN UWA GUDA 2, BAYAN SUN SOKE WANNAN, SUN CE BA ZAI SAKE FARUWA BA, BAYAN YA FARU A KAN HASSAN (RA) DA HUSSAINI (RA).
TO DA AKA TAMBAYESU A KAN WANNAN, SAI SUKA CE: AI "BADA'I" NE YA SA HAKAN YA FARU. WATO –WAI- YA BAYYANA MA ALLAH NE CEWA; ISMA'ILA BN JA'AFAR ZAI RASU KAFIN YA ZAMA IMAMI – DUK DA CEWA; SHI NE YA CANCANCI IMAMANCI A BAYAN UBANSA, SABODA SHI NE BABBAN 'DA A WAJEN UBAN NASA -, DON HAKA SAI YA MAI DA IMAMANCIN KAN 'DAN UWANSA MUSA BN JA'AFAR, DUK DA CEWA; IMAMANCI BA ZAI HA'DU GA 'YAN UWA GUDA 2 BA.

A TAK'AICE DAI, DAGA NAN AQIDAR "BADA'I" TA RAFIDHA 'YAN SHI'A, TA JINGINA MA ALLAH JAHILCI (SUBHANALLAH) TA FARA AIKI.

TO JAMA'A, HAKA DAI ABIN YAKE TA SAUYAWA KAMAR HAWAINIYA!!

AKWAI CIGABA INSHA ALLAHU.

No comments:

Post a Comment